’Abin da ya sa na zama ɗan fashin daji’

Asalin hoton, Getty
Wani jagoran ‘yan fashin daji ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa shekaru da dama da aka kwashe ana nuna wa fulani makiyaya wariya da karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba daga hannun su ya ƙara ta'azzara tashe-tashen hankula a arewacin Najeriya.
A cikin tattaunawar, wadda ba kasafai ake samun irin ta ba, ya ce rikicin zai yi tsanani har sai hukumomi sun shawo kan cin hanci da rashawa da ya zama ruwan dare a yankin.
A tsawon shekaru ƙungiyoyin masu aikata laifuka da aka fi sani da "yan bindiga" a yankin Arewa maso Yamma da tsakiyar Najeriya sun addabi al'umma inda suke kai hare-hare ƙauyuka da sace shanu da yin garkuwa da mutane da kuma ƙaƙaba wa manoma da masu haƙar ma'adinai haraji.
An gudanar da tattaunawar da ɗaya daga cikin shugabannin irin waɗannan ƙungiyoyi yayin tattara bayanai kan wani rahoto da aka wallafa a mujallar The New York Review of Books.
Farfesa kuma marubuciya ƴar Amurka, Helen Epstein tare da wani wakilin kamfanin dillancin labarai na AFP a Arewacin Najeriya ne suka rubuta rahoton.
"Shekaru da dama ana zaluntar makiyaya Fulani lamarin da ya sanya suka ɗauki makamai. A baya ba mu taɓa zama masu aikata laifuka ba," in ji wani shugaban ƴan bindiga mai suna Babangida.
Ayyukan ƴan bindiga sun samo asali ne daga rikice-rikicen da ke tsakanin makiyaya da manoma kan samun damar amfani da wurin kiwo da kuma ruwa, sauyin yanayi da ƙaruwar al'umma sun taka rawa wajen ƙara ta'azzara matsalar.
Daga cikin wannan tashin hankali ne aka samu ƙungiyoyin ƴan bindiga masu ƙarfi, waɗanda galibinsu suka ƙunshi makiyaya Fulani.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rikicin ya sauya daga hare-hare da ramuwar gayya zuwa manyan ayyukan ta'addanci da aikata laifuka masu sarƙaƙiya da ƙungiyoyin ƴan bindiga ke aiwatarwa.
Yawan mambobin waɗannan ƙungiyoyi ya bambanta daga kusan mutum 12 zuwa sama da 100.
Sun samar da wani yanayin samun kuɗaɗe ta hanyar garkuwa da mutane, abin da ke kawo musu maƙudan kuɗaɗe har ma sun ƙulla ƙawance da ƙungiyoyin masu jihadi a Najeriya.
Bayan shafe watanni ana tattaunawa daga bisani dai Babangida ya amince zai yi hira da ƴan jarida a wani ƙauye mai nisa da ke Jihar Katsina bayan wani dattijo mai shiga tsakani daga ɓangaren gwamnati ya shiga lamarin.
"Adalci ne kaɗai mafita idan aka tabbatar da adalci kowa zai zauna lafiya," in ji shugaban ƴan bindigar wanda ya nemi a kira shi da sunansa na farko kawai.
A halin da ake ciki tashin hankali na ci gaba da addabar yankin.
A makon da ya gabata a maƙwabciyar Jihar Zamfara wasu ƴan bindiga sun ƙone wani gida yayin da suka kai hari inda suka kashe mutane 12 daga iyali guda.
A farkon wannan watan wasu 'yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda 8. Haka kuma a watan Satumba an yi garkuwa da mutane sama da 80 mafiya yawa mata a jihohin Zamfara da Neja. An sace da dama daga cikinsu ne ya yin da suke aikin gona.
Matsalar taɓarɓarewar tsaro daya ce daga cikin manyan batutuwan da ake tafka muhawara a kansu lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ke gudana yayin da Bola Tinubu ke neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen watan Janairu.
Cin hanci
Sanye da shuɗiyar riga, mutumin mai shekaru 38, za ka iya bayyana shi a matsayin mutumin kauye kamar sauran mazauna yankin, abin da ya bambanta shi kawai shi ne yana rataye ne da bindiga ƙirar Kalashnikov.
"Babu wani ɗan bindiga da haka kawai ya ɗauki bindiga ya fara ta'aɗɗanci. Akwai abin da ya haifar da haka," in ji Babangida yayin da yake zaune a ƙarƙashin bishiya.
Babangida ya yi ikirarin cewa ce ya shiga harkar ƴan bindiga ne shekaru 10 da suka gabata, bayan wani haɗin gwiwar jami'an ƴan sanda da ƴan banga sun ƙwace shanun iyalinsa da yawansu ya kai 97.
Ya bayyana cewar an kai samamen ne bisa zargin duk Fulani ƴan bindiga ne.
An tilasta masa biyan miliyoyin naira wajen karɓo belin mahaifiyarsa da ɗan‘uwansa.
''Ya yi nasarar ƙwato shanu 10 kacal, daga bisani ya yi amfani da kuɗinsu ya sayo bindigogi'' sannan ya mayar da iyalansa wani sansani cikin daji.
Fulani makiyaya sun shafe shekaru suna kiwon dabbobi inda suke ƙaura daga arewaci lokacin rani zuwa yankunan Arewa ta Tsakiya da kudancin Najeriya ta wasu tsoffin hanyoyi da suka saba bi da dabbobinsu cikin daji.
Jami'an ƙananan hukumomi da suka haɗa da dagatai da ƴan sanda da sojoji ba su ɗauki matakan da suka dace wajen hana manoma mamaye wuraren kiwo ba. A wasu lokutan ana zargin jami'an da haɗa kai da manoman wajen mamaye wuraren da aka yi tanadi don kiwo.
Wariya
Manoma da makiyaya dukansu sun ɗanɗana kuɗarsu a rikicin, inda hare-haren da ake kaiwa wasu ƙauyukan manoma a wasu lokutan ke haddasa asarar rayuka da dama.
Fulani sun yi ƙorafi cewa gwamnati da jami'an tsaro na ware su.
Babangida ya ce idan shanu suka lalata gonaki, "dagacin ƙauyen zai sanya tarar da ta zarce ƙimar amfanin gonar da aka lalata."
"Amma idan manomi ya kashe shanun makiyayi sai a ɗora laifin a kan makiyayin ba tare da biyan shi diyya ba," kamar yadda ya ce..
"Idan dagacin ya kira ƴan sanda za su haɗa kai da alƙali wajen ƙara yawan tarar da za a laftawa makiyayin."
Ko abin da ya faɗa gaskiya ne?

Asalin hoton, Nigerian Military
Sojojin Najeriya kan kira ƴan bindiga da "yan ta'adda" kuma su na gudanar da wani samame na musamman a yankin Arewa maso Yamma domin yaƙar su.
Sai dai yayin da yake magana kan zarge-zargen "rashin adalci" da Babangida ya yi, kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Katsina ya shaida wa AFP cewa: "Abin da yake faɗa gaskiya ce... Ba za a iya ware wannan al'amari daga cikin abubuwan da ke haddasa aikata waɗannan laifuka ba."
Nasiru Mu'azu ya shaida wa AFP cewa jiharsa ta yi ƙoƙarin ƙaddamar da tattaunawar zaman lafiya da kuma magance matsalolin da ke haddasa aikata laifuka. Ya bayyana cewa, "abin da ke faruwa a nan Arewa maso Yamma rikici ne da ya samo asali daga cikin al'umma," sabanin rikicin ƙungiyoyin masu jihadi da ke addabar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ya ƙara da cewa, "Babbar matsala ce" samun daidaito tsakanin ɗaukar tsauraran matakai daga jami'an tsaro da kuma amfani da diflomasiyya wajen warwaren rikici da rashin jituwar.
'Kudi da ɗaukar fansa'
Akwai ƙungiyoyin ƴan bindiga da suke sanyawa manoma a ƙauyuka haraji.
Sojoji sukan kai hare-hare ta sama a yankunan da ƴan bindiga suka ƙwace.
Yadda ƙungiyoyin ƴan banga suke kashe makiyaya na daga cikin abubuwan da suka hana cimma yarjejeniyar sulhu, lamarin da ya sa tashin hankalin ya ƙara ƙamari.
Sabbin ƴan bindiga matasa
Babangida ya bayyana damuwarsa game da sauyin da ake samu tsakanin ƙungiyoyinsu na masu aikata laifuka, inda ake maye gurbin tsoffin ƴan bindiga da fusatattun matasa marassa tausayi.
Ya ɗora alhakin kashe wadanda aka yi garkuwa da su bayan danginsu sun biya kuɗin fansa akan matasan wadanda ke tafka laifuka bayan sun sha ƙwayoyin maye.
Masu fashin baƙi sun bayyana damuwa game da yadda ake ƙulla ƙawance tsakanin ƴan bindiga marassa ilimi da mayaƙan Jihadi.
Babangida ya amince cewar ''wasu daga cikin ƴan bindiga sun haɗe da mayaƙan jihadi saboda wasu dalilai, sai dai ya dage cewar da dama ƴan bindiga na aikawa laifuka ne saboda kuɗi da ɗaukar fansa".



























