Mourinho na son Rashford a Madrid, Everton na harin Osula

Marcus Rashford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marcus Rashford
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Jose Mourinho da ke shirin komawa Real Madird na harin dauko ɗan wasan gaban Ingila Arcus Rashford. da ke taka leda a matsayin ɗan wasan aro a Barcelona daga Manchseter United. (Sport - in Spanish)

Everton da Auston Villa na son ɗan wasan Newcastle William Osula. (The I)

Baba wani ci gaba kan batun tsaiwata kwantaragin ɗan wasan bayan Ingila Levi Colwil, da Chealsea, sai dai za a iya komawa terburin tattaunawa a kaka mai zuwa. (Sky Sports)

Manchester United da Chelsea na son ɗauko ɗan wasan gaban Jamus Karim Adeyemi a wannan kaka, inda Borussia Dortmund ke son siyar da shi kan farashin da ya dace. (Teamtalk)

Ɗan wasan bayan Netherlands Lutsharel Geertruida da ke taka leda a matsayin ɗan wasan Aro a Sunderland daga RB Liepzig, na son ganin ya ci gaba da taka leda a gasar Firimiya a kakar wasa mai zuwa, dai-dai lokacin da Everton ke son ɗaukar sa. (Football Insider)

Real Madrid da Antonio Rudireger za su sanya hannu kan tsawaita kwantaragin ɗan wasan da shekara guda, sai dai Madird na nan kan bakanta na ɗauko mai tsaron bayan Manchester City Josko Gvardiol. (AS - in Spanish)

Mai tsaron ragar Ingila Tom Heaton, na shirin tsawaita kwantaraginsa na ci gaba da zama a Manchester United a tsawon kakar wasanni shida. (Mirror)

Liverpool na harin ɗauko ɗan wasan Inter Milan da Nethrlands Denzel Dumfries don ɗinkin bayan ƙungiyar ta gefe. (Football Insider)