Hanyoyi 6 da ƴanbindiga ke kashe kuɗaɗen da suke karɓa

    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa na daga cikin manyan hanyoyin da 'yanbindiga ke samun kuɗaɗen gudanar da ayyukansu.

A Najeriya, ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, ciki har da Boko Haram ma na da wasu hanyoyin samun kuɗaɗe, inda suke tara biliyoyin nairori ko miliyoyin daloli daga mutanen da suke karɓa, galibi ta hanyar karɓar kuɗin fansa a tsabar kuɗi.

Wani sabon rahoto da ƙungiyar SBM Intelligence na nazari kan al'amuran tsaro a duniya ta fitar ya yi ƙiyasin cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi kimanin dala miliyan 5.8 a matsayin kuɗin fansa tsakanin watan Yulin 2025 da Yulin 2026.

Rahoton ya ce an sace mutane 7,825 a cikin wannan lokaci.

Amma abin tambayar shi ne, ta yaya waɗannan ƙungiyoyin ke kashe kuɗaɗen da suka amsa?

Wace ƙungiya ce ta fi karɓar kuɗin fansar?

Rahoton na SBM Intelligence ya ce ,ƙungiyar Boko Haram da ke ayyukanta a yankin arewa maso gabashin ƙasar ce kan gaba wajen karɓar kuɗin fansar.

''Boko Haram ce ta karbi kashi 90 na waɗannan kuɗaɗe a yankin arewa maso gabashi'', in ji rahoton.

SBM ta yi ƙiyasin cewa ƙungiyar Boko Haram, ta karɓi kusan naira biliyan bakwai , daga garkuwa da mutane da suka yi sau biyu, inda a kowane suka sace fiye da mutum 300.

Rahoton ya kuma ta kuma alaƙanta ƙungiyar ta Boko Haram da sace ɗaliban makarantar Papiri da ke jihar Neja a watan Nuwamban bara.

"An sake samun ƙaruwar sace ɗalibai daga makarantu, inda harin Papiri ya sake nuna yadda illolin hakan ke shafar ilimi da noma da kuma amincewar jama'a ga hukumomi," a cewar rahoton na SBM.

Baya ga Boko Haram, ƙungiyoyin ƴnbindiga da ke ayyukansu a yankin arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya ne ke matsayi na biyu wajen karɓar kuɗin fansa.

Sai dai rahoton bai bayyana adadin kuɗaɗen da ƙungiyoyin suka karɓa ba.

Hanyoyin da ƴan bindiga ke kashe kuɗaɗen da suka amsa

Masu bincike sun yi nuni da cewa karɓar kuɗin fansar na bai wa ƴanbindigar damar sayen makamai da ɗaukar sabbin mambobi da faɗaɗa ayyukansu, lamarin da ke ƙara dagula ƙoƙarin magance matsalar rashin tsaro.

Ga wasu hanyoyi biyar da irin waɗannan ƙungiyoyi ke bi wajen kashe kuɗaɗen da suka karɓa daga hannun mutane, kamar yadda Barista Audu Bulama Bukarti mai bincike kan sha'anin tsaro a nahiyar Afrika ya yi wa BBC bayani.

1. Amfani da Infoma

Waɗanda ake kira "ƴan infoma", wato masu shiga tsakani ko kwaramata wa ƴanbindiga bayanai da sauran mutane, na taka muhimmiyar rawa.

Barista Audu Bulama Bukarti, masanin harkokin tsaro, ya ce aikin ƴan infoma bai tsaya kawai wajen bai wa ƴan bindiga bayanai ba. A cewarsa, suna kuma shiga tsakani wajen karɓo kuɗin fansa idan lokacin biyan kuɗin ya yi.

Ya ce a wasu lokuta, ƴan bindiga kan karɓi kuɗin fansa ta hannun mutanen da ake gani kamar ƴan kasuwa ne, waɗanda suke shiga tsakaninsu da iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su.

A cewar Bukarti, wasu daga cikin waɗannan ƴan infoma kan shiga dazukan da ƴanbindiga ke ɓuya domin kai musu ko karɓo kuɗaɗen fansa, musamman cikin dare, sannan su dawo cikin gari kamar waɗanda suka je wani gari domin harkar kasuwanci.

Daga nan, a cewarsa, "wasu daga cikinsu kan yi amfani da kuɗin wajen sayen abubuwan da ƴan bindigar ke buƙata, kamar babura da man fetur."

"Sukan kuma yi amfani da masu ƙananan sana'o'i, musamman mata, domin su riƙa sayen abubuwa a hankali suna kai musu cikin daji," in ji Bukarti.

Wannan hanya na bai wa 'yan bindiga damar samun kayayyakin da suke buƙata ba tare da sun fito fili zuwa kasuwa ba.

2. Ƴan canji

Wata hanyar da ƴan bindiga ke amfani da ita wajen ɓoye inda kuɗaɗen fansa suka fito ita ce ta ƴan canjin kuɗaɗe.

Barista Bukarti ya ce idan ƴan bindigar sun karɓi kuɗin fansa a naira, sukan kai kuɗin wajen wasu ƴan canji domin a mayar da su zuwa dala ko Sefa, musamman ta hannun waɗanda ba sa bin ƙa'idojin da suka dace wajen gudanar da harkar canjin kuɗaɗe.

A cewarsa, hakan na taimaka musu wajen ɓoye daga inda kuɗaɗen suka fit, domin daga baya idan suna son amfani da kuɗin a Najeriya, za su iya canza su a matsayin dala maimakon naira.

"Ka ga daga nan sun ɓadda sahun kuɗaɗen, sannan idan suna so su yi amfani da su a Najeriya ne ka ga suna da dala ne," in ji Bukarti.

Ya ce idan kuma ƴan bindigar na son amfani da kuɗin a wata ƙasa, za su iya fitar da shi daga Najeriya zuwa ƙasashen da ake amfani da CFA, lamarin da ke ƙara wahalar da aikin hukumomi na gano inda kuɗaɗen suka fito da kuma yadda aka tura su.

3. Masu PoS

A wasu lokutan kuma, idan ƴanbindiga ba sa son karɓar kuɗin fansa a matsayin tsabar kuɗi, sukan buƙaci a tura musu kuɗin ta asusun banki.

Sai dai Barista Bulama Bukarti ya ce a irin wannan yanayin, ƴan bindigar kan yi amfani da masu cire kuɗi ta a bakin hanya da aka fi sani da POS, ta yadda za a ƙara wahalar iya bin diddigin kuɗin.

Ya ce galibi suna tura kuɗin ne zuwa lambar asusun mai POS, wanda wataƙila shi ba lallai ya san cewa kuɗin fansa ne ko kuma kuɗin ƴan bindiga ba.

"Yawanci lambar mai POS suke turawa, idan misali ƴan bindigar da ke Sakkwato suka tura kuɗin zuwa wajen mai POS da ke jihar Neja", a cewarsa, hakan iya ɗaukar lokaci kafin hukumomi su gano ainihin inda kuɗin ya fito da kuma waɗanda suke da hannu a harkar.

4. Sayen makamai

Barista Bulama Bukarti ya ce a wasu lokutan ƴan bindiga kan kashe kuɗaɗen da suka karɓa ta hanyar sayen makamai amma ba kai tsaye ba. Ya ce masu shiga tsakaninsu ne kan taimaka wajen kai kuɗin ga masu sayar da makamai, musamman ta hannun mutanen da suke cikin gari ko wani yaronsu.

"A wasu lokuta, idan mai shiga tsakani ya karɓi kuɗin fansa, zai iya kai kuɗin ga dillalan makamai ta hannun wani mutum da yake aiki da shi a cikin gari, ko kuma a tura kuɗin zuwa wajen mai sayar da makaman idan yana wajen Najeriya," in ji shi.

"Daga nan su kuma za a tura musu makamansu".

Ya ce a wasu lokutan ma, ƴan bindigar ba sa neman a ba su kuɗin fansa kai tsaye. Maimakon haka, sukan umarci dangin wanda aka yi garkuwa da shi da su sayo musu babura ko wasu kayan da suke buƙata, sannan su kai musu.

5. Kirifto da manhajojin canza kuɗi ta intanet

A wasu lokutan kuma, ƴanbindiga kan yi amfani da manhajojin canza kuɗi ta intanet wajen sarrafa kuɗaɗen fansa da suka karɓa.

Barista Bukarti ya ce a wasu lokutan har sukan mayar da kuɗaɗen zuwa kirifto, domin ɓoye inda kuɗin suka fito da kuma ƙara wahalar da hukumomi wajen bin diddiginsu.

"Amma yawanci ƴan Boko Haram da ISWAP ne ke irin wannan, ba ƴan bindiga ba," in ji Bukarti.

Ya ƙara da cewa a wasu lokutan ma kuɗaɗen da ake tura wa waɗannan ƙungiyoyi daga wajen Najeriya ana amfani da kirifto ne wajen aika su, domin a rage yiwuwar gano tushen kuɗin da kuma inda aka tura su.

6. Amfani da mata

Wata hanyar da ƴanbindiga ke amfani da ita wajen kashe kuɗaɗen da suka karɓa ita ce ta wasu mata masu ƙananan sana'o'i.

A wasu lokutan, sukan tura kuɗaɗen a hankali-a-hankali zuwa asusun waɗannan mata, saboda ba kasafai ake zargin mata da hannu a irin wannan harkar ba.

Idan kuma suna buƙatar wasu kayayyaki, sukan aika kuɗin ko kuma su nemi matan su saya musu abubuwan da suke buƙata, ta yadda za a iya kai musu kayan cikin sauƙi ba tare da jawo hankalin hukumomi ba.