KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Talata 12/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Hare-hare sun yi ajalin aƙalla mutum shida a Dafur

    Aƙalla mutum shidda ne suka rasu sakamakon hari ta sama da aka kai a birnin Al-Daein da ke yankin Dafur na ƙasar Sudan.

    Hukumomi sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa an kuma jikkata ƙarin wasu mutum biyar wadanda ke tsananin jin jiki.

    Mazauna yankin sun ce jirgi marar matuƙi na sojoji ne ya fada a wani gini a yau Talata. sai dai sojojin ba su ce komai kan lamarin ba.

  2. Ba zan janye daga takara ba - Buba

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Mahmoud Sadis Buba (Abin Alʼajabi) wani ɗan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Sabon Garin Zariya ne da ke jan hankali saboda yanayin halittarsa. Abin Alʼajabi ya shaida wa BBC dalilin da ya sa ya fito wannan takara.

  3. Iran ta kai ƙarar Amurka gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe ta duniya

    Gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ta shigar da ƙorafi a kan Amurka a gaban Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafe tsakanin Iran da Amurka da ke Hague a ƙasar Netherlands.

    Kamfanonin dillancin labaran Iran sun ce ƙarar na zargin gwamnatin Amurka da karya yarjejeniyar Algiers, wata yarjejeniya da aka cimma a watan Janairun shekarar 1980 ta hanyar shiga tsakani na ƙasar Algeria domin kawo ƙarshen rikicin garkuwa da jami’an diflomasiyyar Amurka a Iran.

    Daga cikin korafe-korafen da Iran ta gabatar akwai “yaƙin kwanaki 12”, hare-haren da suka fara daga ranar 28 ga Fabrairu, da kuma takunkumin tattalin arziki da Amurka ta ƙaƙaba mata.

    Bisa yarjejeniyar Algiers, Amurka ta yi alƙawarin cewa ba za ta tsoma baki kai tsaye ko a fakaice cikin harkokin cikin gida, siyasa da kuma harkokin sojin Iran ba.

    A halin yanzu kuma akwai wasu ƙorafe-ƙorafe guda biyu da Iran ta shigar a kan Amurka a gaban Kotun Ƙasa da Ƙasa ta ICJ, ɗaya kan ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA, ɗaya kuma kan ƙwace kusan dala biliyan biyu daga kadarorin Babban Bankin Iran.

  4. Iran ta gudanar da atisayen soji ba tare da sanarwa ba

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin-juya-halin Iran ta IRGC ta gudanar da wani atisayen soji mai suna “Shugaban Shahidi” ba tare da sanarwa ba.

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an shirya atisayen ne domin gwada hanyoyin tunkarar abokan gaba da kuma tantance dabarun yaƙi.

    Birgediya Janar Hassan Hassanzadeh ya ce a yayin atisayen an samu nasarar gwada dukkan dabaru da salon aiki na runduna da kuma na ɗaiɗaikun jami’ai domin ƙara ƙarfin yaƙi da tunkarar duk wani motsi daga maƙiya.

  5. 'Amurka ta kashe dala biliyan 29 kan yaƙin Iran'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar a ranar Talata cewa kuɗin da Amurka ta kashe kan yaƙin Iran ya kai kusan dala biliyan 29, bisa sabon ƙiyasin da aka fitar yayin zaman sauraron kasafin kuɗi a Majalisar Dokokin ƙasar.

    Sabon adadin ya fi wanda sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayar kimanin makonni biyu da suka gabata da dala biliyan huɗu.

    Pete Hegseth tare da Janar Dan Kaine sun bayyana haka ne yayin da suke kare buƙatar kasafin kuɗin tsaro ta shekarar 2027 da ta kai dala tiriliyan 1.5, inda aka tambaye su kan kuɗin da aka kashe a yaƙin Iran.

    Jules Hurst, shugaban sashen kuɗi na Pentagon wanda shi ma ya halarci zaman, ya ce a ranar 29 ga Afrilu, an kiyasta kuɗin da aka kashe kan yaƙin da dala biliyan 25.

    Sai dai ya ce tawagar hafsoshin soji da masu binciken kuɗi na ci gaba da sa ido kan sabon ƙiyasin.

  6. Mun ƙara faɗin mashigar Hormuz zuwa fiye da mil 200 - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran ta ce ta ƙara faɗaɗa mashigar Hormuz daga mil 20 zuwa sama da mil 200 bayan yaƙin na ƙasar na baya-bayan nan da Amurka.

    Mataimakin shugaban sashen sojin ruwa na rundunar ta IRGC, Mohammad Akbarzadeh ya shaida wa gidan talbijin na Iran cewa a yanzu yankin ya zama wani muhimmin yanki.

    ''A yanzu mashigar ta ƙara faɗi, wadda za a iya gudanar da ayyuka a cikinta'', kamar yadda ya bayyana.

    A cewar Akbarzadeh sun ƙara faɗin mashigar zuwa aƙalla kilomita 500.

    ''A baya-bayan nan Amurka ta yi yunƙurin ƙwace iko da mashigar, amma sai sojojinmu suka hana hakan'', kamar yadda ya bayyana.

  7. Ghana ta soma shirin kwashe ƴan ƙasar daga Afirka ta Kudu

    An yi ta zanga-zangar yaƙi da baƙi tsawon makonni a sassan Afirka ta Kudu inda masu zanga-zangar ke neman mutanen da suka shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya su tattara nasu ya nasu su fice daga ƙasar.

    Asalin hoton, GHANA HIGH COMMISSION IN SOUTH AFRICA

    Hukumomin Ghana sun ce mutum fiye da 200 sun nuna buƙatar a kwashe su daga Afirka ta Kudu saboda fargabar halin da rayuwarsu za ta iya shiga.

    Sun ce suna fargabar cin zarafi da barazana daga wajen ƴan Afirka ta Kudu yayin da suke ci gaba da kiraye-kiraye kan baƙi su fice daga ƙasarsu.

    An yi ta zanga-zangar yaƙi da baƙi tsawon makonni a sassan ƙasar inda masu zanga-zangar ke neman mutanen da suka shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya su tattara nasu ya nasu su fice daga ƙasar.

    Sun yi zargin cewa baƙi da suka shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya ne ke aikata miyagun laifuka a ƙasarsu tare da karɓe musu ayyuka.

    Hukumomin Ghana dai sun yi allahwadai da cin zarafin da ake nuna wa ƴanƙasar.

    Ƙasashe kamar Najeriya da Angola da Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi tsokaci kan abin da suka kira cin zarafin baƙi da ke faruwa da sunan zanga-zangar yaƙi da baƙin haure.

  8. Isra'ila ta amince da hukunta Falasɗinawan da aka samu da hannu a harin Hamas na Oktoban 2023

    Majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wata doka da za ta kafa kotun soji ta musamman da za a gurfanar da Falasɗinawa da ake zargi da hannu a harin da ƙungiyar Hamas ta kai a watan Oktoban 2023.

    Kotun dai za ta iya yanke wa waɗanda aka samu da laifi hukuncin kisa.

    Za a gudanar da shari'o'in ne a birnin Qudus kuma a watsa kai tsaye a shafukan Intanet.

    Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce wannan mataki zai tauye ‘yancin waɗanda ake yi wa shari'ar.

    Har ila yau, akwai iƙirarin cewa an tattara wasu shaidu ne ta hanyar azabtarwa, zargin da hukumomin Isra'ila suka musanta.

  9. Sojoji sun musanta rahoton kisan fararen hula a hare-haren Zamfara

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, JORIS BOLOMEY/AFP via Getty Images

    Rundunar soji a Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kashe farar hula yayin hare-hare ta sama da aka kai a ƙauyen Tumfa da ke jihar Zamfara.

    Kakakin rundunar, Micheal Onoja ya yi watsi da iƙirarin cewa an kai hare-haren ne kan farar hula.

    Martanin nasa na zuwa ne bayan da ƙungiyar Amnesty da ke kare haƙƙin bil adama ta buƙaci gwamnati ta yi bincike kan rahoton zargin kisan farar hula fiye da 100 a wani hari ta sama da aka kai a kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi.

    Sai dai Manjo Onoja ya ce sojoji sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri game da taron manyan jagororin ƴan ta'adda daga sassan yammacin Afirka.

    Ya kuma ce a kan fararen hula aka shirya harin ba.

    "Ba farar hula aka shirya kai wa hare-haren ba kuma ana yin komai domin kare su farar hular," in ji shi.

    Ya tabbatar cewa sojoji na gudanar da ayyuka a yankin inda ya ce suna ci gaba da yin aiki bisa tsarin dokar kare haƙƙin bil adama ta ƙasa da ƙasa.

  10. 'Bai kamata a mayar da mashigar Hormuz makamin yaƙi ba'

    ..

    Asalin hoton, ..

    Ministan harkokin wajen Turkiyya, wanda ya yi bulaguro zuwa Qatar ya ce ƙasarsa za ta goyi bayan yunƙurin buɗe mashigar Hormuz.

    Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai tare da takwaransa na Qatar a birnin Doha, Hakan Fidan ya ce ''bai kamata a mayar da mashigar Hormuz makamin yaƙi ba''.

    Firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani tare da ministan harkokin wajen ƙasar sun ce bai kamata Iran ta riƙa amfani da mashigar ba wajen ƙuntata wa ƙasashen yankin Gulf.

    Abdulrahman Al Thani ya ce a baya-bayan nan ya yi bulaguro zuwa Amurka da nufin taimakawa don kawo ƙarshen yaƙin Iran

  11. Har yanzu ba a yaƙi cutar Hantavirus ba - WHO

    Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO ya ce har yanzu ba a kai ƙarshen yaƙi da cutar Hantavirus ba, duk da nasarar da aka samu ta kawar da jirgin da aka samu ɓullar cutar.

    Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce babu wata alama da ke nuna an samu ɓarkewar cutar, sai dai komai ka iya sauyawa.

    Ya ce haƙƙin kula da lafiyar waɗanda suka kamu aka mayar da da su gida ya rataya ne kan ƙasashensu.

    Ya ce zuwa yanzu an tabbatar da mutum goma 11 sun kamu da cutar inda mutum uku daga ciki suka rasu.

  12. Sojoji sun daƙile yunƙurin buɗe haramtattun cibiyoyin tace mai a Rivers

    .

    Asalin hoton, @NigerianNavy

    Rundunar sojin ruwa a Najeriya ta daƙile ƙoƙarin ɓatagari na kafa cibiyar tace mai ba bisa ƙa'ida ba tare kuma da ƙwato tarin albarkatun mai da ake zargi an tace su ta haramtacciyar hanya a samamen da ta kai a sassan Rivers.

    Bayanin na ƙunshe cikin sanarwar da daraktan yaɗa labarai na rundunar, Navy Capt. Abiodun Folrunsho.

    Folorunsho ya ce an kai samamen ne karƙashin rundunar Delta Sentinel a wani ɓangare na ayyukan yaƙi da satar ɗanyen mai da yi wa tattalin arziki maƙarƙashiya a yankin Neja Delta.

    Ya ce jami'ansu sun daƙile yunƙurin ɓatagarin na kafa haramtattun cibiyoyin tace mai a ƙaramar hukumar Bonny bayan samun bayanan sirri.

  13. An rufe makarantu fiye da 200 a Afirka ta Kudu saboda iska mai ƙarfi

    Bishiya ta faɗa kan mota

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a Lardin Western Cape a Afrka ta Kudu sun rufe makarantu saboda yanayi na iska da ruwa da ke barazana ga harkoki.

    Hukumomin sun kuma yi gargaɗin za a samu tsaiko wajen tashin jirage, za a soke tashin wasu sannan wasu jiragen na iya sauya hanya saboda rashin kyawun yanayin sakamakon iska mai ƙarfi da mamkon ruwan sama.

    Fiye da makarantu 200 aka rufe bayan da aka samu yanayin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ambaliya a sassan Lardin na Western Cape da ke Afirka ta Kudu.

    Jami'ai sun ce yanayin ya yi ɓarna a makarantu da dama.

    Iska da aka yi mai ƙarfi ta ɓaɓɓako bishiyoyi tare da toshe tituna da kuma zubar da rufin wasu gine-gine.

    A ranar Litinin ne gwamnati ta ayyana rashin kyawun yanayin a matsayin babban bala'i.

  14. Fasinjojin ƙarshe na jirgin da aka samu ɓarkewar hantavirus sun isa Netherlands

    Fasinjoji

    Asalin hoton, Reuters

    Fasinjoji na ƙarshe da ma'aikatan jirgin da aka kwashe daga jirgin ruwan da aka samu ɓarkewar cutar hantavirus sun sauka a Netherlands.

    Jiragen sama biyu sun kwashe kusan mutane ashirin da takwas daga tsibirin Tenerife na ƙasar Sifaniya zuwa birnin Eindhoven na ƙasar Netherlands.

    Za a killace su a ƙasar na tsawon wani lokaci kafin su koma gida. A yanzu haka jirgin ruwan mai suna MV Hondius yana kan hanyarsa ta zuwa Netherlands ɗauke da ma'aikata ƴan ƙalilan.

    Da yake magana a Tenerife bayan an kwashe fasinjojin, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yaba da yadda hukumomin Sifaniya suka shawo kan lamarin

    Ya ce bai yi mamaki ba saboda ministocin duk suna nan suna sanya ido don su tabbatar da cewa komai ya tafi yadda ya kamata.

  15. An rantsar da Yoweri Museveni karo na bakwai

    Yoweri Museveni

    Asalin hoton, Getty Images

    An rantsar da Yoweri Museveni mafi daɗewa kan karagar mulki karo na bakwai a matsayin shugaban Uganda.

    An ayyana shi wanda ya yi nasara a zaɓn a aka yi a watan Janairu wanda cike yake da zarge-zargen rikici da maguɗi.

    Sama da shugabannin Afirka 30 da manyan baƙi ne suka halarci bikin rantsarwar da aka yi a Kampala, babban birnin ƙasar.

    Mista Museveni ya sha rantsuwar a gaban dubban magoya baya. Hakan ya sa ya zama ɗaya cikin shugabannin Afirka da suka daɗe kan mulki.

    Jam'iyyun hamayya sun ƙauracewa taron inda suka ce zuwansu zai zama kamar sun amince dasakamakon zaɓen da ke cike da taƙaddama.

    Tuni babban abokin hamayyarsa, Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine ya fice daga ƙasar inda yake iƙirarin cewa rayuwarsa na cikin haɗari tun bayan da ya yi zargin cewa an murɗe zaɓ.

  16. Starmer na fuskantar matsin lamba ya yi murabus

    Sir Keir Starmer

    Asalin hoton, PA Media

    Firaministan Biritaniya Sir Keir Starmer na fuskantar matsin lamba da ya yi murabus, sakamakon kashin da jam'iyyarsa ta sha a faɗin Birtaniya a zaɓen da aka gudanar a makon jiya.

    Ƴan majalisar wakilai sama da saba'in ne suka yi kira gare shi da ya sauka daga mulki.

    Wakilin BBC ya ce Birtaniya ta yi Firaminista huɗu a cikin shekaru huɗu da suka gabata. Yanzu kuma ga wani ya tsinci kansa a tsaka mai wuya; yayin da yan jam'iyyarsa ke tayar da ƙayar baya, kuma majalisar ministocinsa ta rabu kan ya tsaya ko ya tafi.

    Manyan ministoci da dama sun buƙace shi da ya fitar da jadawalin saukarsa daga karagar mulki.

    A jiya Litinin Sir Starmer ya dage cewa ba zai yi murabus ba, kuma zai yaƙi duk wani ƙalubale ga shugabancinsa.

  17. Mutum bakwai sun mutu a fashewar da ta faru a Pakistan

    Aƙalla mutum bakwai, har da ƴansanda biyu sun mutu a wata fashewa da ta faru a wata kasuwa da ke a Pakistan.

    Fashewar da ta faru a Serai Naurang ta raunata gomman mutane.

    Wannan ne hari na biyu mafi muni da ya faru a yankin cikin kwana buɗu.

    Sojojin Pakistan sun daƙile hari na uku. Sun ce yunƙurin kutsawa da wata babbar mota cike da abubuwan fashewa kan shingen binciken jami'an tsaro kusa da iyakar Khyber Pakhtunkhwa da Punjab bai yi nasara ba.

    Farar hula ɗaya ne ya mutu a lamarin.

  18. An kashe farar hula fiye da 400 a Afghanistan tun Oktoba - MDD

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Alƙaluman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar sun ce sama da farar hula ɗari huɗu ne aka kashe a Afghanistan tun watan Oktoba, a rikicin kan iyaka da ya ɓarke tsakanin ta da Pakistan.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutum ɗari biyu da sittin da tara (269) sun mutu a wani hari da jirgin saman yaƙin Pakistan ya kai kan wata cibiyar gyara halin masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi.

    Iyalan waɗanda harin ya rutsa da su sun ce akasarin waɗanda aka kashe maza ne da ke ƙoƙarin rabuwa da jarabar shan ƙwaya.

    Pakistan dai ta musanta wannan zargin, tana mai cewa tana kai hari ne kan cibiyoyin soji da kayayyakin ayyukan ta'addanci.

    Tana zargin gwamnatin Taliban da ba da mafaka ga mayaƙan da ke kai hare-hare ta kan iyaka.

  19. A binciki "asarar rayuka fiye da 100" sanadin harin soji a Zamfara - Amnesty

    Tambarin Ƙungiyar Amnesty

    Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL

    Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan harin da sojoji suka kai ta sama wanda rahotanni suka ce ya kashe aƙalla farar hula 100 a kasuwar Tumfa da ke ƙaramar hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

    A cewar ƙungiyar, tun da ƙarfe 12 na ranar Lahadin da ta gabata ne aka ga jiragen yaƙin soji suna shawagi a saman kasuwar da ke ci mako-mako, kafin su sake dawowa su fara ruwan bama-bamai da misalin ƙarfe 2 na rana.

    Daraktan ƙungiyar Amnesty International a Najeriya, Malam Isa Sanusi, ya ce bisa bayanan da suka tattara, kusan duka waɗanda abin ya shafa farar hula ne.

    "Iran wannan ce ta faru a watan da ya gabata a wani gari tsakanin Borno da Yobe inda aka ka hari a kasuwa aka kashe mutum 10 a harin, cikin waɗanda aka kashe har yanzu ba a samu sheda cewa akwai waɗanda ake zargi mayaƙa ba ne." in ji Isa Sanusi.

    Ya ƙara da cewa a makon da ya gabata ma an samu irin wannan lamari a jihar Neja, inda mutane aƙalla 12 suka rasa ransu - yawancinsu ƙananan yara.

    A cewarsa, tun daga shekarar 2017 ake samun irin wannan lamari a arewa maso gabashin Najeriya musamman a jihar Borno inda a cewarsa,ana kai hare-hare da sunan yaƙi da Boko Haram.

    "Ya kamata gwamnati ta tsaya a yi magana da sojoji, kada aikinsu ya zama sanadin asarar rayukan farar hula da mutanen da ba su ji ba su gani ba." in ji shi.

    A cewarsa, a tsarin doka ta ƙasa ta ƙasa ta ƴancin ɗan'adam, bai kamata a cutar da farar hula ba a duk wani aikin samar da tsaro.

  20. Za mu mayar da martani idan aka kai mana hari - Iran

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran Mohammad Bagher Ghalibaf

    Asalin hoton, EPA

    Iran ta ce dakarunta a shirye suke su mayar da martani kan duk sabbin hare-hare da za a kai mata, bayan da Shugaba Donald Trump ya ce a halin yanzu yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen tana tangal-tangal.

    Kakakin majalisar ƙasar Mohammad Ghalibaf ya ce Iran a shirye take ta fuskanci duk wani abin da ka iya faruwa.

    Wakilin BBC ya ce babbar tambaya a nan ita ce yanzu za a ci gaba da tattaunawa ne ko kuma za a koma a ci gaba da artabu.

    Tun da farko Mista Trump ya yi watsi da daftarin zaman lafiya na baya-bayan nan da Tehran ta gabatar kuma ya ce har yanzu yana fatan samun cikakkiyar nasara.

    Farashin ɗanyen mai dai ya tashi a kasuwar duniya ne bisa fargabar za a ci gaba da gwabza faɗa a yankin na gabas ta tsakiya.