Manyan tarihi 7 da aka kafa a kasuwar ƴan ƙwallon Turai ta 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Kasuwar saye da sayar da ƴan wasa ta bana a nahiyar Turai ta kasance ɗaya daga cikin mafi ƙayatarwa da kuma tsada a tarihin ƙwallon ƙafa, inda manyan ƙungiyoyi suka kashe biliyoyin kuɗaɗe domin ƙarfafa tawagoginsu.

Yayin da aka rufe kasuwar daren da ya gabata, ƙungiyoyi da dama sun yi sayi fitattun ƴan wasa, tare da karya wasu tsofaffin tarihin cinikayya da kuma yin wasu sayayyar da suka ɗauki hankalin masu bibiyar harkokin wasanni a duniya.

Ƙungiyoyin Gasar Premier Ingila ne suka fi fitowa fili wajen kashe kuɗi, amma manyan ƙungiyoyi daga Spain da Jamus da Faransa da Italiya su ma ba a bar su a baya ba, yayin da kowacce ke ƙoƙarin ƙarfafa tawagarta domin fafatawa a gasa daban-daban.

Wasu daga cikin waɗannan cinikayyar sun janyo muhawara saboda yawan kuɗin da aka kashe, yayin da wasu kuma suka kasance abin mamaki sakamakon yadda ƴan wasan suka sauya sheƙa ƙungiyoyin da suka shafe shekaru suna taka leda a cikinsu.

A wannan muƙala mun yi nazarin manyan cinikayyar ƴan wasan da suka fi ɗaukar hankali a Turai a shekarar 2026, tare da duba kuɗaɗen da aka kashe da dalilan da suka sa aka ƙulla yarjejeniyoyin, da kuma yadda ake sa ran waɗannan sauye-sauyen za su yi tasiri ga ƙungiyoyin a kakar da aka fara

Morgan Rogers: Ɗan wasan Ingila mafi tsada a tarihi

Cinikin ɗan wasan tawagar ƙasar Ingila, Morgan Rogers mai shekara 23 ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fi ɗaukar hankalin masu bibiyar ƙwallon ƙafa a wannan bazara, domin yana cikin mafi tsadar cinikayyar da aka taɓa yi a Ingila.

Rogers, wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba, ya yi fice tare da Aston Villa a kakar wasan da ta gabata, inda ya zura ƙwallaye 10 sannan ya bayar da taimakon ƙwallaye shida a wasanni 37 na Gasar Premier.

Bajintar da ya nuna ta sa ya zama wanda manyan ƙungiyoyin Premier suka sanya a gaba wajen neman ɗaukarsa.

Daga ƙarshe dai ɗan wasan ya koma Chelsea a wata yarjejeniya da darajarta ta kai fam miliyan 157.95, lamarin da ya sanya cinikin nasa ya zama mafi tsada da aka yi a ƙasar Ingila

Enzo Fernandez: Mafi tsada a tarihin Man City

A ranar ƙarshe na rufe kasuwar musayar ƴanwasan Manchester City ta sayi ɗan wasan Chelsea, Enzo Fernandez a matsayin mafi tsada a tarihinta kan kuɗi fam miliyan 125.

Haka kuma ɗan ƙasar Argentinan ya kamo tarihin Alexander Isak ya kafa na zama ɗanwasan Premeir mafi tsada a tarihi.

Ɗaukar Fernandez ya sa ya Man City ta kafa tarihin zama ƙungiyar da ta fi kashe kuɗi a kasuwar musayar ƴan wasa ta bazara ɗaya, inda ta kashe fam miliyan 458 jimilla, inda ta karya tarihin da Liverpool ta kafa a barazar bara na kashe fam miliyan 415 a bazara ɗaya.

Kafin Fernandez, City ta ɗauki Elliot Anderson daga Nottingham a watan Yuli kan fam miliyan 116.

Yan Diomande: Mafi tsada a tarihin Madrid

Ɗan wasan gefe na tawagar ƙasar Ivory Coast, Diomande, ya lashe kyautar Gwarzon Matashin Ɗan wasa na Bundesliga bayan ya zura ƙwallaye 12 tare da bayar da taimakon ƙwallaye takwas a lokacin da yake taka leda a RB Leipzig.

Hazakar ɗan wasan mai shekara 19 ta ja hankalin manyan ƙungiyoyin Turai, kafin daga bisani ya koma Real Madrid a wata yarjejeniya da darajarta ta kai dala miliyan 162.

Real Madrid, wadda aka fi sani da Los Blancos ko kuma "sarautar ƙwallon ƙafa" a Turai, ta kuma ƙara wasu fitattun ƴan wasa a tawagarta a wannan bazara.

Sabbin ƴan wasan da ta ɗauka sun haɗa da ɗan bayan Spain Marc Cucurella da ɗan bayan Holland Denzel Dumfries da ɗan bayan Faransa Ibrahima Konate da kuma ɗan wasan tsakiya na ƙasar Portugal Bernardo Silva.

Waɗannan sauye-sauyen na nuna ƙudirin Real Madrid na ƙara ƙarfafa tawagarta domin ci gaba da fafatawa a manyan gasa na cikin gida da kuma na Turai a kakar wasa mai zuwa.

Da yake magana da BBC, mai sharhin wasanni Issa Al-Mismar ya ce daga cikin cinikin ƴanwasan da suka fi ɗaukar hankali a Turai a wannan bazara akwai na Yann Diomande da Morgan Rogers da kuma Elliott Anderson.

A cewarsa, waɗannan cinikayyar sun nuna yadda manyan ƙungiyoyin Turai ke ci gaba da zuba jari wajen sayen matasa masu hazaka domin ƙarfafa tawagoginsu kafin fara sabuwar kakar wasa.

Sandro Tonali: Ɗan wasan Italiya mafi tsada

Ɗan wasan tsakiya na Italiya, Sandro Tonali, ya yi fice a Gasar Premier Ingila a ƙungiyar Newcastle United, kafin ya fara sabon babi a Tottenham Hotspur, wadda ke cikin ƙungiyoyin da suka fi kashe kuɗi wajen sayen 'yan wasa a wannan kakar.

An rawaito cewa cinikin ya kai dala miliyan 124.9, tare da yiwuwar ƙarin kuɗaɗe da za su iya ɗaga darajarsa zuwa dala miliyan 135.

Hakan ya sa Tonali ya zama ɗan wasan Italiya mafi tsada a tarihi, kana kuma ɗan wasa mafi tsada da Tottenham ta taɓa saya.

Komawar tasa na zuwa ne bayan ya shafe kaka uku a Newcastle United, wadda ya koma daga AC Milan a watan Yulin 2023 kan kuɗin da aka ruwaito sun kai fam miliyan 74.25.

Ayyoub Bouaddi: Balaraben ɗanwasa mafi tsada

Bajintar da matashin ɗan wasan Morocco, Ayyoub Bouaddi mai shekara 18 ya nuna a Gasar Ligue 1 ta Faransa da kuma Gasar Kofin Duniya ta 2026 ta taimaka wajen komawarsa Manchester City daga Lille ta Faransa.

Ɗan wasan na tawagar ƙasar Morocco ya koma Ingila ne a yarjejeniyar da aka fara kimanta darajarta da dala miliyan 109.89, tare da yiwuwar ƙarin dala miliyan 5.67 idan ya cika wasu sharuɗɗan da ke cikin kwantiragin.

Komawarsa Etihad ya sa Bouaddi ya zama ɗan wasan Larabawa mafi tsadar ciniki a tarihin ƙwallon ƙafa.

Haka kuma ya kafa tarihin zama ɗan wasa mafi tsada da aka taɓa sayarwa daga wata ƙungiya da ke buga Gasar Ligue 1 ta Faransa, lamarin da ke nuna irin ƙimarsa a idanun manyan ƙungiyoyin Turai.

Ana sa ran matashin ɗan wasan zai taka muhimmiyar rawa a shirin Manchester City na ci gaba da fafatawa domin lashe manyan kofuna a Ingila da kuma Turai a shekarun da ke gaba.

Gonzalo Ramos: Mafi tsada a tarihin AC Milan

Bayan da kocin Portugal Ruben Amorim ya karɓi aikin horas da AC Milan, Gonzalo Ramos mai shekara 25, ya koma ƙungiyar ta Italiya.

Ɗan wasan gaban ya bar Paris Saint-Germain zuwa AC Milan a wata yarjejeniya da ta kai Yuro miliyan 81.27, lamarin da ya sa ya zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin ƙungiyar ta Milan.

A tsawon shekaru uku da ya yi tare da ƙungiyar ta Faransa, Ramos ya zura ƙwallaye 45 a raga cikin wasanni 131 da ya buga, abin da ya taimaka wajen jawo hankalin Milan.

Rodri zuwa Barcelona

Rodri, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa a Gasar Kofin Duniya, ya koma Barcelona a ɗaya daga cikin manyan cinikin ƴan wasa da suka fi ɗaukar hankali a kasuwar ƴan wasa ta bana.

Da farko an yi ta alaƙanta kyaftin ɗin tawagar Sifaniyar da komawarsa Real Madrid, amma daga ƙarshe ya zaɓi Barcelona, babban abokiyar hamayyar Madrid.

Ya koma ƙungiyar ta Catalonia daga Manchester City kan kuɗin da aka rawaito sun kai fam miliyan 87.75.

Ana sa ran ɗan wasan na tsakiya, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or a 2024, zai ƙara wa tawagar Barcelona ƙarfi, musamman yadda ,kungiyar ke amfani da salon sarrafa wasa da kuma ƙwato ƙwallo daga hannun abokan hamayya.

Da yake magana da BBC, mai sharhi kan harkokin wasanni Issa Al-Masar ya bayyana komawar Rodri Barcelona a matsayin "mataki mai ma'ana kuma mai ƙarfi" ga ƙungiyar ta Catalonia.