KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 17/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Lahadi 17/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. UAE ta ayyana harin da aka kai kusa da cibiyar nukiliyarta a matsayin 'ta'addanci'

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana harin da aka kai da jirage marasa matuka a kusa da tashar makamashin nukiliyarta da ke Barakah a matsayin "aikin ta'addanci ne na rashin hankali" wanda zai ƙara dagula lamura a yankin.

    Ma'aikatar harkokin wajen UAE ta yi Allah-wadai da harin "da kakkausar murya" a cikin wata sanarwa da ta fitar, tare da jaddada cewa tana da 'yancinta na diplomasiyya da na soja na mayar da martani ga duk wata barazana.

    Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen ta fitar ba ta ambaci daga inda harin ya fito ba, amma ta ce harin ya faɗa kan wani injin janerata da ke wajen cibiyar makamashin nukiliyar ta Barakah da ke yankin Dhafra, kuma jirgi mara matukin ya fito ne daga kan iyakar yammacin ƙasar.

    Ana samun tankiya tsakanin Iran da UAE a ƴan kwanakin nan.

    UAE ta bayyana cewa Iran ta kai hare-hare sama da 3,000 kan cibiyoyinta da wuraren farar hula a yaƙin da take yi da Amurka da Isra'ila.

  2. Har yanzu Ronaldo ya kasa lashe babban kofi a Al-Nassr

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu Cristiano Ronaldo bai samu damar lashe babban kofi ba a Al-Nassr, bayan da suka sha mamakin rashin nasara 1-0 a gida a hannun Gamba Osaka a wasan ƙarshe a AFC Champions League Two.

    A gaban magoya baya 26,000 a filin wasa na King Saud University Stadium, tun farko ƙungiyar Saudiyya ta Al-Nassr ce aka fi sa ran za ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mataki na biyu a nahiyar Asiya — wadda take daidai da Europa League ta Turai.

    Sai dai Deniz Hummet ya ci wa baƙi kwallo a Riyadh ranar Asabar.

    Ku karanta sauran cikakkun labaran wasanni kai tsaye a nan.

  3. Ranar Talata 26 ga watan Mayu za a yi tsayuwar Arafa

    Arafa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Dhul Hijjah a yau Lahadi.

    Cikin wata sanarwa da shafin Haramain ya wallafa a shafinsa na X, ya ce gobe Litinin ne ɗaya ga watan na babbar sallah.

    Hukumomin na Saudiyya sun kuma ce ranar Talata 26 ga watan Mayu ne za a yi tsayuwar Arafa, yayin da za a yi Idin babbar sallah ranar Laraba 27 ga watan na Mayu.

  4. Hukumomin Congo sun je wajen da Ebola ta kashe mutum 80

    Wasu manyan jami'an kiwon lafiya daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango na ziyara a lardin gabashin ƙasar, inda aka ruwaito cewa mutum 80 sun mutu sakamakon cutar Ebola.

    Ministan lafiya na ƙasar, Dr. Roger Kamba, da tawagarsa sun sha alwashin ƙara sa ido da tallafa wa ma'aikatan lafiya domin shawo kan matsalar.

    Sai dai hukumomi a birnin Kinshasa sun musanta sanarwar da hukumar lafiya ta duniya ta fitar na ɓullar cutar Ebola a babban birnin ƙasar.

    WHO ta ayyana cewa an samu ɓarkewar cutar bayan da aka gano wasu da suka kamu da ita maƙociyar ƙasar Uganda.

  5. Na fice daga harkokin siyasar Najeriya - AM Sadique Abubakar

    @CAS_AMSadique

    Asalin hoton, @CAS_AMSadique/X

    Tsohon babban hafsan sojin saman Najeriya kuma ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Bauchi a 2023, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (mai ritaya), ya bayyana ficewarsa daga harkokin siyasa.

    AM Abubakar ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X a yau Lahadi, inda ya bayyana cewa ba zai sake neman wata takarar siyasa ba.

    Ya ce a yanzu ba ya cikin kowace jam’iyyar siyasa, amma zai ci gaba da ba da gudummua a matsayinsa na ɗan Najeriya.

    “Na yi bankwana da siyasar Najeriya mai cike da gurɓacewar yanayi. A Yanzu ba na cikin kowace jam’iyya ko neman wata takara," in ji shi.

    A shekarar 2023 ne ya tsaya takarar gwamnan jihar Bauchi a jam'iyyar APC, sai dai bai yi nasara ba, yayin da aka yi tunanin zai sake neman takarar a 2027 kafin wannan sanarwar.

  6. PDP tsagin Tanimu Turaki za ta tantance ƴantakara sama da 3,000

    PDP

    Asalin hoton, PDP

    Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, tsagin Tanimu Turaki da ke samun goyon bayan gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ta ce za a tantance mutum 3,181, masu neman tsayawa takara ƙarƙashin jam'iyar domin shiga zaɓen 2027.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, PDP ta ce a zaman da ta gudanar na masu ruwa da tsaki karo na 104, ta amince da fara tantancewar daga ranar Talata 19 ga watan Mayu, 2026 a faɗin ƙasar.

    Ta kuma kafa kwamitin tantancewar tare da na sauraren ƙorafe-ƙorafe.

    Ta ce za ta tantance mutum 1 da ya ke son takarar shugaban ƙasa, sai wasu 112 da suke son takarar gwamna a jihohi daban-daban, da 198 da ke son takarar sanata, da 748 da ke son takarar majalisar tarayya da 2,122 masu son takarar majalisar dokokin jiha.

    Jam’iyyar PDP dai ta faɗa rikici sakamakon samun saɓanin shugabanci da ya barke tsakanin ɓangaren da Makinde ke marawa baya da kuma wanda Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ke goyon baya.

  7. Netanyahu ya ce zai tattauna da Trump ta waya kan batun Iran

    Netanyahu

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce zai tattauna da shugaban Amurka Donald Trump ta waya a yau.

    Netanyahu ya ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na musamman na jami'an gwamnati domin murnar ranar Jerusalam.

    "Idanunmu na kan Iran. Zan yi magana da abokinmu shugaba Trump a yau, kamar yadda nake yi a ƴan kwanakin nan," in ji shi.

    Netanyahu ya ce yana sa ran jin wani ci gaba da aka samu bayan ziyarar Trump China da wasu batutuwa.

    "Akwai abubuwa da dama da za su iya faruwa, kuma a shirye muke kan kowane yanayi," in ji Netanyahu.

  8. Sanatan Republican da ke adawa da Trump ya rasa tikitin takara

    Bill Cassidy

    Asalin hoton, Kevin Dietsch/Getty Images

    Fitaccen sanatan jam'iyyar Republican mai mulki a Amurka, wanda ya yi fice a adawa da Trump ya faɗi a zaɓen fitar da gwanin tsayawa takara.

    Sanata Bill Cassidy na ɗaya daga cikin sanatocin Repblican ƙalilan da suka kaɗa ƙuri'ar tsige Trump saboda harin da aka kai wa ginin majalisar a 2021.

    Ɗan majalisar dattawan ya zo na uku a zaɓen fitar da gwanin majalisar dattawan daga jihar Louisiana, bayan da ɗantakarar da Trump ya tsayar ya yi nasara a zaɓen.

    Tun da farko Mista Trump ya buƙaci ƴan jam'iyyar kada su zaɓi Lauren Boebert, yarmajalisar wakilai, wadda a baya ta kasance na gaba-gaba a goyon bayansa.

  9. Abin da ya sa hukumar tace fina-finan Kano ta dakatar da jarumanta biyu

    Amina Uba Hassan da Adam Garba

    Asalin hoton, Amina Uba Hassan/Adam Garba/FB

    Hukumar tace fina-finan Kano ta yi ƙarin haske da dalilan da ya sa ta dakatar da wasu jarumanta biyu har na tsawo shekara guda.

    Da safiya yau ne hukumar ta sanar da dakatar da Adam Garba da aka fi sani da Raba-gardama da kuma Amina Uba Hassan da ka fi sani da Jamila a cikin Labarina.

    Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan ganinsu a wani bidiyo da ta yi zargin ya saɓa wa tarbiya.

    ''An ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaftace tarbiya da nuna kyawawan ɗabi’u a dukkan bidiyoyin da ake fitarwa, tare da tabbatar da bin dokokin hukuma ya kamata'', in ji sanarwar.

    Hukumar ta ce bidiyon ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Jihar Kano.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa dakatarwar na nufin an hana su gudanar da duk wani aikin fim a Jihar Kano har tsawon shekara guda.

    ''Karya wannan doka na iya jawo hukunci mai tsauri kamar yadda yake ƙunshe cikin tanadin dokar da ta kafa hukumar'', kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Sanarwar ta kuma ambato shugaban hukumar, Abba El-Mustapha na kira ga daraktoci da masu shirya fina-finai su mutunta wannan umarnin dakatarwa.

    A nasa ɓangare jarumi Adam Garba ya nuna damuwarsa kan dakatarwar.

    Cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa ya ce ya kamata hukumar ta tuntuɓe su, domin jin abin da ya faru a bidiyon.

  10. Gobara ta tashi a tashar nukiliyar UAE

    gobara

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ce gobara ta tashi cibiyar nukiliyar ƙasar da ke yankin Al Dhafra, bayan harin jirgin maras matuƙi.

    Harin ya faɗa kan wanin injin wuta da ke wajen tashar nukiliyar ƙasar ta Barakah

    Hukumomin ƙasar sun ce babu labarin jikkata ko rasa rai a lamarin, saboda bai yi wata illa wa tashar ba.

  11. Iran ta naɗa kakakinta majalisar dokokinta matsayin lura da alaƙar China

    Iran ta naɗa kakakin majalisa dokokinta - wanda ya zama babban mai shiga tsakanin a yarjejeniyar ƙasar da Amurka - a matsayin wanda zai lura da alaƙar ƙasar da China.

    Naɗin Mohammad Bagher Ghalibaf na zuwa ne kwanaki bayan ziyarar Shugaba Trump na Amurka zuwa China.

    Shugaba Trump ya yi iƙirarin cewa Shugaban China Xi Jinping ya ce zai taimaka wajen buɗe mashigar Hormuz, sannan zai tabbatar ƙasarsa ba ta aike wa Iran tallafin soji ba..

    Tsohon babban mai shiga tsakani na Iran, Ali Larijani, da aka kashe a hare-hare ta sama watanni biyu da suka gabata, shi ma da na irin wannan muƙami game da China.

  12. 'FIFA ta magance ƙorafe-ƙorafen Iran kan Gasar Kofin Duniya'

    Tawagar Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar ƙwallon ƙafar Iran Mehdi Taj ya gana da babban sakataren ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA, Mattias Gradstrom a birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya inda suka tattauna ƙorafe-ƙorafen da ƙasar ke da su game da Gasar Kofin Duniya.

    Mista Taj ya ce tattaunawar ta warware duka matsalolin da Iran ke ganin za su iya kawo mata tarnaƙi a bulagron nata domin halartar gasar.

    Ya ce bayan tattaunawar a yanzu tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar za ta iya halartar gasar ba tare da wata matsala ba.

    A nasa ɓangare sakaten na FIFA, Mattias Gradstrom ya yaba wa tattaunawar, wadda ya ce ta taimaka wajen magance damuwar da Iran ke da shi game da zuwanta gasar.

    A gobe Litinin ne ake sa ran tawagar Iran za ta tashi zuwa sansanin horonta da ke Turkiyya, a shirye-shiryen zuwa gasar.

    Tawagar Iran

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Makaken jirgin ruwan yaƙin Amurka na USS ya koma ƙasar bayan yaƙin Iran

    jirgin ruwan yaƙi na Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa makaken jirgin ruwan yaƙin ƙasar, na USS Gerald R. Ford da akja tura yankin Gabas ta Tsakiya kafin fara yaƙin Iran ya koma Amurka a ranar Asabar bayan aikin kwanaki 326.

    Wannan ne lokaci mafi tsawo da jirgin - wanda ke ɗaukar jiragen yaƙi, kuma suke sauka a kansa - ya yi tun bayan yaƙin Vietnam.

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegsett ya je tashar ruwa ta Norfolk da ke jihar Virginia domin tarbar jirgin, wanda shi ne mafi girma da ke jiragen sama.

    A cewar sojojin Amurka, jirgin ta taimaka a hare-haren da ƙasar ta ƙaddamar a yankin Karebiyan, inda sojojin Amurka suka ƙaddamar da hare-hare kan ƙananan jiragen ruwan masu safarar ƙwaya, tare da ƙwace tankokin mai da kuma kama shugaban Venezuela Nicolas Maduro da mai ɗakinsa.

    Daga nan kuma jirgin ya nufi yankin Gabas ta Tsakiya, domin taimakawa a hare-haren da Amurka ta ƙaddamar kan Iran.

    A tsawon wannan lokaci, akwai lokacin da gobara ta tashi a sashen wanke-wanke na jirgin inda ta ji wa ma'aikata biyu mummunan raunuka tare da lalata kusan gadaje 100.

    An kuma riƙa samun rahotonnin matsaloli a sashen banɗakunan jirgin da sashen tsaftace shi.

  14. Hezbollah ta ce ta kai hari kan sansanin sojin Isra'ila arewacin ƙasar

    Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta kai hari da jirage marasa matuƙa kan wani sansanin sojin Isra'ila a arewacin ƙasar, yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta mai tangal-tangal ƙasashen ɓangarorin biyu ta kasa dakatar da hare-haren da aka fara tun a ranar 2 ga watan Maris.

    Ƙungiyar wadda ke samun goyon bayan Iran ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar cewa dakarunta sun kai hari kan sansanin soji na ''Yaara garisson'' ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa.

    A baya Hezbollah ta sha bayyana kai hare-hare kan dakarun sojin Isra'ila a kudancin Lebanon, inda a cewar ƙungiyar, Isra'ila ta kwace wasu yankunan a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.

  15. Kazakhstan ta aika wa Iran manyan motocin kayan agaji 30

    agajji

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan birnin Sarakhs a Iran ya ce manyan motoci ɗauke da kayan agaji daga Kazakhstan sun ira lardin.

    Majid Beiki ya ce kayan agajin da suka karɓa sun haɗa da fulawa da magunguna da kayyakin gwangwani a sikari waɗanda suka isa ƙasar.

    Mista Beiki ya bayyana kayan agajin a matsayin alamar jin kai da tsausayawa daga maƙwabtan ƙasashe.

    Birnin Sarakhs na yankin arewa maso gabashin lardin Khorasan Razavi a kusa da kan iyakar ƙasar da Turkmenistan da ke tsakiyar Asiya.

  16. Sarkin Musulmin Najeriya ya buƙaci a fara duba watan babbar sallah daga yau

    Sarkin Musulmi

    Asalin hoton, Sultanate Council Sokoto

    Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya buƙaci al'ummar musulmin ƙasar su fra duban watan babbar sallah daga yau Lahadi 17 ga watan Mayun 2026.

    Cikin wata sanarwa da fadar ta fitar ta ce a kai rahoton ganin watan ga dagaci ko hakimi mafi kusa, domin a sanarwa fadar Sarkin Musulmin, wanda shi ne shugaban kwamitin ƙoli kan Addinin Musulunci a Najeriya.

    Akan gudanar da babbar sallah a ranar kowace 10 ga watan Zulhijja, kwana guda bayan tsayuwar Arfa da mahajjata ke yi a Saudiyya.

    Al'ummar Musulmi kan yanka dabbobi domin yi layya a lokacin babbar sallar, yayin da mahajjata ke yin hadaya.

  17. Marabanku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukan sada zumunta.