Jerin ƴan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 9

Tsohon ɗan takarar gwamna a jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Gbadebo Rhodes-Vivour da kuma tsohon babban lauyan tarayya Abubakar Malami, na cikin jerin ƴan takarar gwamna da jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta fitar.

Jam'iyyar adawar ta Najeriya ta wallafa sunayen mutanen da za su yi takarar gwamna da mataimakansu a babban zaɓen shekarar 2027 a jihohi 28.

Ɗaya daga cikin shahararrun sunayen da ke cikin jerin shi ne Great Ogboru na Jihar Delta, wanda ya daɗe yana neman zama gwamna tun shekarar 2000. Ya taɓa fafatawa da tsohon gwamnan Jihar Delta, James Ibori.

Tun shekarar 2000, Ogboru ya riƙa sauya sheƙa daga wannan jam'iyyar zuwa waccan, amma bai taɓa samun nasara ba.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu a shafinsu na intanet, jam'iyyar ta bayyana cewa ta fitar da jerin sunayen ne "domin bai wa ƴan Najeriya jagoranci na gari da kuma ingantaccen zaɓin da ya bambanta da wanda ake da shi a baya."

Jam'iyyar African Democratic Congress na fuskantar matsalolin cikin gida sakamakon rikice-rikicen da ke faruwa a wasu jihohi inda jam'iyyar ta rarrabu.

Duk da ƙoƙarin da ake yi na warware matsalar, lamarin ya ja lokaci har sai da ɓangarorin biyu suka kai batun gaban kotu, kuma har yanzu kotu na ci gaba da sauraron ƙarar.

Cikakken jerin sunayen ƴan takara

Kalu Kalu Agu - Abia

Kalu Kelechi lauya ne kuma ɗan siyasar Najeriya. Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Jihar Abia a zaɓen shekarar 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), amma bai yi nasara ba.

Alozie Ogadinma Darlington ne zai yi takara a matsayin mataimakin gwamna.

Modibbo Hamman Tukur Ribadu - Adamawa

Modibbo Hamman Tukur Ribadu ya yi aiki a matsayin darakta a sashin leƙen asiri na binciken kuɗi na Najeriya (NFIU) a shekarar 2019. Ya sami digiri na biyu (MSc) a fannin kasuwanci na ƙasashen duniya sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin darakta a hukumar NFIU kafin naɗin.

Yana cikin rukunin ma'aikata na farko da suka fara aiki a NFIU, a ƙarƙashin EFCC. Ya shiga hukumar a watan Maris na 2005 a matsayin Mai nazarin bayanan Kuɗi/Musayar Kuɗi kuma Mai duba harkar bin dokokin Banki.

Aguwa Kevin Iliya ne zai yi masa takarar mataimakin gwamna.

Akpanudoedehe John James - Akwa Ibom

Akpanudoedehe John James ya yi Sanata mai wakiltar Yankin Akwa Ibom ta Arewa-maso-Gabas a shekarar 1999.

James ya yi aiki a matsayin manajan tallace-tallace na kamfanin Dajucom a shekarun 1980, kafin ya kafa nasa kamfanin mai suna John Silver Group.

Nsien Mkpombik Tommy ne zai yi masa takarar Mataimakin Gwamna.

Haliru Dauda Jika - Bauchi

An haifi Halliru Dauda Jika a shekarar 1976 a Jihar Bauchi, Najeriya. Jika ɗan kasuwa ne kuma dan /'siyasa.

Ya taba rike mukamin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi tare da wakiltar yankin Bauchi ta Tsakiya.

Jika ya halarci Kwalejin Sardauna Memorial da ke birnin Kaduna, a shekarar 1999. Daga baya ya koma kwalejin Fasaha ta Kaduna (Kaduna Polytechnic) domin karantar aikin injiniyan gine-gine (Civil Engineering), inda ya kammala karatunsa a shekarar 2003.

Sama'ila Mohammed Kabir zai yi masa Mataimakin Gwamna

Herman Iorwase Hembe - Benue

Herman Iorwase Hembe ɗan siyasa ne kuma lauya ɗan asalin yankin ƙaramar hukumar Konshisha a jihar Benue, yankin Arewa ta tsakiyar Najeriya.

An haife shi a ranar 22 ga watan Yuni, 1975.

Hembe ya shiga harkar siyasa ne yayin da yake karatu a Jami'ar Jihar Benue. An fara zaɓen sa a matsayin ɗan Majalisar Wakilai na tarayya a shekarar 2011 don wakiltar mazaɓar Vandeikya/Konshisha ta jihar Benue.

A lokacin da yake riƙe da muƙamin ɗan majalisa, ya yi aiki a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisa mai kula da babban birnin tarayya (FCT), sannan daga baya ya zama Shugaban kwamitin majalisa mai kula da harkokin saye da sayarwa na gwamnati (Public Procurement).

A shekarar 2022, ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Benue a ƙarƙashin jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023.

Abba John Abba ne zai yi masa takarar Mataimakin Gwamna.

Babagana Buhari - Borno

Mamman Dauda shi ne ɗan takarar maitaimaki.

Nkoyo Toyo - Cross River

Nkoyo Toyo lauya ce, mai fafutukar ci gaban al'umma, kuma ƴar siyasa wadda ta yi aiki a fannin hidimar jama'a, bayar da shawarwari da kare haƙƙin jama'a, da kuma tsara manufofi.

Ta samu digiri daga Jami'ar Ahmadu Bello da Jami'ar Legas da Jami'ar Sussex, da kuma Harvard Kennedy School.

Toyo ta yi aiki a matsayin jakadiyar Najeriya a ƙasashen Habasha da Djibouti, inda ta wakilci ƙasar a Tarayyar Afirka (AU), da Kwamitin zaman lafiya da tsaro, da Hukumar kula da tattalin arziki ta Afirka.

Ta kuma yi aiki a matsayin ƴar majalisar wakilai, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen kula da harkokin waje, sauye-sauyen da suka shafi batun jinsi, da kuma ƙoƙarin samar da zaman lafiya.

Kafin ta shiga harkar siyasa, ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar 'Gender and Development Action' (GADA) a shekarar 1994, ƙungiyar da ke inganta damar mata ta fuskar tattalin arziki da siyasa a Najeriya.

Okwoche Andrew Adagbor zai yi ma ta takarar mataimakin Gwamna.

Great Ogboru - Rivers

Chief Great Ovedje Ogboru shi ne na huɗu a cikin yara 16. An haife shi a ranar 10 ga Afrilu, 1958, a Port Harcourt, cikin iyalin Ogboru na Abraka. Shi ɗan ƙabilar Urhobo ne.

A shekarar 1980, Great Ogboru ya tafi Legas don neman arziki. Yana da shekaru 25, ya kafa kamfaninsa mai suna Fiogret Ltd, wanda ke harkar kasuwancin kifi.

Kamfanin ya shiga harkokin kasuwanci daban-daban kamar ƙera kayan ɗaki, da jigilar kaya ta ruwa, da kuma harkar canjin kuɗaɗe ƙasashen waje (bureau de change).

A shekarar 1990, an zarge shi da hannu wajen shirin juyin mulki a kan Janar Ibrahim Babangida. Wannan zargi ya sa Ogboru ya tafi gudun hijira a Birtaniya daga 1990 zuwa 2000. Daga baya ya koma Angola da Namibia. Sai dai a shekarar 1999, gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar ta wanke shi daga zargin.

Yayin da yake gudun hijira a Birtaniya, ya halarci kwasa-kwasai a Chartered Institute of Marketing da ke Landan. Ya kuma halarci Jami'ar Huron ta South Dakota (reshen Landan) don samun digirin MBA, sannan ya samu digirin digirgir (Masters) a fannin dangantakar ƙasa da ƙasa daga Jami'ar Kent da ke Canterbury.

Ya yi imanin cewa Jihar Delta tana cikin mawuyacin hali kuma dole ne a samu sauyi. Wannan ya sa ya fara neman takarar Gwamna tun shekarar 2003 a ƙarƙashin jam'iyyu daban-daban. Ya yi takarar Gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar Alliance for Democracy a 2003, da Democratic Peoples Party a 2007 da 2011, da Labour Party a 2015, da kuma All Progressives Congress a 2023.

A yanzu, Great Ogboru shi ne ɗan takarar Gwamna na jam'iyyar African Democratic Congress a Jihar Delta a babban zaɓen shekarar 2027.

Afiari Gloria za ta yi masa takarar mataimakiyar gwamna

Ukpai Mbah Ude - Ebonyi

Onwe Daniel Ede

Ochi Oboozeze Chukwuma - Enugu

Eze Anrze Christopher

Bala Bello - Gombe

Bala Sani Sisa

Sabo Mohammed Nakudu - Jigawa

An haifi Sabo Mohammed Nakudu a ranar 11 ga Satumba 1968 a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, Najeriya.

Nakudu ya zama ɗan majalisar wakilai daga 2007 zuwa 2015. Ya yi wa'adi biyu yana wakiltar mazaɓar Birnin Kudu.

A shekarar 2015, ya tsaya takarar Sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma a ƙarƙashin jam'iyyar All Progressives Congress kuma ya yi nasara.

A watan Oktoban 2022, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa Nakudu lambar yabo ta ƙasa 'Commander of the Order of the Niger.'

Yanzu, ta tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin ADC.

Musa Ya'u Balarabe - zai yi masa takarar mataimaki.

Isa Mohammed Ashiru - Kaduna

Isa Mohammed Ashiru ɗan siyasar Najeriya ne, kuma ya bayyana kansa a matsayin shugaba mai mayar da hankali kan ci gaba, wanda ya fito daga Kudan a Jihar Kaduna.

Dangane da bayanan da ke shafinsa na intanet, yana da gogewar aikin gwamnati na sama da shekaru 17 tare da gogewa sosai a fannin jagoranci a majalisa.

Ashiru ya yi aiki a matsayin ɗan Majalisar Wakilan Tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Shi ne wanda ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2019.

Ashiru shi ne ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC a zaɓen shekarar 2027.

Kantiok Rmiya Ishaku - Mataimakin Gwamna

Ibrahim Ali Amin - Kano

Shehu Abdulkadri Bari - Mataimaki

Ahmad Babba-Kaita - Katsina

Ahmad Baba Kaita tsohon ɗan majalisar wakilai ne wanda ya wakilci mazaɓar Kankia/Ingawa/Kusada daga shekarar 2011 zuwa 2018.

An fara zaɓensa a matsayin sanata a shekarar 2018 a ƙarƙashin jam'iyyar APC bayan an gudanar da zaɓen cike gurbi. Ya sake tsayawa takara a shekarar 2019 kuma ya yi nasara.

An haifi Babba-Kaita a ranar 8 ga watan Satumbar 1968.

Aminu Yar'Adua Ahmed ne xai yi masa takarar mataimakin gwamna.

Abubakar Malami - Kebbi

Abubakar Malami (SAN) fitaccen ɗan siyasa ne kuma lauya a Najeriya. An haife shi a ranar 10 ga Afrilu, 1967, a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi. Mahaifinsa sanannen alƙali ne a kotun ɗaukaka ƙara ta Shari'a, wanda ya jagoranci shari'o'i masu muhimmanci da dama dangane da dokokin Musulunci.

Tsohon babban lauyan tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, ya fito a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Kebbi.

Malami, mai shekaru 58, yana ɗaya daga cikin mutane masu tasiri sosai a gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

A halin yanzu, ana tuhumar tsohon babban jami'in shari'ar da laifuka a gaban babbar Kotun tarayya da ke Abuja, sakamakon ƙarar da hukumar yaƙi masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ta shigar a kansa.

Ana tuhumarsa da laifuka 16 da suka shafi hakasta kuɗin haram da kuma cin zarafin muƙami, waɗanda jimillar kudinsu ya kai Naira biliyan 8.7 (dalar Amurka miliyan 6; fam miliyan 4.5).

Lauyan, wanda ya auri ƴar Shugaba Buhari ta uku, Nana Hadiza, ya fice daga jam'iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) domin komawa jam'iyyar adawa ta African Democratic Congress, wadda ake kallon a matsayin babbar abokiyar hamayyar APC a babban zaɓen shekarar 2027.

Zakari Mohammed - Kwara

Zakari Mohammed ɗan siyasa ne, mai gudanarwa, kuma ƙwararre a fannin yaɗa labarai a Najeriya.

An haife shi a ranar 7 ga watan Yuli na shekarar 1973 a yankin ƙaramar hukumar Baruten ta jihar Kwara.

Mohammed ya wakilci mazaɓar tarayya ta Baruten/Kaiama a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga shekarar 2011 zuwa 2019. A lokacin Majalisar dokoki ta tarayya ta 7, ya riƙe muƙamin Shugaban kwamitin majalisa kan Yaɗa Labarai da Harkokin Jama'a.

A lokacin Majalisar dokoki ta tarayya ta 8, ya jagoranci kwamitin majalisa kan Ilimin matakin Farko da ayyukan da suka shafe shi, tare da kwamitin Majalisa kan Yarjejeniyar musayar man Fetur (Oil Swap Contracts).

Olawuyi Julius Olayide zai yi masa takarar mataimakin Gwamna.

Gbadebo Rhodes-Vivour - Lagos state

Gbadebo Rhodes-Vivour, mai shekaru 42, masanin taswirar gine-gine (architect) ne, kuma ƙwararre kan manufofin gwamnati, kuma ɗan siyasa.

An haife shi a ranar 8 ga Maris, 1983, a cikin iyalin Rhodes-Vivour na Legas. A cewarsa, yana alfahari da kasancewarsa dan asalin Legas, kasancewar tushensa da asalinsa sun samo asali ne daga jihar Legas.

Gbadebo ya fito ne daga iyalin da suka shahara a fannin shari'a. Mahaifinsa, Mai Shari'a Olawale Rhodes-Vivour, tsohon alƙali ne a Kotun ƙolin Najeriya. Marigayi Mai Shari'a Akinwunmi Rhodes-Vivour kakansa ne, kuma shi jikan Mai Shari'a Steven Bankole Rhodes ne—mutum na biyu a tarihin Najeriya da aka naɗa a matsayin alƙali ɗan ƙasa (ba bature ba).

Saboda sha'awarsa ta siyasa da ayyukan fafutuka, ya yi karatun digirinsa na biyu (Masters) a fannin bincike da manufofin gwamnati a Jami'ar Legas (UNILAG).

A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da BBC Pidgin a shekarar 2023, Gbadebo ya bayyana cewa a matsayinsa na gwanin tsara gine-gine, zai "tsara yadda Legas za ta kasance domin ta amfani kowa da kowa."

Gbadamosi Babatunde Olalere zai yi masa takarar Mataimaki

Nuhu Angbazo - Nasarawa

Ahmed Yusuf

DR. Mohammed Kpautagi - Niger

Musa Mamman

Biodun Collins Ogundipe - Ogun

Muraina Oluwaranti Oluyemi

Taofeek Adegboyega Adegoke - Oyo

Wahab Adeniyi

Brig.Gen John Sunday Sura - Plateau

Pwajok-Kele Chundung Bitrus

Gabriel Pidomson - Rivers

Okumgba David Amapakaye

Manir Mohammad MOHAMMAD Daniya - Rivers

Isah Bello Ambarura

Abubakar Umar Tutare - Taraba

Kwetishe Haruna Kwenyan

Kassim G. Gaidam - Yobe

Kori Lawan Mohammed

Shinkafi Bilyaminun Yusuf - Zamfara

Muhammad Abdulmuddalib Auwal

Me ya sa jam'iyyar ke da ƴan takara a jihohi 28?

Jam'iyyar African Democratic Congress ta fitar da sunayen ƴan takarar gwamna da mataimakansu ne saboda a cewarta su ne waɗanda za su tsaya takara a zaɓen 2027.

Sauran Jihohi na gudanar da nasu zaɓukan daban da lokacin da aka saba.

A ranar 15 ga watan Augusta ne dai aka gudanar da zaɓen a jihar Osun, inda Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord ya lashe zaɓen da kuma ɗan takarar ADC shi ne Najeem Salaam.

Bayelsa da Anambra da Imo da Ondo da Edo da Ekiti da Kogi su ne sauran jihohin da ke gudanar da zaɓukansu ba a lokacin da aka saba ba.