'FIFA ta magance ƙorafe-ƙorafen Iran kan Gasar Kofin Duniya'
Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Iran Mehdi Taj ya gana da babban sakataren ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, Mattias Gradstrom a birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya inda suka tattauna ƙorafe-ƙorafen da ƙasar ke da su game da Gasar Kofin Duniya.
Mista Taj ya ce tattaunawar ta warware duka matsalolin da Iran ke ganin za su iya kawo mata tarnaƙi a bulagron nata domin halartar gasar.
Ya ce bayan tattaunawar a yanzu tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar za ta iya halartar gasar ba tare da wata matsala ba.
A nasa ɓangare sakaten na FIFA, Mattias Gradstrom ya yaba wa tattaunawar, wadda ya ce ta taimaka wajen magance damuwar da Iran ke da shi game da zuwanta gasar.
A gobe Litinin ne ake sa ran tawagar Iran za ta tashi zuwa sansanin horonta da ke Turkiyya, a shirye-shiryen zuwa gasar.