Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannans ahfi na kawo muhimman al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 02/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Aisha Babangida

  1. Muna fatan Iran da Amurka za su koma teburin Sulhu - Pakistan

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce har yanzu tana da fatan cewa Iran da Amurka za su koma teburin tattaunawa domin warware matsalolinsu.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana cewa ziyarar da Field Marshal Asim Munir, shugaban rundunar sojin Pakistan, ya kai Tehran, ta haifar da gagarumin ci gaba wajen buɗe ko ciyar da batun mashigin Hormuz gaba.

    Pakistan ce take taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka dangane da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.

    Sai dai duka Iran da Amurka sun bayyana cewa an karya wannan yarjejeniya, kuma ba sa ci gaba da bin tanade-tanadenta.

    Iran ta sanar da cewa za ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar Islamabad idan har Amurka ta koma aiwatar da nata ɓangaren yarjejeniyar.

  2. Cutar diphtheria ta ɓulla a Filato, Katsina da Kano

    Cutar Mashaƙo na ci gaba da yaɗuwa a wasu sassan jihohin Filato, Katsina da Kano, inda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da janyo rashin lafiya ga wasu dayawa.

    A Jihar Filato kaɗai, aƙalla mutum 23 sun mutu yayin da ake zargin mutane 143 sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi daban-daban, musamman a Jos ta Arewa.

    Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Nicholas Baamlong, ya ce yawancin mace-macen sun faru ne cikin makonni uku da suka gabata, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar.

    Ya bayyana cewa wasu marasa lafiya tara na karɓar magani a cibiyoyin killace masu ɗauke da cutar, inda ya ce ƙarancin maganin cutar antitoxin da kuma jinkirin kai marasa lafiya asibiti na daga cikin manyan ƙalubalen yaƙi da cutar.

    Hukumomi sun ƙaddamar da yaƙin wayar da kai tare da neman tallafi daga Hukumar NCDC domin samar da magunguna da kayan gwajin cutar.

  3. Red Crescent ta Iran ta kai ƙarar harin da Amurka gaban ICC

    Hukumar ba da agajin gaggawa ta Iran (IRCS) ta rubutawa Kotun Hukunta Manyan Laifuks ta Duniya da ke Hague wata wasiƙa inda ta kai ƙarar Amurka kan harin da ta kai wani taron ɗaurin aure a Kudancin Iran.

    A cikin wasiƙar Red Crescent ta ce mutane huɗu sun mutu ciki har da wani yaro guda, kuma sun mutu ne dalilin harin da Amurkan ta kai. An kuma rawaito cewa mutum 67 sun jikkata.

    Hukumar ta ce an kai harin ne da misalin ƙarfe 21:30 na safe a ranar Talata, lokacin da ake gudanar da bikin auren a garin Kuhestak da ke yankin Sirik.

    "Idan aka la'akari da mummunan halin da wadanda suka jikkata ke ciki, za a iya samun ƙarin waɗanda suka mutu a nan gaba," kamar yadda sanarwar da aka watsa a Telegram ta bayyana. Auren dai na fararen hula ne.

  4. Ya kamata ƴan APC su tausasa harshensu lokacin kamfe - Kawu Sumaila

    Sakamakon yadda sauye-sauyen da gwamnatin hugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ta jam'iyyar APC ta kawo a kasar wadanda wasu ke gani sun haifar da wahalahalu na tsanani na rayuwa, wani jigo a jam'iyyar kuma dan majalisar dattawa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya shawarci ƴan jam'iyyar su yi amfani da kalamai na sanin ya kamata da mutuntawa da kuma tausasa harshe wajen yakin neman zaɓen 2027.

    Sanatan ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya yi da BBC, yana mai nuni da cewa yadda yan kasar suka fusata da halin tabarbarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa to sai an bi su da kalamai na shawo kai.

    Danmajalisar Dattawan ya ce ya mika wa kwamitin yakin neman sake zaben Shugaba Tinubu wasu jerin shawarwari da suka shafi rayuwar 'yan Najeriya, wadanda ya ce ya 'yan kwamitin ya kamata su yi amfani da su a aikinsu na kamfe.

    Ya yi karin bayani da cewa: ''Na yi kira ga shi Abdul'aziz Abubakar Yari da 'yan kwamitinsa da mu da muka shiga zabe cewa mu gaya wa kanmu gaskiya, mu kalli halin da Najeriya take ciki.''

    ''Akwai abubuwa guda uku kwarara wadanda dole maganganunmu sai sun nuna a jikinmu mun san wani abin yana faruwa,'' in ji shi.

    Ya ce, ''Akwai kalubale na tsaro wanda mutane suna rasa rayuwarsu kuma wasu suna cikin wani yanayi na rashin jin dadi na barin garuruwansu, akwai abin tausayawa. Ga zama a cikin tsoro a bangarori da dama a karkashin jagorancinmu.''

    To amma kuma Kawu Sumailan ya kara jaddada irin zargin da ake yi a kan wasu daga cikin 'yan kwamitin yakin neman zaben Shugaba Tinubun na cewa wasunsu da dama suna da kashi a gindinsu, duka da cewa 'yan jam'iyyarsa ne ta APC, inda ya ce:

    ''Gaskiyar magana da yawa daga cikin mambobin wannan kwamitin su ne matsalar gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da APC.''

    ''Yan jam'iyyarmu amma kowa zai amsa sunan ubansa. Kowa yana komawa gida a zabo shi ya taho.''

    Ya ce,'' Kuma dukkan irin wadannan abubuwa mun fada a zaman sirri, mun fada a zaman fili, sannan mun fada wajen 'yan jaridu.''

    ''Na duba na ga yawan wadanda suke cikin wannan kwamiti sun taimaka kwarai da gaske wajen tsunduma gwamnatin APC da tsunduma gwamnatin Tinubu cikin matsalar da ake kallonta da shi.''

    Sanatan mai wakilitar mazabar Kano ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya ya yi karin haske da cewa muhimmin aiki da kuma kasancewar gwamnati na farko shi ne ta tabbatar da tsaron rayuwa da mutunci da dukiyar al'ummarta, daga nan kuma sai samar da abubuwa na more rayuwa su biyo baya.

    Dangane da hakan ya nuna lalle akwai gazawar gwamnati a wannan bangare na sauke nauyin da ke kan gwamnati a kan al'ummarta.

    Ya ce: ''To mutane ba za su gamsu ba matukar ba su ga ko'ina an zauna lafiya ba.Matukar ba su yaba a zahiri sun fito sun ga kokarin da muke yi ba. To duk kokarin da muke yi ya kamata mu tausaya a irin maganganunmu.''

    Kawu ya kwatanta shugabanci da yadda likita yake yi wa maras lafiya magani, da cewa likita yana kokarin yi mawa mutum magani yana tausaya masa amma kuma alokaci guda yana yi masa abin da ke sa mutumin ya ji zafi domin ta hakan ne zai samu lafiya.

    Ganin cewa Sanatan yana daya daga cikin fitattun 'yan jam'iyyar APC daga Kano wanda kuma ya tsaya takarar sake neman kujerar sanatan da yake kai, ya fito yana nuna cewa lalle akwai matsalar a yadda jam'iyyar za ta tunkari al'ummar Najeriya kan su sake zabenta a 2027 sai ya ce:

    ''Babu wani abu ai magana ce ta mu gaya wa kanmu gaskiya kuma duk wanda yake bin maganganu na haka ne dole za ka fade su da dadi ba dadi. In ma an ki maganar da muka fada daga baya za a zo a yarda da ita.''

    Dangane da yadda 'yan adawa ke ganin APC din ba ta abin da yza ta yi wa 'yan kasar yakin neman zabe da su, sai Kawu Sumaila ya ce:

    ''Daga daya zuwa goma zan iya lissafa maka 'yan'adawa da suka yi wa Najeriya illar da APC ba ta yi mata ba , kuma idan aka fito da ita tashin hankali ne. Su su ma dawo su shiga zabe abin kunya ne don ba irin karyar da ba su yi wa 'yan Najeriya ba.''

    Sanata Kawu ya ce shi dai rokon da zai yi shi ne musamman 'ga Arewacin Najeriya shi ne jama'a su daina duba cewa sai gwamnati ko dan APC ko jami'an tsaro ne za su yi, kowa ya bayar da gudummawarsa a ceto yankin daga halin da yake ciki.

  5. Tankokin mai biyu sun tarwatse bayan taka nakiyoyi a mashigar Hormuz - Iran

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce tankokin mai guda biyu sun tarwatse tare da kama da wuta bayan sun taka nakiyoyin ruwa a Mashigar Hormuz.

    A cikin wata sanarwa, IRGC ta zargi sojojin Amurka da karkatar da jiragen zuwa wata hanya da ta bayyana a matsayin haramtacciya, inda ta ce jiragen sun faɗa hannun jami'an Amurka bayan an sauke ma'aikatansu.

    Rundunar ta ce a baya ta yi gargaɗi kan haɗarin amfani da wata mashiga da aka dasa nakiyoyi a cikinta, tare da yin barazanar hukunta kamfanonin jiragen ruwa da ba su bi hanyar da ta amince da ita ba.

    An ce tankokin biyu na ci gaba da ƙonewa bayan aukuwar lamarin.

  6. Hare-haren Iran: Amurka ta buƙaci ƴan ƙasarta a Gabas ta Tsakiya su yi taka-tsantsan

    Amurka ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke zaune ko tafiya a ƙasashen Gabas ta Tsakiya su ƙara yin taka-tsantsan saboda fargabar hare-haren Iran da ƙarin tashe-tashen hankula da ka iya biyo bayan rikicin da ke ƙara tsananta a yankin.

    Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abu Dhabi da kuma Ofishin Jakadancin Amurka na Dubai sun yi gargaɗin yiwuwar samun abubuwan da ba a yi tsammani ba, inda suka shawarci Amurkawa su kasance cikin shiri saboda yiwuwar soke jirage, rufe sararin samaniya da kuma wasu matsalolin tafiye-tafiye.

    Sanarwar ta kuma tunatar da cewa cibiyoyin diflomasiyyar Amurka sun taɓa zama abin hari a Gabas ta Tsakiya da wasu sassan duniya a baya.

    Haka kuma ta yi gargaɗin cewa Iran da ƙungiyoyin da ke mara mata baya na iya kai hare-hare kan wasu muradun Amurka a ƙasashen ƙetare, ciki har da kamfanoni da cibiyoyin da ke da alaƙa da Amurka.

  7. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 252 a Najeriya — NCDC

    Cibiyar daƙile cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar zazzaɓin Lassa ya kai 252 a bana, yayin da adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya kai 1,035.

    NCDC ta ce an samu sabbin mutum 14 da aka tabbatar sun kamu da cutar tsakanin 10 zuwa 16 ga watan Agusta a jihohin Ondo, Bauchi, Edo da Benue.

    Hukumar ta ƙara da cewa yawan mace-macen ya sa adadin masu mutuwa daga cutar ya kai kashi 24.4 cikin 100, wanda ya fi na shekarar 2025 da ya tsaya a kashi 18.6 cikin 100.

    A cewar NCDC, jihohi 23 sun riga sun samu aƙalla mutum ɗaya da aka tabbatar ya kamu da cutar a ƙananan hukumomi 117, kuma hukumar na ci gaba da sa ido da ɗaukar matakan daƙile yaɗuwar cutar.

  8. Iran ta gargaɗi ƙasashe kan haɗin gwiwa da Amurka wajen kai mata hari

    Hedikwatar Khatam al-Anbiya ta Iran ta gargadi ƙasashen yankin da ke haɗin gwiwa da sojojin Amurka wajen kai mata hari tana cewa su sa ran fuskantar mummunan sakamako.

    Gargadin ya zo ne bayan hare-haren da Amurka ta kai wasu yankunan kudancin Iran a daren Talata.

    Iran ta ce dakarunta sun mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin Amurka da ke Jordan, Bahrain da Erbil na Iraqi.

    Hedikwatar ta kuma yi gargaɗi ga ƙasashen da ke karɓar sojojin Amurka, tana cewa duk ƙasar da ta taimaka wa abin da ta kira sojojin Amurka masu kai hari, za su ɗanɗana kuɗarsu.

    A gefe guda, Iran ta ce hare-haren Amurka sun kashe fararen hula aƙalla biyar tare da jikkata sama da 60 a ƙauyen Kohstak da ke Sirik, yayin da ake gudanar da bikin aure.

    Rahotannin kafofin yaɗa labaran Iran sun ce yara na cikin waɗanda suka mutu, yayin da mata da yara ke cikin mafi yawan waɗanda suka jikkata.

  9. Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin Amurka a Bahrain da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa

    Sojojin Iran sun sanar da cewa sun kai hare-hare da jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin sojojin Amurka da ke ƙasashen Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

    A cewar sanarwar rundunar, an kai harin ne a sansanonin Dhafra da Manhad na UAE, tare da kai wasu hare-hare a sansanin Sheikh Isa da ke Bahrain.

    Iran ta ce hare-haren sun zo ne a matsayin martani ga hare-haren jiragen yaƙin Amurka da aka kai a baya.

    Sa'o'i kaɗan kafin haka ma,rundunar juyin juya halin Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Kuwait da Jordan.

  10. Jami’in sojin Nijar ya zargi ƙasashen waje da hannu a boren sojoji a ƙasar

    Wani jami’in sojin Nijar, Roger Gabriel, ya zargi wasu ƙasashen waje hannu a boren da sojoji suka yi a sansanin sojin 101 da ke Yamai a ranar 29 ga Agusta.

    Ya ce ya samu kira da saƙonni daga mutane a Nijar da ƙasashen waje da ke nuna tsoma bakin ƙasashen waje da ke goyon bayan waɗanda suka kai hari a sansanin.

    Jami’in ya yi zargin cewa wasu jami’ai daga Chadi da wasu masu alaƙa da tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, sun ambaci yiwuwar taimakon ƙasashen waje da dakarun musamman.

    Sai dai ba a tabbatar da waɗannan zarge-zarge da wata hujja mai zaman kanta ba.

    Hukumomin Nijar dai sun ce sun shawo kan lamarin bayan harbe-harbe da aka yi a sansanin.

  11. Ba na son ƙulla wata yarjejeniya da Iran - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta wani rahoto da ABC News ta wallafa a daren Talata, inda ya zargi kafar da ya ƙirƙirar labaran ƙarya da bayar da rahoton cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin tilasta Iran ta shiga tattaunawa.

    Trump ya ce ba shi da sha’awar ƙulla wata yarjejeniya da Tehran.

    "Saɓanin abin da ABC, wadda nake kira Fake News, ta ruwaito, ba na ƙoƙarin dawo da Iran kan teburin tattaunawa. Ba ni da wata sha’awa ga su sa hannu kan wata yarjejeniya da ba ta da wani amfani a gare su," in ji Trump kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

    "Na fi son halin da ake ciki a yanzu, inda muke daf da samun cikakken iko kan mashigin Hormuz, yayin da tattalin arzikin Iran ke ci gaba da durƙushewa gaba ɗaya. Suna kawai ƙoƙarin jinkirta abin da babu makawa zai faru."

    A ƙarshen saƙonsa, shugaban na Amurka ya ce "Yaushe mutanen Iran za su tashi su yi gwagwarmaya?"

    Kalaman Trump sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan da ya bayyana sabbin hare-haren da Amurka ta kai a kusa da mashigin Hormuz a matsayin "waɗanda suka dace", tare da gargadin cewa Washington za ta kaddamar da hare-hare masu ƙarfi fiye da haka idan Iran ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

    Iran ta ce hare-haren sun auka kan fararen hula da ke halartar wani bikin aure a ƙauyen Kohstak Sirik, inda aƙalla mutum biyar suka mutu, ciki har da yaro ɗaya.

    Kafafen yaɗa labarai na Iran sun kuma ruwaito cewa mutane sama da 60 sun jikkata a harin.

  12. Harin Amurka ya kashe jami’an Rundunar Sararin Samaniya ta IRGC huɗu

    Ofishin Hulɗa da Jama'a na Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) a lardin Kermanshah ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa mambobi huɗu na Rundunar Sararin Samaniya ta IRGC a lardin sun mutu sakamakon harin da Amurka ta kai.

    Ba a bayyana ƙarin cikakkun bayanai game da lamarin ba.

    A daren jiya, bayan hare-haren Amurka, mataimakin gwamnan lardin Kermanshah ya ce babu wani yanki na lardin Kermanshah da aka kai wa hari.

    A cewar kafafen yaɗa labarai na Iran, mataimakin kwamandan Rundunar Seyyed al-Shohada a birnin Diyar ya kuma ce a yau cewa mayaƙan Basij uku sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin da aka kai kan tsibirin Lavan.

  13. Pakistan: Muna fatan Iran da Amurka za su koma kan teburin tattaunawa

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana cewa har yanzu tana da fatan cewa Iran da Amurka za su koma kan teburin tattaunawa domin warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar diplomasiyya.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce ziyarar da Field Marshal Asim Munir, babban hafsan sojojin Pakistan, ya kai Tehran ta "haifar da gagarumin ci gaba wajen buɗe ko ciyar da batun mashigin Hormuz gaba."

    Pakistan na taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka dangane da tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.

    Duk da haka, Iran da Amurka sun bayyana cewa an karya wannan yarjejeniya, kuma ba sa ci gaba da bin tanade-tanadenta.

    Iran ta sanar da cewa za ta koma bin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad idan har Amurka ta sake fara aiwatar da nata ɓangaren yarjejeniyar.

  14. Abin da muka sani game da lafiyar Mojtaba Khamenei

    Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga shugabannin kasashen Musulmi, musamman na Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha, da su haɗa kai domin tunkarar Amurka da Isra'ila. Wannan kira na kunshe ne a cikin wani sako da kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya wallafa.

    Sakon ya zo ne watanni shida bayan hare-haren Amurka da Isra'ila, da suka yi ajalin mahaifinsa, tsohon Jagoran Addinin Iran Ali Khamenei, tare da ji wa Mojtaba munanan raunuka, kamar yadda wasu majiyoyi na kusa da muƙarrabansa suka shaida wa Reuters.

    A cikin sakon da aka gabatar yayin taron Makon Hadin Kan Musulunci, Khamenei ya ce shugabannin kasashen yankin dole ne su "gano hakikanin makiyansu, su fahimci shirye-shiryensa, sannan su fahimci manufofinsa," yana nufin Amurka da Isra'ila, kamar yadda IRNA ta ruwaito.

    Ya kara da cewa Washington da Isra'ila ba makiyan Iran da abin da ya kira "gungun masu adawa" kawai ba ne, makiyan sauran dukkan kasashen Musulmi na yankin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka ne, har da waɗanda ke haɗa gwiwa da su.

    Wannan shi ne sako na biyu da ya fitar sako a baya-bayan nan yana jaddada muhimmancin hadin kai a cikin gida. A wani sako da aka wallafa ranar 28 ga watan Agusta, ya yi gargadi kan kalamai da za su iya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al'umma, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnatin Iran suka bayyana.

  15. Hare-haren Amurka sun kashe mutum bakwai a Iran

    Wani jami'in ƙaramar hukuma a lardin Khuzestan na ƙasar Iran ya ce mutane bakwai sun mutu, yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Amurka ta kai a daren Talata kan wurare uku a lardin.

    Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya rawaito Valiollah Hayati, mataimakin jami'in tsaro da kula da harkokin tabbatar da doka na lardin Khuzestan, yana cewa biranen Ahvaz da Aghajari ne aka kai wa hari a lokacin hare-haren sama da Amurka ta kai a daren Talatar.

    An kuma ba da rahoton irin waɗannan hare-hare a yankunan bakin teku na lardin Hormozgan.

    A ɗaya daga cikin hare-haren, a cewar jami'ai, aƙalla fararen hula biyar, ciki har da yaro ɗaya, sun mutu a ƙauyen Dehstak Sirik, yayin da sama da mutum 60 da ke halartar wani bikin aure suka jikkata.

  16. Abubuwa biyu da za su iya tantance wanda zai lashen zaɓen Najeriya na 2027

    Yayin da jam'iyyun siyasa da ƴan takara ke ci gaba da zage damtse wajen shirya wa babban zaɓen Najeriya na 2027, akwai abubuwan da masu kaɗa ƙuri'a za su fi la'akari da su wajen zaɓen wanda zai zama shugaban ƙasa.

    Tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, rashin lantarki, matsalolin kiwon lafiya da ilimi da kuma shugabanci na daga cikin abubuwan da ƴan Najeriya ke yawan magana a kansu.

    A baya-bayan nan batun tallafin man fetur ya haifar da muhawara a Najeriya bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ce zai mayar da tallafin idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

    Amma wadanne abubuwa ne za su fi jan hankalin masu kada ƙuri'a gabanin zaɓen 2027?

  17. Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-hare a sansanonin Amurka

    Iran ta ce ta ƙaddamar da jerin hare-hare kan wuraren da Amurka ke amfani da su a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan rahotannin da suka ce ƙarin hare-haren saman da Amurka ta kai sun kashe mutum biyar a wani bikin aure a Iran.

    Iran ta mayar da martani da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a kasashe da dama, inda rahonni ke cewa an tare makamai masu linzami da jiragen sama maras matuka Rundunar juyin-juya-hali ta Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka masu yawa a ƙasar Jordan, maganar da jami'an Amurka suka yi gaggawar musantawa.

    Rundunar ta kuma yi iƙirarin cewa ta samu nasara a wasu hare-haren da ta kai kan wurare a arewacin Iraki.

    A nata ɓangaren, Amurka ta ce, sojojinta suna sane da rahotannin da ke cewa an kai hari kan wurin bikin auren, amma sun musanta cewa sun kai hare-hare da gangan kan fararen hula.

    A cikin 'yan kwanakin nan, Amurka ta ƙara yawan hare-harenta ta sama a yankin bayan wani sararawa ta makonni.

  18. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin Hausa na kai tsaye da fatan an wayi gari lafiya. Yau Laraba da Hausawa ke yi wa taken ta Bawa ranar samu, mun sake dawowa da labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa.