Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An murƙushe yunƙurin sojoji na yin bore a Nijar - Gwamnati
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi bayani kan harbe-harben da aka kwashe tsawon dare ana ji har zuwa wayeywar garin Asabar a Yamai, babban birnin kasar inda ta ce ta murƙushe yunƙurin bore da wasu sojoji suka yi.
Lamarin ya tayar da hankulan mazauna birnin tare da jawo hankalin ƙasashen duniya.
A cikin sanarwar da ya karanta ta gidan talabijin na gwamnati, ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce kimanin ƙarfe 12:20 na dare wani rukuni na sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.
Sai dai ya ce dakarun ƙasar sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka dakile yunƙurin tare da dawo da doka da oda.
"Bayan jajircewar dakarun ƙasar, yanzu komai ya koma daidai kuma an murƙushe boren da suka so tayarwa," in ji sanarwar gwamnatin.
Kafin wannan bayani daga gwamnati, babu tabbas kan asalin inda ake harbe-harben, kuma ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba.
Ministan bai kuma yi karin haske kan ko akwai wadanda suka rasa rai ko kuma wadanda suka ji rauni ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters dai ya ambato wasu majiyoyin tsaro na cewa an kai hari a filin jirgin saman Yamai tare da yunƙurin kutsawa fadar shugaban ƙasa.
Wasu mazauna Yamai da BBC ta tuntuba sun ce sun ji karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman Diori Hamani, fadar shugaban ƙasa da kuma wasu sansanonin soji.
Wani mazaunin birnin ya shaida wa BBC cewa: "Tun misalin ƙarfe ɗaya na dare muke jin karar harbe-harbe da kuma wasu abubuwan fashewa."
Wani mutum na biyu kuma ya ce ya ji karar harbe-harben lokacin da ya tashi sallar asuba.
"Har ma mun yi addu'a a masallaci domin neman wa ƙasar zaman lafiya. Samari sun fito ƙofar gida suna tattaunawa kan abin da ke faruwa. Yawancin mutane na cewa 'yan ta'adda ne," in ji shi.
Mazauna birnin sun ce har zuwa wayewar gari ana ci gaba da jin harbe-harbe a wasu sassan Yamai.
Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motocin yaƙi masu sulke da aka tura domin ƙarfafa tsaro a yankunan da ke kusa da filin jirgin saman birnin.
Wata majiyar tsaro ta kuma shaida wa Reuters cewa jami'an tsaron Nijar sun yi galaba kan waɗanda suka kai harin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun tsere.
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, inda suka hambarar da gwamnatin da aka zaɓa ta Mohamed Bazoum, Nijar ke fuskantar ƙalubalen tsaro daga ƙungiyoyin mayaƙa masu alaƙa da Al-ƙa'ida da kuma IS.
Ƙasar mai arzikin ma'adanan yureniyom da danyen man fetur ta sauya akalar manufofinta na ƙetare bayan juyin mulkin, inda ta ƙarfafa alaƙa da Rasha tare da nisantar ƙasashen yamma.
Nijar da makwabtan ta Burkina Faso da Mali sun kuma fice daga ƙungiyar Ecowas tare da kafa Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES).
A baya, shugaban ƙasar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya zargi Faransa da hannu wajen ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, zargin da Paris ta musanta.
Me hukumomi suka ce?
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar (CNSP) ta wallafa wani gajeren sako a shafinta na sada zumunta da safe, inda ta ce ta tura jami'an tsaro domin shawo kan lamarin kuma ta bukaci mutane su kwantar da hankalinsu.
Sanarwar ta ce: "Mu kwantar da hankalinmu kuma a guji yada bayanan da babu tabbaci a kai.
"Dakarun kasarmu sun fita domin kare kare kasarmu.
"Mu kasance masu hada kai, mu kuma kiyaye tare da nuna goyon baya," a cewar sanarwar.
Hari mai kama da na baya?
A ranar 18 ga watan Yuni mahara sun kai wani mummunan hari kan babban filin jirgin kasar na Diori Hamani da birnin Yamai, sai dai dakarun kasar sun yi ikirarin dakile yunkurin.
Harin ya kasance shi ne na biyu a ƙasa da watanni 6 a filin jirgin na Yamai.
Domin a watan Janairun wannan shekara ma masu iƙirarin jihadi sun kai wani harin a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kaiwa.
A ranar 28 ga watan Janairun 2026 ɗin an samu harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin sama na Diori Hamani
Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato, yana mai cewa an shafe kusan sa'a guda ana jin ƙasar.
An jin ƙarar harbe-harben daga ƙofar shiga filin jirgin, kamar yadda wasu shaidu biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Jamhuriyar Nijar na fama da ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi da ke addabar sassan ƙasar kamar Boko Haram da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), mai alaƙa da Al-Qaeda.
A baya-bayan nan ne hukumomi a jamhuriyar ta Nijar suka ƙaddamar da wani aikin rushe gidaje fiye da 26,000 da ke kusa da filin jirgin saman na Diori Hammani da ke birnin Niamey.
Hukumomin dai sun ce sun ƙudiri niyyar rushe gidajen ne bisa dalilan tsaro, wani al'amari da ya janyo tankiya tsakaninsu da ƴan ƙasar musamman mutanen da abin ya shafa.