Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da ya rage kimanin wata ɗaya a fara Gasar Kofin Duniya, tuni ƙasashen da suka samu gurbin gasar suka fara shirye-shiryen tafiya.

A ranar 11 ga watan Yuni mai kamawa ne za a yaye labulen gasar a filin wasa na Estadio Azteca da ke birnin Mexico City na ƙasar Mexico.

Gasar za ta ɗauki hankali matuƙa, kasancewa ƙwararrun ƴan wasa daga fitattun ƙasashe a harkar ƙwallon ƙafa za su halarta.

Yayin da gasar za ta kasance ta farko ga wasu ƴan wasan, za kuma ta kasance ta ƙarshe da wasu ƴanwasan da suka jima suka taka leda a harkar ƙwallon ƙafa.

Ana buga gasar Kofin Duniya duk bayan shekara huɗu, inda aka buga gasa ta ƙarshe a Qatar a 2022, wadda Argentina ta lashe, bayan doke Faransa a wasan ƙarshe.

Ina za a buga gasar?

Za a buga Gosar Kofin Duniya ta bana a ƙasashe guda uku da suka haɗa da Amurka da Mexico da kuma Kanada.

A gaba ɗayan gasar za a buga wasanni 104 a tsakanin birane 16 na ƙasashen uku.

Ƙasashen Canada da Mexico kowace za ta karɓi baƙuncin wasanni 13 a biranen ƙasashen biyar da suka haɗa da:

Mexico:

  • Mexico City
  • Guadalajara
  • Monterrey

Canada:

  • Toronto
  • Vancouver

Amurka:

Mafi yawan wasannin gasar za a buga su a ƙasar Amurka, inda za a yi wasa 78 a biranen ƙasar 11 da suka haɗa da:

  • Atlanta
  • Boston
  • Dallas
  • Houston
  • Kansas City
  • Los Angeles
  • Miami
  • New York/New Jersey
  • Philadelphia
  • San Francisco Bay Area
  • Seattle

Daga kan zagayen kwata fayinal, har a kammala gasar za a buga wasannin ne Amurka.

Yadda aka raba jadawalin gasar

Ƙasashe 48 ne za su fafata a gasar ta bana, wadda aka sake wa fasali, saɓanin 32 da suke shiga gasar a shekarun baya.

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya FIFA ce ta sake fasalin gasar tare da ƙara yawan ƙasashen da suke halartar gasar.

An kuma raba jadawalin gasar zuwa rukunoni 12 da suka ƙunshi ƙasashen huɗu-huɗu kowane.

Ga dai yadda aka raba jadawalin gasar

Ƙasashen da ake sa ran za su haska

Brazil ce kan gaba a lashe kofin gasar, wadda ta ɗauka sau biyar, sai Jamus da Italiya da suka ɗauki kofin sau huɗu kowannensu, da kuma Argentina mai uku, sai Faransa da Uruguay da suka ɗauka sau biyu kowane.

A gasar ta bana akwai ƙasashen da ake ganin za su haska a gasar ta bana, yayin da ake ganin za su iya lashe gasar ta bana.

Ƙasashe ne masu zaƙa-ƙuran ƴan wasa da a yanzu ludayinsu ke kan dawo.

Masana harkokin wasanni na lissafo wasu ƙasashe da ake ganin za su yi bajinta a gasar ta bana da suka haɗa da:

Ingila da Sifaniya da Faransa da Jamus da Brazil da Argentina da Norway da kuma Morocco.

Yaushe za a buga wasan ƙarshe?

Za a buga wasan ƙarshen na Gasar Kofin Duniya ta bana a ranar 19 ga watan Yuli mai zuwa.

Za a buga wasan na ƙarshe ne tsakanin ƙasashen da suka kai matakin a filin wasa na MetLife Stadium da ke birnin New Jersey/New York na Amurka.

Kyaututtukan da za a raba a gasar

A gasar ta bana, an ƙara kuɗin ladan lashe kofin da matakin da tawagogin za su kai da sama da kashi 50% idan aka kwatanta da abin da aka kashe a gasar da ta gabata ta 2022 a Qatar.

Tawagogin da suka ƙare a matsayi na 33 zuwa 48 za su samu kuɗi miliyoyin daloli, tare da ƙarin kuɗin shiri daga FIFA domin atisaye da sufuri da tsare-tsare da sauransu.

Sannan ƙasashen da ba su tsallake zagaye na farko ba, kowacce za ta samu dala miliyan 9.

Haka kuma za a bai wa kowace ƙasa - da ta samu gurbi a gasar - dala miliyan 1.5 domin shirye-shiryen zuwa gasar, wanda hakan ke nufin kowace ƙasa za ta samu aƙalla dala miliyan 10.5.

Me za a bai wa ƙasashen da suka yi zarra?

Hukumar FIFA - wadda ke shirya gasar - ta keɓe dala miliyan 50 ga ƙasar da ta samu nasarar lashe gasar ta bana.

Wadda ta zo ta biyu a gasar za ta za samu ladan dala miliyan 33.

Ƙasar da ta yi ta uku a gasar za ta samu kyautar dala miliyan 29, yayin da ta huɗu za ta samu kyautar dala miliyan 27