An rufe makarantu fiye da 200 a Afirka ta Kudu saboda iska mai ƙarfi
Hukumomi a Lardin Western Cape a Afrka ta Kudu sun rufe makarantu saboda yanayi na iska da ruwa da ke barazana ga harkoki.
Hukumomin sun kuma yi gargaɗin za a samu tsaiko wajen tashin jirage, za a soke tashin wasu sannan wasu jiragen na iya sauya hanya saboda rashin kyawun yanayin sakamakon iska mai ƙarfi da mamkon ruwan sama.
Fiye da makarantu 200 aka rufe bayan da aka samu yanayin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliya a sassan Lardin na Western Cape da ke Afirka ta Kudu.
Jami'ai sun ce yanayin ya yi ɓarna a makarantu da dama.
Iska da aka yi mai ƙarfi ta ɓaɓɓako bishiyoyi tare da toshe tituna da kuma zubar da rufin wasu gine-gine.
A ranar Litinin ne gwamnati ta ayyana rashin kyawun yanayin a matsayin babban bala'i.