Tsawon wane lokaci Amurka za ta iya ɗauka tana yaƙi da Iran?

    • Marubuci, Mehrnoush Pourziaei
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
    • Aiko rahoto daga, Washington
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Yayin da Amurka ke kokarin nuna nasarorin da take ikirarin sojojinta na samu a daya daga cikin mafiya tsauraran ranaku na rikicin Mashigar Hormuz, kafafen yada labarai na Amurka na ci gaba da mayar da hankali kan rikice-rikicen cikin gida a ma'aikatar tsaron kasar, wato Pentagon.

Sabbin bayanai kan murabus din Sakataren Sojojin Kasa na Amurka da kuma matakin da Pentagon ta dauka na takaita damar samun wasu muhimman takardun umarni bayan bayyanar sabanin ra'ayi a cikin ma'aikatar, sun kara jefa Sakataren Tsaro Pete Hegseth cikin matsin lamba.

Mutumin da a baya ake kallonsa a matsayin daya daga cikin amintattun mutanen Shugaba Donald Trump, yanzu yana fuskantar suka ba kawai daga 'yan Democrat ba, har ma daga wasu 'yan jam'iyyar Republican.

A wani rahoto na musamman, jaridar Wall Street Journal ta ce Sakataren Tsaron Amurka na ci gaba da tsawaita aikin sojojin kasar a yankin har zuwa karshen shekara mai zuwa.

Jaridar ta ruwaito majiyoyin da suka san batun na cewa ana yin hakan ne domin a bar wa Shugaba Trump karin zabin matakan da zai iya dauka nan gaba.

Rahoton ya ce duk da cewa Donald Trump ya nuna sha'awar ayyana karshen yakin a hukumance a tattaunawarsa da mashawartansa, ba ya nuna rashin jin dadinsa da ci gaba da halin da ake ciki a yanzu, wanda ya hada da killace hanyoyin ruwa, da ci gaba da takunkumi da kuma hare-hare lokaci-lokaci.

A halin yanzu Pentagon na da sojoji kusan dubu hamsin da jiragen ruwa na yaki goma sha tara a yankin, ciki har da jiragen daukar jiragen sama biyu, domin ci gaba da samar wa shugaban kasar zabin matakan da zai dauka idan bukatar hakan ta taso.

Ma'aikatar Tsaron Amurka ta kuma sanar da iyalan sojojin Runduna ta 82 ta sojojin lema cewa akwai yiwuwar a tsawaita aikinsu har zuwa karshen shekara mai zuwa.

A cewar New York Times, irin wannan mataki na nufin ci gaba da manyan ayyukan tallafi da samar da kayan aiki ga dakarun Amurka na dogon lokaci a yankin.

Kimanin sojoji dubu ashirin daga cikinsu na cikin jiragen ruwa, kuma suna bukatar abinci kusan dubu dari hudu da hamsin da man fetur galan miliyan takwas a kowane mako.

A wani bangare kuma, Washington Post ta ruwaito cewa bayyanar sabanin ra'ayi tsakanin manyan kwamandojin soja da kuma adawarsu da wasu matakan Pete Hegseth ya sa Pentagon ta cire wasu muhimman takardun sirri daga wata kafar sadarwa ta cikin gida.

Majiyoyi uku da ba a bayyana sunayensu ba sun ce an cire takardun da suka shafi umarnin Ofishin Sakataren Tsaro, wadanda ke kunshe da bayanai kan wurare da shirye-shiryen jiragen ruwa, da rundunoni da makaman Amurka.

Wani tsohon jami'in ma'aikatar tsaron ya shaida wa Washington Post cewa cire ko takaita damar samun irin wadannan takardu na iya jinkirta shirye-shiryen gaggawa tare da kara wa kwamandoji wahalar aiwatar da ayyukansu.

Sai kuma mujallar The Atlantic wadda ta mayar da hankali kan murabus din tsohon Sakataren Sojojin Kasa, Dan Driscoll.

Mujallar ta ce Driscoll ya bayyana damuwarsa kan makomar sojojin Amurka karkashin jagorancin Pete Hegseth kai tsaye ga Shugaba Trump a wani taro da suka yi a Fadar White House a makon da ya gabata.

A cewar daya daga cikin majiyoyi hudu da suka san abin da ya faru, Donald Trump ya yi mamakin bayanin da Driscoll ya yi masa game da yawan janar-janar da sauran manyan jami'an da aka kora, ko aka tilasta musu yin murabus, ko kuma aka hana su karin girma bisa umarnin Pete Hegseth.

Rahoton ya ce Driscoll ya gargadi shugaban kasar cewa yawan shugabannin da suka fice daga rundunar na iya hana sojojin Amurka yin sauye-sauyen da suka dace da sake gina kansu yadda ya kamata.

Mujallar The Atlantic ta kara da cewa yawan janar-janar da ke aiki a rundunar sojin Amurka ya kai mafi karancin matsayi a tarihinta, duk da cewa kasar na ci gaba da rike da sojoji fiye da dubu dari hudu da hamsin masu aiki a sassa daban-daban na duniya.

Wane makami aka yi amfani da shi a harin Kohstak?

A wani binciken musamman, jaridar New York Times ta nazarci shaidu da suka danganci harin da Amurka ta kai a wani yankin zama na Kohstak, inda ta ce masana masu zaman kansu kan makamai sun gano alamu da ke nuna cewa an yi amfani da bama-bamai masu linzami wajen kai harin.

Jaridar ta ruwaito Trevor Ball, tsohon kwararre kan lalata abubuwan fashewa a rundunar sojin Amurka, yana cewa fikafikan bama-baman da wasu sassan bayansu da aka gano a wurin harin sun yi daidai da tarkacen bama-baman Joint Stand-Off Weapon (JSOW).

Ya ce irin wadannan makamai sun taba bayyana a hare-haren da Amurka ta kai a wasu wurare a baya.

New York Times ta kuma ce wani bidiyo da babbar rundunar sojin Amurka, wato CENTCOM, ta fitar a lokacin da ta sanar da harinta kan Iran ya nuna wani bam irin na JSOW a makale karkashin fikafikin wani jirgin yakin Amurka.

Wani farfesa a fannin dokokin kasa da kasa a Jami'ar Rutgers, Adil Haque, ya shaida wa jaridar cewa ya kamata a binciki rundunar sojin Amurka kan harin.

A cewarsa, abin da ya bayyana daga bayanan da ake da su shi ne cewa harin "yana da wahalar bayar da hujja ko karewa", domin babu wata alamar cewa akwai wata cibiya ko abin da ya shafi soja a kusa da ginin da aka kai wa hari.

A cewar New York Times, harin da aka kai Kohstak shi ne na hudu da ake zargin Amurka ta kai a lokacin rikicinta da Iran inda hare-hare kan gine-ginen da ba su da wata alaka da soja suka yi sanadin mutuwar fararen hula.

"Tsarin iko a Iran mai rikitarwa"

A wani sharhi da ta wallafa, babbar wakiliyar harkokin waje ta kafara yada labarai ta Politico, Nahal Toosi, ta yi duba kan daya daga cikin tambayoyin da suka fi daukar hankalin jami'an gwamnatin Donald Trump tun bayan fara yakin: Me ya sa gwamnatin Iran ba ta ruguje ba?

Marubuciyar ta ce wani bangare na kuskuren lissafin gwamnatin Trump ya samo asali ne daga watsi da daya daga cikin muhimman ka'idojin yaki, wato sanin abokin gaba.

Ta ce baya ga samar da makamai da kuma kulla kawance, da fahimtar karfi, da gazawa da juriyar bangaren da ake fada da shi na taka muhimmiyar rawa wajen tantance sakamakon rikici.

A cewarta, wani bangare na matsalar shi ne yadda wasu jami'an Amurka suka kasa fahimtar tsarin iko a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ta ce duk da kasancewar bangarori daban-daban da cibiyoyin iko masu ra'ayi daban-daban a cikin tsarin, hakan bai taba haifar da irin rabuwar kai ko rikicin cikin gida da wasu jami'an Amurka suka yi tsammani ba.

Ta rubuta cewa:

"An ware wasu mutane daga gwamnati ko kuma an rage tasirinsu, amma tsarin ya ci gaba da kasancewa a dunkule kusan tsawon shekaru hamsin, har ma a lokutan dogayen yake-yake. Jamhuriyar Musulunci ba ta taba fuskantar rarrabuwar kai ko rugujewa ba."

Marubuciyar ta bayyana watsi da wannan hakika a matsayin raunin da ya fi addabar tsarin yanke shawarar gwamnatin Donald Trump, tana mai gargadin cewa dogaro da tunanin cewa akwai "babbar tsaga a cikin gwamnati" na iya haifar da kuskuren lissafi wajen tattaunawa, da kakaba takunkumi ko ma daukar matakin soja.

Ta ce har yanzu Fadar White House na ganin cewa ta fi masu suka da manazarta da ke wajen gwamnati sanin Iran.

Don nuna wannan ra'ayi, Toosi ta nakalto mai magana da yawun Fadar White House, Anna Kelly, wadda ta ce:

"Wadannan manazarta na waje hasashe kawai suke yi. Abu ne mai ban mamaki a ce wai sun fi masu tattaunawar Amurka da suka gana kai tsaye da jami'an Iran fahimtar matsayin Iran."

Sai dai kuma Nahal Toosi ta ce Iran na cikin wani yanayi na musamman mai rauni a halin yanzu. A cewarta, kasar ba ta taba kasancewa cikin irin wannan kadaici ko matsin lamba ba.

Ta rubuta cewa:

"Hukumomin tsaron Iran da ma'ajiyoyi makamanta sun sha munanan hare-hare.

An kashe manyan jami'ai da dama, ciki har da tsohon jagoranta, a farkon kwanakin yakin.

Iran na fama da takunkumin toshe hanyoyinta na teku da Amurka ta yi, da karin takunkumi, sannan kuma tana ci gaba da fuskantar hare-haren sama na Amurka."

Duk da haka, Toosi ta ce akwai batu guda da masana kan Iran da kuma jami'an gwamnati na yanzu da na baya da suka tattauna da Politico suka amince a kai:

"Canje-canjen matsayi da sauyin tasiri a cikin tsarin mulkin Iran ba sabon abu ba ne. Sabanin ra'ayoyin da ake gani sun fi kasancewa kan dabaru ne, ba kan manyan manufofin kasa da dabarun dogon lokaci ba."

Abin da ke fitowa daga wadannan rahotanni na iya nuna irin hadin kai a gwamnatin Iran da kuma sabani a Ma'aikatar Tsaron Amurka.

Sai dai watakila abin da ya fi muhimmanci shi ne bambancin yanayin kafafen yada labarai da kuma samun bayanan sirri a kasashen biyu.

A Iran, kafafen yada labarai ba su da damar kalubalantar manufofin gwamnati ko bayar da rahotanni kan sabanin ra'ayi a matakai mafiya girma na mulki.

A Amurka kuwa, duk da kokarin gwamnati na dakile yaduwar bayanai da kuma sarrafa labarin da ake fitarwa a hukumance, kafafen yada labarai sun samu damar fallasa sabanin ra'ayi tsakanin wasu manyan kwamandojin soja da Sakataren Tsaro, da murabus din Sakataren Sojojin Kasa, har ma da cikakkun bayanai kan wani harin da ya haddasa ce-ce-ku-ce a wani bikin aure a kudancin Iran.

Saboda haka, babban bambancin na iya zama ba wai rashin jituwa ko kuma jituwar ba ne, illa dai yadda ake bayyana ta ga jama'a.

A gefe guda, sabani da rikice-rikice na cikin gida na ci gaba da kasancewa a boye daga idon jama'a, yayin da a daya gefen kuma kafafen yada labarai masu zaman kansu ke iya fito da wasu daga cikin wadannan rikice-rikice fili ga jama'a.