KAI TSAYE, Alonso zai fara aiki da Chelsea da zarar an kammala kakar bana

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 17 zuwa 24 ga watan Mayun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Mourinho ya kammala kakar bana ba tare da rashin nasara ba a Benfica., Benfica

    Jose Mourinho ya kammala kakar gasar lig ta bana ba tare da rashin nasara ba a Benfica, amma duk da haka ya kare a matsayi na uku a teburin babbar gasar ƙwallon ƙafa ta Portugal.

    Benfica ta doke Estoril da ci 3-1 a wasansu na ƙarshe a kakar nan, wanda ya tabbatar da cewa ta kammala Primeira Liga ba tare da rashin nasara ba, wadda ta ci wasa 23 tda kunnen doki 11.

    Sai dai ta kammala kakar da maki 80 — maki takwas a bayan wadda ta lashe kofin, Porto, sannan maki biyu tsakani da Sporting mai matsayi na biyu, sannan Benfica ta uku

    Nasarar da suka samu a kan Estoril za ta iya wasan ƙarshe da Mourinho ya jagoranci Benfica, saboda yana matakin ƙarshe na tattaunawa domin zama sabon kocin Real Madrid, shekaru 13 bayan wa’adinsa na farko a Bernabeu.

    Kociyan mai shekara 63 ya koma Benfica a watan Satumban bara kan kwantiragin shekaru biyu, amma shugaban Real Madrid, Florentino Perez na son ɗaukarsa aiki, bayan da suka fuskanci kalubale a bana

    Wannan ba shi ne karon farko da Benfica ta yi kakar lig ba tare da shan kashi ba, amma ta kasa lashe kofin gasar ba.

    A kakar 1977-78, Porto ta yi kunnen doki ƙasa da Benfica da wasanni biyu kuma ta lashe kofin lig saboda bambancin ƙwallaye.

    Benfica ta Mourinho yanzu ta shiga jerin ƙungiyoyin Turai kaɗan da suka yi kakar lig ba tare da shan kashi ba amma suka kasa lashe gasar, tare da FC Sheriff ta Moldova a kakar 2024-25 da kuma Red Star Belgrade ta Serbia a kakar 2007-08.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Har yanzu Ronaldo na jiran ranar da zai fara lashe kofi a Al-Nassr

    Har yanzu Cristiano Ronaldo bai samu damar lashe babban kofi ba a Al-Nassr, bayan da suka mamakin rashin nasara 1-0 a gida a hannun Gamba Osaka a wasan ƙarshe a AFC Champions League Two.

    A gaban magoya baya 26,000 a filin wasa na King Saud University Stadium, tun farko ƙungiyar Saudiyya ta Al-Nassr ce aka fi sa ran za ta lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mataki na biyu a nahiyar Asiya — wadda take daidai da Europa League ta Turai.

    Sai dai Deniz Hummet ya ci wa baƙi kwallo a Riyadh ranar Asabar.

    Wannan sabon koma baya ne ga Ronaldo bayan da a kwanaki huɗu baya da golan Al-Nassr Bento ya ci daf da tashi a ƙarshen wasa, wanda ya sa tauraron Portugal ɗin ya ci gaba da jiran babban kofi tun bayan komawarsa Al-Nassr a watan Janairun 2023.

    Wannan sakamakon ya bai wa abokan hamayyarsu na gasar Saudi Pro League, Al-Hilal, damar yin kunnen doki 1-1 tare da ci gaba da kasancewa maki biyu kacal a bayan Al-Nassr mai jagoranci yayin da wasa ɗaya ya rage a gasar.

    Sai dai ƙungiyar Ronaldo za ta zama zakarun Saudiyya karo na 11 — kuma na farko tun 2019 — idan ta doke Damac a gida ranar Alhamis.

    Al-Hilal, wadda ta lashe gasar sau 21, za ta buga wasan ƙarshe a kakar nan a gidan Al-Fayha a lokaci guda ranar Alhamis.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Daga Jaridu

    Juventus na shirin sake ruɓanya himmarta wajen ganin ta ɗauko ɗan wasa Bernardo Silva, da ke shirin barin Manchester City a kakar wasannin nan, wajen ganin sun yi nasarar kan Atletico Madrid da Barcelona wajen siyen ɗan wasan. (Corriere dello Sport - in Italian)

    Ana sa ran daraktan wasanni Bercelona Deco zai halarci gasar wasan ƙarshe na gasar F A a Ingila, don kallon yadda ɗan wasan Chelsea Joao Pedro zai taka leda, duk da cewar Chelsea ɗin ba ta son siyar da ɗan wasan. (Mail)

    Coventry City na son ɗauko ɗan wasan Netherlands Georginio Wijnaldum, da kwantaraginsa zai ƙare da Al-Ettifaq, a kakar wasannin nan. (Football Insider)

    Everton na harin ɗan wasan Burnley loum Tchaouna, da ke cikin tawagar ƴan wasan Faransa ƴan shekaru ƙasa da 21. (Football Insider)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. , Daga Jarida

    SC Freiburg na son siyen ɗan wasan gaban Leeds Unite Wilfried Gnonto, yayin da Leeds United ɗin ta ke shirin siyar da ɗan wasan, ko kuma ta bayar da shi aro amma da alƙawarin siyensa nan gaba. (Sky Sports Germany)

    Ana danganta mai tsaron bayan Italiya Alessandro Bastoni da Barcelona, sai dai ya na son ci gaba da zama a Inter Milan, idan har komawar ta sa zuwa ƙungiyar ta Spaniya ba ta tabbata ba. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

    Juventus na iya duba yiwuwar baiwa ɗan wasan Brasil Douglas Luiz, da ke buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a Aston Villa, damar burge mai horar da ƴan wasan ƙungiyar ko kuma ya siyar da shi. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

    Bayern Munich na son ɗan wasan Atalanta Charles De Ketelaere, a wani shirin ko ta kwana idan aka sami rashin tabbacin komawar ɗan wasan Newcastle United Anthony Gardon bai yi nasara ba. (Football Italia)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Napoli ta samu tikitin Champions League da za ta iya sayen Hojlund, Napoli

    Ana sa ran Rasmus Hojlund zai koma Napoli daga Manchester United, bayan da ya taimaka wa ƙungiyar ta Serie A wajen tabbatar da samun gurbin shiga Gasar Zakarun Turai ta Champions Leagueta baɗi, bayan nasarar da suka samu a kan Pisa.

    Ɗan wasan tawagar Denmark ɗin, wanda ya koma Naples buga wasannin aro a watan Agusta, ya bai wa tsohon abokin wasansa na United Scott McTominay ƙwallon farko a minti na 21 da ya zura a raga a filin wasa na Stadio Romeo Anconetani.

    Mai tsaron baya Amir Rrahmani ya ƙara ta biyu, kafin Hojlund ya ci ta uku a karin lokaci, wanda ya kai yawan ƙwallayensa da ya zura a raga a Serie A zuwa 11 a wannan kakar.

    Nasarar ta tabbatar wa Napoli za ta kammala kakar a cikin huɗun farko a Serie A, inda ƙungiyar Antonio Conte ke da tazarar maki biyar a kan Como mai matsayi na biyar yayin da wasa ɗaya ya rage.

    A matsayin wani ɓangare na yarjejeniya tsakanin Man United da ƙungiyar Italiya, yanzu Napoli za ta biya kuɗin sayen Hojlund kan fam miliyan 38.

    Ɗan wasan mai shekara 23 ya ci ƙwallo 15 tare da bayar da takwas aka zura a raga a wasa 43 a dukkan kakarnan, tun bayan komawarsa Italiya, inda ya taɓa taka leda a Atalanta kafin ya koma Man United kan kuɗin fam miliyan 64 a shekarar 2023.

    Napoli za ta tabbata a matsayi na biyu idan ta doke Udinese a wasan ƙarshe a kakarbana.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Fernandes ya yi kan-kan-kan a yawan bayar da ƙwallo a zura a raga a Premier League, Manchester United

    Bruno Fernandes ya yi kan-kan-kan a tarihin bayar da bayar da ƙwallo a zura a raga a kakar gasar Premier League, yayin da Manchester United ta doke Nottingham Forest 3-2 a wasan mako mai na 37 da suka buga ranar Lahadi a Old Trafford.

    Ƙwallon da Fernandes ya bai wa Bryan Mbeumo ya zura a raga da sakamakon ya koma 3-1, hakan ya sa kyaftin ɗin United ya yi kafaɗa da kafaɗa da Thierry Henry da Kevin de Bruyne wajen bayar da ƙwallo a zura a raga karo na 20 a kaka guda — yayin da wasa ɗaya ya rage a kammala wasannin bana.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.