Wane ne Abu-Bilal al-Mainuki da sojojin Najeriya da na Amurka suka kashe?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Da safiyar yau ne Shugaba Trump na Amurka ya ce dakarun Amurka da na Najeriya sun kashe - mataimakin babban kwamandan ƙungiyar IS na duniya a wani harin haɗin gwiwa.

A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka, ya ce daga yanzu Abu-Bilal al-Mainuki ba zai ƙara zama wata barazana ga sojojin Amurka da ƙasashen Afirka, ba.

A nata ɓangare rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan Abu-Bilal al-Mainuki, a wani harin haɗin gwiwa tsakanin dakarun ƙasar da na Amurka.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rudunar sojin ta Najeriya Samali Uba ya fitar a yau Asabar, ya ce sun samu nasarar kai wani tsararren hari da muka shirya ƙarƙashin shirinta na yaƙi da ta'adanci da ya yi sanadiyar kisan Abu-Bilal al-Minuki, ɗaya daga cikin manyan mayaƙan ISIS kuma ɗaya daga cikin ƴan ta'addan duniya."

Tuni dai Shugaba Tinubu na Najeriya ya fitar da sanarwar yabo ga sojojin ƙasarsa da na Amurka bisa kisan da suka yi wa Abu-Bilal al-Minuki a harin da suka kai gidansa da ke yankin Tafkin Chadi.

Wane ne Abu-Bilal al-Mainuki?

Dangane da sanin ainihin tarihinsa, BBC ta tattauna da Dr Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security Limited, mai nazarin al'amarun tsaro a yankin Sahel da kuma Dr Audu Bulama Bukarti mai bincike kan ayyukan ƴanbindiga ƙasashen Afirka.

Sunansa na ainihi shi ne Abubakar Ibn Muhammad in Ali, Almuniki, kuma an haife shi a shekarar 1982 a garin Mainok da ke yankin ƙaramar hukumar Bin Sheikh a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda Kabiru ya bayyana.

Dr Bukarti ya ce shekarunsa sun kama tsakanin 44 zuwa 45, kuma ana kiransa da Almuniki ne saboda garinsa na Mainok, ake yi maa alkunya da hakan.

''Daga bayanan da muke da su ya shiga ƙungiyar ISWAP, wadda reshe ta ISIS a yankin Afirka ta Yamma, kuma ya taimaka wa ƙungiyar samun dakaru masu yawa, tun bayan shigarsa'', in ji Dr Kabiru Adamu.

A cewar masanin tsaron, Abu-Bilal al-Minuki, ya samu ilimin ta'addanci, kuma yana da dabarun tsara hare-hare da yadda ƙungiyar za ka kauce wa dabarun sojojin Najeriya.

''Bisa ga tarihin yadda ya fara ayyukan ƙungiyar, aƙidunsa sun sha bamban da sauran mayaƙan ƙungiyar da suka yi shuhura'', in ji shi.

Dr Bukarti ya ce al-Mainuki na daga cikin mayakan da suka ɓangare daga Shekau.

Kabiru Adamu ya ƙara da cewa bisa ga aƙida yana da saɓani da Mamman Nur wani jigo a ƙungiyar da ma Abubakar Shekau, wanda a baya suke ƙarƙashin inuwar guda kafin ɓallewar ISWAP.

''Abu-Bilal al-Minuki ya fara shahara ne bayan kashe Shekau da Mamman Nur'', in ji shi.

'Ƙusa ne a ƙungiyar ISIS ta duniya'

Shugaba Trump na Amurka ya bayyana al-Mainuki da kasance mutum na biyu mafi girman muƙami a ƙungiyar ISIS.

To amma Dr Bukarti ya ce ba hakan batun yake ba, amma dai ya kasance babban kusa a ƙungiyar ta ISIS.

''Yana dai da ƙarfi a ƙungiyar ISWAP, kuma mamba ne a ofishin da ke kula da ƙawayen ISWAP a yankin tafkin Chadi, wanda kuma ya taimaka wajen tara mata kuɗi da mayaka'', in ji Bukarti.

Shi ma Dr Kabiru Adamu ya ce Abu-Bilal al-Mainuki mamba ne sashen 'Maktar Al-Furkqan' na uwar ƙungiyar ISIS ta duniya.

''Shi wannan sashe shi ke taimaka wa ƙungiyar ISIS wajen yadda za ta gudanar da ayyukanta da kuma tsara dabarun tara wa ƙungiyar kuɗaɗe daga daular Afirka ta Yamma da yankin Sahel'', in ji masanin tsaron.

Shugaban kamfanin na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce Abu-Bilal al-Minuki na cikin mutanen da Amurka ta lissafa cikin jerin mutanen da ake ɗaukar nauyin ta'addanci a duniya.

''A baya-bayan nan ayyukansa sun bunƙasa saboda rawan da yake takawa wajen kitsa hare-haren ISWAP'', in ji shi.

Wace rawa yake takawa a IS?

Dr Kabiru Adamu ya ce Abu-Bilal al-Minuki na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar IS a duniya.

Ya ƙara da cewa kai-tsaye babu wani hari da za a ce shi ya kitsa a Najeriya ko Afirka ta yamma, kasancewarsa mamba a ƙoli a ƙungiyar.

"Shi shugaban ne can ƙoli (gudanarwa) ba jagoran filin daga ba, tun 2018 da ya yi fice aka san shi a matsayin shugaba na can ƙoli, ba na filin daga ba'', in ji shi.

Masanin tsaron ya ce Al-Minuki shugaba ne da ke tsarawa da shirya hare-hare a can sama, amma ba shugaban filin daga ba da ke kitsawa ko zartar da hare-haren ba.

Kabiru Adamu ya ce baya da kasancewar al-Minuki mamba a sashen 'Maktar Al-Furkqan', haka kuma yana cikin ɓangare na ISIS ne da ke can ƙoli da ake cewa ''General Directorates of Provinces''.

''Mamba ne a wanan kwamiti na ƙoli na ƙungiyar, kuma shi ne ma ke wakiltar yankin Afirka ta Yamma a Sahel a cikin wannan kwamiti'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.

Shi ma Dr Bukarti ya ce an fi sanin al-Mainuki a wajen jagorancin ƙungiyar da ƙarfafa alaƙarta ƙungiyoyin ƙasashen waje.

''Ba a san shi da shiga gaba wajen ƙaddamar da hare-hare ba, ni dai ban san wani hari da ya jagoranci kaiwa ba'', in ji Dr Bukarti

A ina aka kashe shi?

Cikin wata sanarwa da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya fitar ya ce sojojin Amurka da na Najeriya sun kashe Abu-Bilal Al-Manuki ne a harin haɗin gwiwa da suka kai gidansa a wani tsibiri da ke yankin Tafkin Chadi, bayan samun sahihan bayan sirri.

Rudunar sojin ta Najeriya ta danganta Abu-Bilal al-Minuki da hannu a sace ɗaliban makarantar ƴan mata da ke Dapchi, 2018, inda aka sace dalibai 100 a makarantar kwanan, da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda hakan ya jefa damuwa a faɗin ƙasar.

Tun a farkon wannan shekarar ne dai Amurka ta girke ɗaruruwan dakarunta a Najeriya, domin bayar da shawarwarar ƙwararu da musayar bayanai na sirri kan yaƙi da ƴan bindigar.

Haka kuma tsawon watanni Shugaba Trump na Amurka na zargin gwamnatin Najeriya da rashin ɗaukar matakan da suka dace wajen daƙile ayyukan masu ɗauke da makamai wajen kare mabiya addinin Kirista a ƙasar.

Sai dai gwamantin ta Najeriyar ta musanta zargin, inda ta ce ƴan bindigar na kai hare-hare ne kan Musulmi da mabiya addinin Kirista a ƙasar.

Ko a ranar Kirsimetin shekarar da ta gabata, sai da dakarun Amurka suka kai wani hari jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya da ta ce an kai shi ne kan dakarun ISIS da ke harkokinsu a yankin.

A shekarar 2024 ne dai rundunar sojin Najeriya ta yi iƙirarin kashe Abu-Bilal Al-Manuki da wasu, kwamandojin ƙungiyar ISWAP a ƙasar.

Don haka ne Dr Kabiru Adamu ya ce a yanzu akwai buƙatar sojojin ƙasashen biyu su ftar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da iƙirarin nasu da tabbatar da cewa shi ɗin ne.