Yadda mata za su kauce wa ciwon kai na ɓari ɗaya

    • Marubuci, Sarah Bell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Kwanciya a ɗaki mai duhu yayin da azabar ciwo ke ci gaba da dukan goshi abu ne da ya zama ruwan dare ga masu fama da migraine da dama.

Wannan cuta mai raunana jiki na iya yin babban tasiri ga zamantakewar mutum, aikinsa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwarsa.

Har ila yau, ta fi shafar mata, inda bincike ya nuna cewa mata sun fi kamuwa da cutar migraine fiye da maza har sau ninki uku.

Sai dai me ke haddasa ciwon kan na bari ɗaya, kuma wane mataki ne za a iya ɗauka domin taimakawa wajen rage tasirinsa?

Alamomin ciwon kai na ɓari ɗaya (migraine)

Cutar migraine na shafar kusan mutum ɗaya cikin mutane bakwai a faɗin duniya, wato fiye da mutum biliyan ɗaya, a cewar ƙungiyar Migraine Trust ta Birtaniya.

Migraine wata cuta ce ta jijiyoyin ƙwaƙwalwa mai alaƙa da gado, wadda ke sa ƙwaƙwalwa ta fi saurin mayar da martani ga sauye-sauye da ke faruwa.

Dokta Katy Munro, ƙwararriya ce kan migraine a Cibiyar National Migraine Centre ta Birtaniya, ta ce wasu mutanen da ke ɗauke da ƙwayoyin halittar masu nasaba da cutar ba sa ganin alamunta ko kaɗan, kuma sukan rayu ba tare da wata matsala ba.

Sai dai a wasu mutane, wasu abubuwa daga muhalli ko yanayin rayuwa kan tayar da wasu hanyoyin aiki na musamman a cikin ƙwaƙwalwa.

Hakan kuma kan jawo sakin wasu sinadarai na jijiyoyin ƙwaƙwalwa da ke haddasa alamomin migraine.

Alamomin na iya haɗawa da ciwon kai, amma kuma har da amai da jiri da kuma rikicewar tunani ko rashin mayar da hankali.

Dokta Munro, wadda ke gabatar da shirin podcast mai suna Heads Up kan migraine, ta ce wani lokaci mutum kan fuskanci wasu alamomin ciwon migraine ɗaya, amma idan ya sake kamuwa daga baya sai alamomin su ɗan bambanta.

''Haka kuma alamomin na iya bambanta tsakanin ƴan'uwa, kuma tabbas suna iya canzawa yayin da mutum ke tafiyar da rayuwarsa."

Me ke haifar da ciwon migraine?

Ba kasafai abu guda ɗaya kaɗai ke haddasa ciwon migraine ba.

Sau da yawa ƙananan abubuwa ne daban-daban ke taruwa har su kai mutum matakin da zai jawo masa ciwon.

Waɗannan abubuwa na iya haɗawa da sauye-sauyen sinadaran hormones a jiki da rashin daidaiton yawan sukari a jini da kuma rashin isasshen barci ko yin dogon lokaci ba tare da barci mai kyau ba.

Damuwa na taka muhimmiyar rawa wajen haddasa migraine.

Sai dai kuma wani lokaci ciwon na iya faruwa ne bayan mutum ya samu natsuwa bayan wani lokaci na tsananin damuwa.

Dokta Munro ta ce hakan na yawan faruwa musamman ga mata. Ta ce: "Sau da yawa mu ne ke ɗaukar nauyin tafiyar da al'amura da dama a lokaci guda, muna kula da jadawalin iyali da kuma tabbatar da cewa komai yana tafiya yadda ya kamata."

Sauye-sauyen yanayi kamar canjin zafi, matsin iska da kuma yawan danshi a sararin samaniya na iya haddasa ciwon migraine.

Hakan na iya faruwa ne saboda yadda jiki ke amsa waɗannan sauye-sauyen kai tsaye, ko kuma saboda wasu illolinsu kamar rashin ruwa a jiki.

Haka kuma wasu matsalolin lafiya kamar ƙarancin sinadarin baƙin ƙarfe a jiki (iron), cutar celiac, ko kuma rashin aiki yadda ya kamata na gland ɗin thyroid na iya haifar da ko kuma tsananta ciwon migraine.

Wane tasiri sinadaran hormones ke yi?

Aƙalla kashi 10 cikin 100 na yara na fama da migraine, kuma cutar na shafar yara maza da mata daidai gwargwado.

Sai dai wannan yanayin kan canza da zarar yara mata sun fara al'ada yayin balaga.

Dokta Munro, wadda tsohuwar likitar iyali (GP) ce, ta ce wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ke sa mafi yawan ciwon migraine ya fi ƙaruwa a tsakanin mata fiye da maza.

''Kuma muna ganin hakan yana ci gaba a tsawon rayuwa har zuwa lokacin da mace ta daina al'ada."

Sauye-sauyen sinadaran hormones na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa migraine.

Musamman, raguwar sinadarin oestrogen sosai kafin fara al'ada na sa hare-haren migraine su fi tsanani a wannan lokaci.

Haka kuma saurin sauye-sauyen hormones a lokacin perimenopause wato matakin da mace ke shiga kafin ta daina al'ada gaba ɗaya, na iya sa migraine ya ƙara tsananta.

Dokta Munro ta ce: "A wannan lokaci hormones kan rikice sosai. Migraine a lokacin perimenopause babbar matsala ce ga mata da dama."

Sai dai ta ce batun ba hormones kaɗai ba ne. "Wataƙila kina ƙoƙarin kula da yara matasa da kuma iyaye tsofaffi a lokaci guda, ko kuma alamomin shiga lokacin daina al'ada suna hana ki samun isasshen barci," in ji ta.

Bayan mace ta daina al'ada gaba ɗaya, ciwon migraine kan ragu, kuma ba sa yawan faruwa kamar da, saboda matakan hormones a jiki sun fi samun daidaito.

Ta yaya zaka gane ka kamu da ciwon migraine?

Cutar migraine kan bi matakai huɗu. Na farko shi ne matakin gargaɗi ko prodromal phase, lokacin da sauye-sauye ke faruwa a cikin ƙwaƙwalwa.

A wannan lokaci, wasu mutane kan fara nuna alamun gargaɗi kamar yawan hamma da matsananciyar gajiya ko ciwon wuya.

Mataki na biyu shi ne aura, wanda kan ɗauki kusan awa ɗaya. A mafi yawan lokuta, mutum kan fuskanci matsalolin gani kamar layuka masu karkace-karkace ko kuma ganin farin ɗigo-ɗigo.

Kimanin mutum ɗaya cikin uku masu fama da migraine ne ke fuskantar wannan yanayi.

Daga nan sai matakin ciwon kai, wanda shi ne lokacin da alamomin suka fi tsanani.

Wannan mataki kan ɗauki tsakanin sa'o'i huɗu zuwa 72. Wasu mutane kuma kan fuskanci tashin zuciya da amai a wannan lokaci.

Mataki na ƙarshe shi ne wanda ake kira postdromal ko kuma matakin da ke biyo bayan ciwon, wanda kan ɗauki kwana ɗaya ko biyu bayan ciwon kai ya lafa sosai.

Dokta Katy Munro ta ce mutum kan ji tamkar wani babban abin niƙa ya murƙushe shi.

''Kana ƙoƙarin dawo da ƙarfinka sannu a hankali, kuma a irin wannan lokacin ne mutane da dama kan koma bakin aiki, amma har yanzu ba su dawo cikakkiyar ƙoshin lafiya ba."

Waɗanne ɗabi'u ne taimaka wa ciwon migraine?

A baya, an saba bai wa masu fama da migraine shawarar su guji abubuwan da ake zargin suna tayar da ciwon kamar caffeine ko cakulan.

Sai dai Dokta Munro ta ce ya fi dacewa a mayar da hankali kan daidaita tsarin rayuwa da ayyukan yau da kullum gwargwadon iko.

Ta ce yana da amfani mutum ya kasance kamar mai binciken migraine, ta hanyar yin tunani kan abubuwan da suka canza a kwanaki biyu ko uku kafin ciwon ya bayyana.

Hakan na iya taimaka masa gano abubuwan da ke haddasa ciwon domin ya yi ƙoƙarin kauce musu a gaba.

Sai dai kuma, a cewarta, rayuwa ba ta tafiya daidai koyaushe. "Ba za mu iya zama cikakku a kowane lokaci ba. Don haka kada ku ɗora wa kanku laifin abin da ya faru. Ku yi iyakar ƙoƙarinku," in ji ta.

Cin abinci a kai a kai da kuma guje wa faɗuwar yawan sukari a jini na da muhimmanci.

Haka kuma samun isasshen barci, tare da ƙoƙarin kwanciya da tashi a lokaci guda a mafi yawan kwanaki, na taimakawa wajen rage yiwuwar harin migraine.

Ko da yake motsa jiki yana da muhimmanci ga kowa, yana iya tayar da migraine ga wasu mutane.

Don haka masu fama da ciwon ya kamata su tabbatar suna samun isasshen abinci da ruwa musamman lokacin motsa jiki.

Dokta Munro ta ce wannan fahimta na iya bayyana dalilin da ya sa ƙarshen mako ke zama lokaci mai haɗari ga wasu masu fama da migraine, domin akwai yiwuwar suna yin abubuwa daban da yadda suka saba yi a ranar Juma'a.

"Wataƙila kuna gaggawar kammala ayyukan mako. Ko kuma da yamma kuna hutawa ta hanyar shan giya kaɗan wadda ba ku saba sha a sauran kwanakin mako ba. Haka kuma watakila kuna kwanciya barci a makare fiye da yadda kuka saba," in ji ta.

Ta ƙara da cewa abin da ya kamata mutum ya yi shi ne ya duba abubuwan da suka canza a tsarin rayuwarsa, sannan ya yi ƙoƙarin sa su kasance masu daidaito gwargwadon iko.

Wanne magani ne zai taimaka?

Samun magani cikin gaggawa da zarar alamun harin migraine sun fara bayyana na da matuƙar muhimmanci.

Dokta Munro ta ce sau da yawa mutane kan jira na ɗan lokaci domin ganin ko harin ciwon zai tsananta kafin su ɗauki matakin magani.

"A lokacin da mutum ya jira har ciwon ya yi ƙarfi, kamar ƙwallon dusar ƙanƙara ce da ke ci gaba da ƙaruwa. Idan ya kai wannan mataki, duk abin da za ka yi na iya kasa yin tasiri sosai. Amma idan an sha magani da wuri, zai taimaka wajen daƙile ciwon tun kafin ya tsananta."

Dokta Munro ta ce ana iya amfani da magungunan rage tashin zuciya da amai tare da magungunan rage zafi kamar ibuprofen ko aspirin.

Ta ce paracetamol ba ya yin tasiri sosai wajen magance migraine, sannan ta yi gargaɗin guje wa amfani da codeine, saboda yana iya sa ciwon kai ya ƙara muni.

Haka kuma akwai wasu magunguna na musamman da aka tanada domin migraine, waɗanda ake kira triptans, kuma likitoci na iya rubuta su ga marasa lafiya.

Ta ce akwai wasu shaidu da ke nuna cewa sinadarai masu gina jiki kamar magnesium da Vitamin B2 na iya taimakawa wajen rage yawan hare-haren migraine.

Matan da ke fama da migraine a lokacin al'ada kan ga cewa ƙwayoyin hana ɗaukar ciki na iya taimaka musu wajen daidaita sauye-sauyen hormones.

Haka kuma maganin maye gurbin hormones (HRT) na iya taimakawa a lokacin perimenopause, wato matakin da mace ke shiga kafin ta daina al'ada gaba ɗaya.

Masana kimiyya sun gano wasu sinadarai a cikin jijiyoyi da ke taka muhimmiyar rawa wajen haddasa migraine.

Ɗaya daga cikinsu shi ne wani sinadari da ake kira CGRP, wanda ke da tasiri ga wasu masu fama da ciwon.

A yanzu akwai magungunan da aka ƙirƙira domin hana wannan sinadarin yin tasiri.

Sauran hanyoyin magani sun haɗa da botox, wanda masana ke ganin na iya hana sakin wasu sinadarai masu haddasa jin zafi.

Haka kuma wasu hanyoyin magani na gaba ɗaya kamar allurar acupuncture, Yoga, Tai Chi, da kuma hanyoyin koyar da mutum yadda zai sarrafa yadda ƙwaƙwalwarsa ke fahimtar ciwo (pain reprocessing therapy) na iya taimakawa.

Dokta Munro ta ce abu mafi muhimmanci shi ne mutane su nemi ƙarin bayani da ilimi game da migraine da hanyoyin magance shi.

"Akwai dalilai masu yawa na fatan samun sauƙi, don haka kada ku karaya ko ku yi tunanin kun gwada komai. A zahiri, akwai wasu hanyoyi da dama da za a iya gwadawa."