Masarautun arewacin Najeriya 14 da Ɗanfodiyo ya bai wa tuta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Fiye da shekaru 200 da suka gabata, Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo ya jagoranci wani gagarumin sauyi a Arewacin Najeriya wanda ya haifar da kafuwar Daular Sakkwato ko Daular Usmaniyya.

Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo na daga cikin manyan jagororin addini da siyasa da suka yi tasiri a tarihin Arewacin Najeriya

Bayan jihadin da ya jagoranta a farkon ƙarni na 19, ya bai wa wasu almajiransa tuta domin su je su yi jihadi a garuruwansu har su kafa mulki.

Har zuwa yau, waɗannan tutoci na ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na tarihin masarautun.

Dalilin ba su tutar

Ibrahim Ado Kurawa, Editan ''Najerian Year Book Who and Who'' masanin tarihi, marubuci kuma mai bincike a Najeriya, ya ce dalilin ba su tutar shi ne a lokacin da koyarwar Sheikh Fodiyo ta fara samun karɓuwa da nisa a masarautar Gobir.

Sarkin Gobir na wancan lokacin ya ɗauki hakan a matsayin barazana gare shi da kuma mulkinsa.

''Don haka ne ya kori Shehu daga ƙasarsa, ya kuma rubuta wasiƙu zuwa ga sauran sarakuna , yana faɗa musu cewa su yi hankali da wa'azin Shehu da almajiransa'', in ji shi.

A cewar masanin tarihin daga nan ne Shehu ya yi ƙaura daga Ɗagel zuwa Gudu a da ke jihar Sokoto ta yanzu.

"A Gudu ne ya tara mayaƙa ya yi jihadi ya kifar da mulkin ƙasar Gobir, sannan ya kafa Daula a Sokoto tare da naɗa ɗansa Muhammad Bello a matsayin sarki'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Kurawa ya ya ce a Gudu ne almajiran Shehu daga ko'ina suka riƙa zuwa wurinsa suna yi masa mubaya'a tare da ba su tuto domin su je garuruwansu su yi wa'azi ga sarakunsu har su amince da koyarwar Musulunci, in kuwa suka yi sai su yaƙe su domin kafa sarauta.

A wannan muƙala mun yi waiwaye kan sarakunan da Ɗanfodiyo ya bai wa tuta da kuma muhimmancin hakan a tarihi.

Kano

Masarautar Kano ta kasance ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙasar Hausa da suka karbo tuta bayan jihadin Shehu.

A cewar Kurawa bayan jihadin wasu malamai daga ƙadsar Kano sun je wurin Shehu suka kuma karɓo tuta.

''Sai a lokacin da suka je Shehu ya tambaye su wane ne limaminku a ƙasar Kano, sai suka ambaci sunan Sulaimanu, wanda da suka dawo suka yi masa mubaya'a har ya zama sarkin Kanu ya kafa masarauta'', in ji shi.

Masarautar Kano na daga cikin manyan masarautu masu daɗaɗɗen tarihi a ƙasar Hausa.

Katsina

A shekarar 1806 ne sarakunan Fulani suka karɓe sarautar Katsina daga hannun sarakunan Haɓe.

Inda Sarki Umaru Dallaji ya zama sarki na farko a Katsina bayan mubaya'a ga Daular Sokoto.

Masarautar ta kasance ɗaya daga cikin masarautu masu ƙarfin faɗa a ji a ƙasar Hausa, har lokacin zuwan Turawan mulkin mallaka.

Zazzau

Masarautar Zazzau, wadda a yanzu ke jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin manyan masarautu masu tarihi a arewacin ƙasar.

Ado Kurawa ya ce bayan da almajiran Shehu uku, ƙarƙashin jagorancin Musa Bamalli suka karbo tuta daga Daular Sokoto, da suka koma Zazzau sun riƙa, har sarkin Zazzau na lokacin Ishaq ya yarda da su ya kuma bi su.

''Sai bayan mutuwar Sarki Ishaq ne da aka naɗa wani, sai ya bijire wa koyarwar masu jihadin, lamarin da ya sa suka yaƙe shi, tare da naɗa Musa Bamalli, wanda kuma bayan ya ƙare mulki ba a naɗa ɗansa ba aka naɗa sauran mutanen da suke karɓo mtutar tare''.

Masanin tarihin ya ce wannan shi ne dalilin da ya sa sarautar zazzau take da asali daga gidaje uku.

Daura

Masarautar Daura, wadda ita ke cikin jihar Katsina ta yanzu, na daga cikin masarautun da Shehu ya bai wa tuta.

Masanin tarihin ya ce bayan jihadin almajiran Shehu, ƙarƙashin jagorancin Malam Ishaku suka yaƙi sarakunan Haɓe tare da kafa sabuwar masarauta.

Masarautar Daura na daga cikin masarautu na tarihi a arewacin Najeriya.

Misau

Tarihi ya nuna cewa na kafa masarautar Misau ta kafu a shekarar 1831 bayan jihadin Shehu.

Sai dai bayanan tarirhi sun nuna cewa Gwani Muktar daga Daular Borno ne ya fara assasa masarautar.

Bayan mutuwarsa a wani yaƙi, ɗansa Muhammadu Manga na farko ya karɓo tuta daga Sokoto.

Katagum

Bayan jihadin Shehu Usman Ɗanfodio, Ibrahim Zakiyul Kalbi (Malam Zaki) ya kafa masarautar Katagum, wadda a lokacin take ƙarƙashin Borno.

Katagum, wadda a yanzu haka ke cikin jihar Bauchi, ta kasance cikin masaurautu masu ƙarfi a jihar.

Bauchi

Bayan Jihadin Shehu, masarautar Bauchi ta faɗa hannun Mallam Yakubu, wanda ya karɓo tuta daga Sokoto.

A matsayinsa na mai majorantar masarautar, Sarki Yakubu ya yi ƙoƙarin haɗa kan al'ummar masarautar mai mabambantan ƙabilu.

Ya kuma gina katanga domin kare masarautar daga hare-haren maƙiya, wadda kuma ta ci gab a da kasancewa cikin masu ƙarfi a yankin kafin zuwan turawa.

Jama'are

Ita ma masarauta ce da fulani suka jagorance ta bayan jihadin Shehu a farkon ƙarni an 19.

Muhammadu Wabi na farko ne ya fara jagorantar masarautar bayan karɓo tutar a 1835.

Masarautar ta kasance cikin na gaba-gaba a bunƙasa harkokin ilimi a cikin masarautun Daular Usmaniyya.

Gombe

Bayan karɓo tuta daga Sokoto a 1804, Buba Yero ya kafa masarautar Gombe.

Ya faɗaɗa masarautar har zuwa yankin Kogin Gongola, kafin daga baya ta rabe a kafa wata masarautar.

Masarautar na daga cikin mafiya tasiri a yankin.

Adamawa

Bayan karɓo tuta daga Sokoto, Modibo Adama ya kafa masarautar Adamawa a 1809 da aka fi sani da Fombina a lokacin.

Masarautar ta girma inda ta zama ɗaya daga cikin manyan masarautun Daular Sokoto, wadda ta nausa har zuwa cikin ƙasar Kamaru.

Haɗejia

Masarautar Haɗejia da ke jihar Jigawa a yanzu na cikin tsofaffin masarautu masu tarihi a arewacin Najeriya.

Bayan jihadin Shehu masarautar ta kasance ɗaya daga cikin masarautun fulani masu ƙarfi a Daular Usmaniyya.

Sarki Malam Sambo Diginsa ne ya jagoranci karɓo tutar, atre da kafa masarautar a 1808.

Bidda

Masarautar Bida da a baya ke ƙarƙashin Daular Nufe, ta koma ƙarƙashin Daular Usmaniyya a farkon ƙarni 19 bayan jihadin na Shehu.

Musulunci ya yaɗu zuwa ƙasar Nupe bayan jihadi, ta hanyar wani mutum da ake kira Mallam Dendo da yake wa'azi.

Wanda kuma ya kafa masarautar Bida bayan kwashe shekaru.

Ilorin

Bayan jihadin Shehu, masarautar Ilorin ta ɓalle daga Daular Oyo, zuwa masarautar Musulunci mai cin mai biyayya ga Daular Sokoto.

Abd al-Salam (ɗa ga Alimi mai wa'azi) ne ya fara zama sarki bayan kifar da tsohon sarkin masarautar Afonja a 1823–1829.

Kazaure

An kafa masarautar Kazaure a 1819 sakamakon jihadin Shehu Danfodiyo a farkon ƙarni an 19.

Wani fitaccen malami ne mai suna Dan Tunku ya karɓo tutar tare da kafa masarautar wadda ke kusa da masarautun Kano da Katsina da kuma Daura.