Gaske ne Opay zai dakatar da aiki a watan Satumba?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Alamu na nuna cewa cikin ƴan Najeriya da dama ya ɗuri ruwa bayan wani saƙon bogi da ya yi yawo a kafafen sada zumunta ya yaɗa cewa kamfanin zai dakatar da aiki a ranar Litinin.

A ranar 30 zuwa 31 ga Agustan 2026, wani saƙo na bogi ya yaɗu a kafafen sada zumunta yana cewa OPay zai dakatar da harkokinsa daga ranar 1 ga watan Satumban 2026, kuma ya buƙaci kwastomomi su cire kuɗaɗensu.

Sai dai OPay ya fito fili ya musanta wannan rahoto, yana mai cewa ƙarya ce kuma an ƙirƙiri labarin ne domin yaudarar jama'a.

Ba a dai san takamaiman wanda ya ƙirƙiri wannan saƙon na bogi ba, amma akwai wasu dalilai da ake yawan ganin irin waɗannan jita-jita suna yaɗuwa.

Martanin Opay

Har yanzu babu hujjar da ta nuna wanda ya ƙirƙiri wannan labari ko ainihin manufarsa. Amma OPay ya tabbatar cewa saƙon bogi ne, kuma da alama an yaɗa shi ne domin tayar da hankali, haifar da rudani, ko kuma rage amincewar jama'a ga kamfanin.

A wata sanarwa da Opay ya fitar a ranar Lahadi a shafinsa na X, kamfanin ya ce ƙarya ce tsagwaronta cewa zai dakatar da aiki domin yin hutu a watan Satumba.

"OPay ba zai tsaya aiki a watan Satumba ba. Muna nan kuma ba za mu je ko'ina ba."

Haka kuma ya ce dukkan ayyukansa na ci gaba kamar yadda aka saba, kuma ofisoshinsa da hidimominsa a faɗin Najeriya suna aiki yadda ya kamata.

OPay ta shawarci masu amfani da manhajarta da su riƙa dogaro da bayanan da ke fitowa daga shafukanta na hukuma kawai, kada su yarda da saƙonnin da ake tura wa ta WhatsApp ko kafofin sada zumunta ba tare da tabbaci ba.

Mene ne Opay?

OPay kamfani ne na fasahar kuɗi (fintech) da ke ba mutane damar yin hada-hadar kuɗi ta wayar hannu, kamar aika kuɗi, karɓar kuɗi, ajiya, biyan kuɗin wuta, sayen kati, da sauran ayyukan banki ta manhaja. Kamfanin yana daga cikin manyan kamfanonin kudi na dijital da ke aiki a Najeriya.

Opay kamfani ne na fasahar kuɗi da ke ba da ayyukan kuɗi ta hanyar lasisin da yake da shi a Najeriya. Kamfanin ya bayyana cewa yana aiki ne a ƙarƙashin dokokin babban bankin Najeriya (CBN), kuma ana kula da ajiyar kwastomomi ta hanyoyin da aka tanada.

OPay wata manhaja ce ta kuɗi da ke ba mutane damar gudanar da yawancin ayyukan banki ta waya ba tare da zuwa reshen banki ba.

Ta zama ɗaya daga cikin hanyoyin da mutane da dama a Najeriya ke amfani da su wajen tura kuɗi da biyan buƙatun yau da kullum

A baya-bayan nan, Opay da takwarorinsa irin su Moniepoint sun samu karɓuwa a wajen ƴan Najeriya saboda dalilai kamar haka.

  • Sauƙin buɗe asusu.
  • Saurin aika kuɗi.
  • Yawan wakilan OPay a kasuwanni da unguwanni.
  • Manhaja mai sauƙin amfani.

OPay ya fara aiki a Najeriya ne a shekarar 2018 bayan samun lasisi daga Babban Bankin Najeriya (CBN) a shekarar, inda kuma ya ƙaddamar da manhajarsa ta biyan kuɗi da walat na dijital domin sauƙaƙa hada-hadar kuɗi ga 'yan ƙasar.

A cewar bayanan da OPay ya fitar a shekarar 2026, kamfanin yana da sama da masu amfani miliyan 45 a Najeriya. Haka kuma yana aiki da'yan kasuwa da dillalai sama da miliyan ɗaya a faɗin ƙasar.