Fiorentina ta kori kociyanta Fabio Grosso kasa da wata yana kan aikin, Fabio Grosso
Fiorentina ta kori kocinta, Fabio Grosso a ranar Lahadi, bayan da ya yi rashin nasara uku a jere a farkon kakar wasa ta bana, hakan ya sa ƙungiyar tana ƙarshen teburin Serie A.
Fiorentina ta sha kashi da ci 4-0 a hannun AS Roma a karshen mako, sannan ta yi rashin nasara da ci 3-0 a gida a hannun Frosinone, wadda a bana ta hau Serie A, kafin rashin nasarar da ta yi a gida da ci 2-1 a hannun Torino ranar Asabar.
Hakan ya sa Fiorentina ta zura ƙwallo ɗaya kacal, yayin da aka zura mata ƙwallaye tara. Za ta ziyarci Venezia ranar Juma'a.
Tsohon ɗan wasan tawagar Italiya mai shekaru 48 ya shafe ƙasa da wata uku a matsayin kocin Fiorentina, bayan da ya maye gurbin Paolo Vanoli a ranar 8 ga Yuni kuma ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyu.
Vanoli ya jagoranci Fiorentina zuwa matsayi na 15 a kakar wasan da ta gabata, bayan da ya karɓi ragamar ƙungiyar daga Stefano Pioli, wanda aka kora bayan fara kakar wasa da rashin nasara a wasa 10 a jere.
A baya Grosso ya taɓa horar da Bari, Hellas Verona, Brescia, Sion, Frosinone da Olympique Lyonnais.