KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannans ahfi na kawo muhimman al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 02/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR da Aisha Babangida

  1. Ba na son ƙulla wata yarjejeniya da Iran - Trump

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta wani rahoto da ABC News ta wallafa a daren Talata, inda ya zargi kafar da ya ƙirƙirar labaran ƙarya da bayar da rahoton cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin tilasta Iran ta shiga tattaunawa.

    Trump ya ce ba shi da sha’awar ƙulla wata yarjejeniya da Tehran.

    "Saɓanin abin da ABC, wadda nake kira Fake News, ta ruwaito, ba na ƙoƙarin dawo da Iran kan teburin tattaunawa. Ba ni da wata sha’awa ga su sa hannu kan wata yarjejeniya da ba ta da wani amfani a gare su," in ji Trump kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

    "Na fi son halin da ake ciki a yanzu, inda muke daf da samun cikakken iko kan mashigin Hormuz, yayin da tattalin arzikin Iran ke ci gaba da durƙushewa gaba ɗaya. Suna kawai ƙoƙarin jinkirta abin da babu makawa zai faru."

    A ƙarshen saƙonsa, shugaban na Amurka ya ce "Yaushe mutanen Iran za su tashi su yi gwagwarmaya?"

    Kalaman Trump sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan da ya bayyana sabbin hare-haren da Amurka ta kai a kusa da mashigin Hormuz a matsayin "waɗanda suka dace", tare da gargadin cewa Washington za ta kaddamar da hare-hare masu ƙarfi fiye da haka idan Iran ta ɗauki matakin ramuwar gayya.

    Iran ta ce hare-haren sun auka kan fararen hula da ke halartar wani bikin aure a ƙauyen Kohstak Sirik, inda aƙalla mutum biyar suka mutu, ciki har da yaro ɗaya.

    Kafafen yaɗa labarai na Iran sun kuma ruwaito cewa mutane sama da 60 sun jikkata a harin.

  2. Harin Amurka ya kashe jami’an Rundunar Sararin Samaniya ta IRGC huɗu

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Ofishin Hulɗa da Jama'a na Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) a lardin Kermanshah ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa mambobi huɗu na Rundunar Sararin Samaniya ta IRGC a lardin sun mutu sakamakon harin da Amurka ta kai.

    Ba a bayyana ƙarin cikakkun bayanai game da lamarin ba.

    A daren jiya, bayan hare-haren Amurka, mataimakin gwamnan lardin Kermanshah ya ce babu wani yanki na lardin Kermanshah da aka kai wa hari.

    A cewar kafafen yaɗa labarai na Iran, mataimakin kwamandan Rundunar Seyyed al-Shohada a birnin Diyar ya kuma ce a yau cewa mayaƙan Basij uku sun mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata a harin da aka kai kan tsibirin Lavan.

  3. Pakistan: Muna fatan Iran da Amurka za su koma kan teburin tattaunawa

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana cewa har yanzu tana da fatan cewa Iran da Amurka za su koma kan teburin tattaunawa domin warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar diplomasiyya.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta ce ziyarar da Field Marshal Asim Munir, babban hafsan sojojin Pakistan, ya kai Tehran ta "haifar da gagarumin ci gaba wajen buɗe ko ciyar da batun mashigin Hormuz gaba."

    Pakistan na taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka dangane da tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad.

    Duk da haka, Iran da Amurka sun bayyana cewa an karya wannan yarjejeniya, kuma ba sa ci gaba da bin tanade-tanadenta.

    Iran ta sanar da cewa za ta koma bin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad idan har Amurka ta sake fara aiwatar da nata ɓangaren yarjejeniyar.

  4. Abin da muka sani game da lafiyar Mojtaba Khamenei

    ..

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga shugabannin kasashen Musulmi, musamman na Gabas ta Tsakiya da yankin Tekun Fasha, da su haɗa kai domin tunkarar Amurka da Isra'ila. Wannan kira na kunshe ne a cikin wani sako da kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya wallafa.

    Sakon ya zo ne watanni shida bayan hare-haren Amurka da Isra'ila, da suka yi ajalin mahaifinsa, tsohon Jagoran Addinin Iran Ali Khamenei, tare da ji wa Mojtaba munanan raunuka, kamar yadda wasu majiyoyi na kusa da muƙarrabansa suka shaida wa Reuters.

    A cikin sakon da aka gabatar yayin taron Makon Hadin Kan Musulunci, Khamenei ya ce shugabannin kasashen yankin dole ne su "gano hakikanin makiyansu, su fahimci shirye-shiryensa, sannan su fahimci manufofinsa," yana nufin Amurka da Isra'ila, kamar yadda IRNA ta ruwaito.

    Ya kara da cewa Washington da Isra'ila ba makiyan Iran da abin da ya kira "gungun masu adawa" kawai ba ne, makiyan sauran dukkan kasashen Musulmi na yankin Yammacin Asiya da Arewacin Afirka ne, har da waɗanda ke haɗa gwiwa da su.

    Wannan shi ne sako na biyu da ya fitar sako a baya-bayan nan yana jaddada muhimmancin hadin kai a cikin gida. A wani sako da aka wallafa ranar 28 ga watan Agusta, ya yi gargadi kan kalamai da za su iya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin al'umma, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnatin Iran suka bayyana.

  5. Hare-haren Amurka sun kashe mutum bakwai a Iran

    Wani jami'in ƙaramar hukuma a lardin Khuzestan na ƙasar Iran ya ce mutane bakwai sun mutu, yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Amurka ta kai a daren Talata kan wurare uku a lardin.

    Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya rawaito Valiollah Hayati, mataimakin jami'in tsaro da kula da harkokin tabbatar da doka na lardin Khuzestan, yana cewa biranen Ahvaz da Aghajari ne aka kai wa hari a lokacin hare-haren sama da Amurka ta kai a daren Talatar.

    An kuma ba da rahoton irin waɗannan hare-hare a yankunan bakin teku na lardin Hormozgan.

    A ɗaya daga cikin hare-haren, a cewar jami'ai, aƙalla fararen hula biyar, ciki har da yaro ɗaya, sun mutu a ƙauyen Dehstak Sirik, yayin da sama da mutum 60 da ke halartar wani bikin aure suka jikkata.

  6. Abubuwa biyu da za su iya tantance wanda zai lashen zaɓen Najeriya na 2027

    ..

    Asalin hoton, Multiple/X

    Yayin da jam'iyyun siyasa da ƴan takara ke ci gaba da zage damtse wajen shirya wa babban zaɓen Najeriya na 2027, akwai abubuwan da masu kaɗa ƙuri'a za su fi la'akari da su wajen zaɓen wanda zai zama shugaban ƙasa.

    Tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi, rashin lantarki, matsalolin kiwon lafiya da ilimi da kuma shugabanci na daga cikin abubuwan da ƴan Najeriya ke yawan magana a kansu.

    A baya-bayan nan batun tallafin man fetur ya haifar da muhawara a Najeriya bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya ce zai mayar da tallafin idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

    Amma wadanne abubuwa ne za su fi jan hankalin masu kada ƙuri'a gabanin zaɓen 2027?

  7. Iran ta ce ta ƙaddamar da hare-hare a sansanonin Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce ta ƙaddamar da jerin hare-hare kan wuraren da Amurka ke amfani da su a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan rahotannin da suka ce ƙarin hare-haren saman da Amurka ta kai sun kashe mutum biyar a wani bikin aure a Iran.

    Iran ta mayar da martani da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a kasashe da dama, inda rahonni ke cewa an tare makamai masu linzami da jiragen sama maras matuka Rundunar juyin-juya-hali ta Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka masu yawa a ƙasar Jordan, maganar da jami'an Amurka suka yi gaggawar musantawa.

    Rundunar ta kuma yi iƙirarin cewa ta samu nasara a wasu hare-haren da ta kai kan wurare a arewacin Iraki.

    A nata ɓangaren, Amurka ta ce, sojojinta suna sane da rahotannin da ke cewa an kai hari kan wurin bikin auren, amma sun musanta cewa sun kai hare-hare da gangan kan fararen hula.

    A cikin 'yan kwanakin nan, Amurka ta ƙara yawan hare-harenta ta sama a yankin bayan wani sararawa ta makonni.

  8. Buɗewa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu bibiyar shafin Hausa na kai tsaye da fatan an wayi gari lafiya. Yau Laraba da Hausawa ke yi wa taken ta Bawa ranar samu, mun sake dawowa da labarai da rahotanni dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa.