Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juventus ta matsa kan Silva, Barcelona na harin Pedro
Juventusna shirin sake ruɓanya himmarta wajen ganin ta ɗauko ɗan wasa Bernardo Silva, da ke shirin barin Manchester City a kakar wasannin nan, wajen ganin sun yi nasarar kan Atletico Madrid da Barcelona wajen siyen ɗan wasan. (Corriere dello Sport - in Italian)
Ana sa ran daraktan wasanni Bercelona Deco zai halarci gasar wasan ƙarshe na gasar F A a Ingila, don kallon yadda ɗan wasan Chelsea Joao Pedro zai taka leda, duk da cewar Chelsea ɗin ba ta son siyar da ɗan wasan. (Mail)
Coventry City na son ɗauko ɗan wasan Netherlands Georginio Wijnaldum, da kwantaraginsa zai ƙare da Al-Ettifaq, a kakar wasannin nan. (Football Insider)
Everton na harin ɗan wasan Burnley loum Tchaouna, da ke cikin tawagar ƴan wasan Faransa ƴan shekaru ƙasa da 21. (Football Insider)
SC Freiburg na son siyen ɗan wasan gaban Leeds Unite Wilfried Gnonto, yayin da Leeds United ɗin ta ke shirin siyar da ɗan wasan, ko kuma ta bayar da shi aro amma da alƙawarin siyensa nan gaba. (Sky Sports Germany)
Ana danganta mai tsaron bayan Italiya Alessandro Bastoni da Barcelona, sai dai ya na son ci gaba da zama a Inter Milan, idan har komawar ta sa zuwa ƙungiyar ta Spaniya ba ta tabbata ba. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Juventus na iya duba yiwuwar baiwa ɗan wasan Brasil Douglas Luiz, da ke buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a Aston Villa, damar burge mai horar da ƴan wasan ƙungiyar ko kuma ya siyar da shi. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Bayern Munich na son ɗan wasan Atalanta Charles De Ketelaere, a wani shirin ko ta kwana idan aka sami rashin tabbacin komawar ɗan wasan Newcastle United Anthony Gardon bai yi nasara ba. (Football Italia)