An ji ƙarar harbe-harbe a babban birnin Jamhuriyar Nijar

Sojojin Nijar

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

An shafe dare ana jin karar harbe-harbe da fashe-fashe a sassa daban-daban na Yamai babban birnin Nijar.

Wasu mazauna birnin sun ce sun ji karar harbe-harbe a kusa kusa da filin jirgin sama na Diori Hamani da kuma fadar shugaban ƙasa da kuma sansanin soji na 101.

Babu dai tabbas kan asalin inda ake harbe harben, kuma babu wata sanarwa a hukumance.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ambato wasu majiyoyin tsaro a ƙasar na cewa mahara ne suka kawo hari a filin jirgin saman Yamai da kuma ƙoƙarin kutsawa fadar shugaban ƙasa.

Wani mazauni Yamai ya shaida wa BBC cewa “tun misalin karfe ɗaya na dare muke jin karar harbe-harben da karar wasu abubuwan fashewa”.

Wani mutum na biyu da BBC ta yi magana da shi ya ce: ”Na ji karar harbe-harben ne lokacin da na tashi sallar asuba, har ma mun yi addu’a a masallaci domin nema wa kasar zaman lafiya.

“Samari sun fito sun tsattsaya a kofar gida suna tattaunawa kan abin da ke faruwa. Yawancin mutane na cewa ‘yan ta’adda ne,” a cewar mazaunin na birnin Yamai wanda bai so a bayyana sunansa ba.

Ya ce ana harbe-harbe ne a wani sansanin soji a Yamai da ke kusa da filin jirgin saman kasar.

Wasu sun ce sun ji karar harbi kusa da fadar shugaban kasa da kuma kusa da kafar talabijin din kasar da wasu sassa na Yamai.

Mazauna birnin sun ce har zuwa wayewar gari sun ci gaba da jin karar harbe-harbe a sassan birnin.

Wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motocin yaki masu sulke da aka tura domin tabbatar da tsaro a unguwanin da ke kusa da filin jirgin saman birnin Yamai.

Sai dai wata majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa jami'an tsaron Nijar sun yi galaba kan maharan kuma suna gudanar da bincike a yanzu haka.

Ya kara da cewa wasu daga cikin maharan sun arce.

A 2023 ne sojoji suka kwace mulki a Nijar inda suka hambarar da gwamnatin da yan kasar suka zaba ta Mohamed Bazoum, kuma tun lokacin Nijar ke fama da hare-haren mayaka masu alaka da Al Qaeda da kuma IS.

Nijar kasa ce mai arzikin albarkatun kasa kamar ma'adanin yureniyom (uranium) da kuma danyen man fetur.

Juyin mulkin da aka samu ya sanya kasar ta raba gari da kasashen yamma yayin da ta mayar da hankali wajen karfafa alakar dangantaka da Rasha.

Nijar da sauran makwaftanta kamar Burkina Faso da Mali sun fita daga kungiyar kasashen yammacin Afirka ta Ecowas, inda suka samar da kungiyar kasashen yankin Sahel ta AES.

A baya shugaban kasar Abdourahamane Tiani ya dora alhakin hare-haren da ake kaiwa a cikin kasar kan Faransa, kasar da ta yi wa Nijar din mulkin mallaka, kuma daya daga cikin kasashen da gwamnatin mulkin sojin ta kora tun bayan kama mulki.

Hari mai kama da na baya?

A ranar 18 ga watan Yuni mahara sun kai wani mummunan hari kan babban filin jirgin kasar na Diori Hamani da birnin Yamai, sai dai dakarun kasar sun yi ikirarin dakile yunkurin.

Harin ya kasance shi ne na biyu a ƙasa da watanni 6 a filin jirgin na Yamai.

Domin a watan Janairun wannan shekara ma masu iƙirarin jihadi sun kai wani harin a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kaiwa.

A ranar 28 ga watan Janairun 2026 ɗin an samu harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin sama na Diori Hamani

Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato, yana mai cewa an shafe kusan sa'a guda ana jin ƙasar.

An jin ƙarar harbe-harben daga ƙofar shiga filin jirgin, kamar yadda wasu shaidu biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Jamhuriyar Nijar na fama da ƙungiyoyi masu iƙrarin jihadi da ke addabar sassan ƙasar kamar Boko Haram da ƙungiyar Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), mai alaƙa da Al-Qaeda.

A baya-bayan nan ne hukumomi a jamhuriyar ta Nijar suka ƙaddamar da wani aikin rushe gidaje fiye da 26,000 da ke kusa da filin jirgin saman na Diori Hammani da ke birnin Niamey.

Hukumomin dai sun ce sun ƙudiri niyyar rushe gidajen ne bisa dalilan tsaro, wani al'amari da ya janyo tankiya tsakaninsu da ƴan ƙasar musamman mutanen da abin ya shafa.