Kane yana alfahari da yake cikin ƴan takarar Ballon d'Or a bana, Ballon d'Or

Asalin hoton, Getty Images
Harry Kane ya ce yana alfahari da yake cikin ƴan takarar kyautar Ballon d’Or, yana mai cewa yana “matukar farin ciki” da gagarumar gudunmuwar da yake bayarwa da zura ƙwallaye da dama a kakar wasan da ta gabata.
Ɗan wasan mai shekaru 33 shi ne wanda ake gani yana kan gaba tsakanin ƴan takara wajen lashe kyautar da za a gudanar a watan Oktoba, bayan da ya zura ƙwallo 73 a wasannin da ya buga wa Bayern Munich da Ingila a kakar da ta gabata.
Wannan adadi bai kai wanda Lionel Messi ya samu ba a 2011/12, wanda ya zura ƙwallo 82 a raga.
Idan Kane ya lashe kyautar, zai zama ɗan Ingila na biyar da ya taɓa yin hakan, bayan Sir Stanley Matthews, Sir Bobby Charlton, Kevin Keegan da Michael Owen. Haka kuma zai zama ɗan Ingila na farko da ya lashe kyautar tun bayan da Owen ya yi hakan a shekarar 2001.
A kakar dbara da Kane ya zura ƙwallaye 73 a raga ta sa ya karya tarihin Cristiano Ronaldo mai 69 a raga a kakar a shekarar 2011-12.


