Yadda ƴanbindiga suka karɓi fiye da naira biliyan 7 kuɗin fansa a Najeriya

Jakar Ghana Must Go

Asalin hoton, Twitter

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa ta zama hanyar samun manyan kuɗaɗe da ƙungiyoyin ƴanbindiga ke amfani da su a Najeriya, lamarin da ke shafar al'ummomi a yankuna daban-daban na ƙasar.

Duk da ci gaba da ayyukan jami'an tsaro, ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai na ci gaba da sace mutane tare da neman makudan kuɗaɗen fansa daga iyalan da ke neman hanyar kuɓutar da 'yan uwansu.

Wani sabon rahoto da ƙungiyar SBM Intelligence na nazari kan al'amuran tsaro a duniya ta fitar ya yi ƙiyasin cewa masu garkuwa da mutane sun karɓi kimanin dala miliyan 5.8 a matsayin kuɗin fansa tsakanin watan Yulin 2025 da Yulin 2026.

Rahoton ya nuna girman matsalar da kuma yadda kuɗin fansa ke ci gaba da zama abin da ke ƙarfafa aikata wannan laifi.

Masu binciken sun yi nuni da cewa karɓar kuɗin fansar na bai wa ƴanbindigar damar sayen makamai da ɗaukar sabbin mambobi da faɗaɗa ayyukansu, lamarin da ke ƙara dagula ƙoƙarin magance matsalar rashin tsaro.

Da gaske ana biyan kuɗin fansa a Najeriya?

Tarin kuɗi

Asalin hoton, EFCC

Dr Kabiru Adamu, Shugaban Kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited mai nazarin harkokin tsaro a yankin Sahel duk da cewa a hukumance gwamnatin Najeriya ta haramta biyan kudin fansa, amma bisa ga bayanan da ake samu ana biyan kuɗin.

''A zahiri kowane ɗanƙasa ya san cewa ana biyan kuɗin fansa a Najeriya''.

Ya ce idan aka sace mutum a Najeriya hanya biyu ce ta kuɓutar da shi, ko dai a ƙwato shi da ƙarfi ko kuma a biya kudin fansa.

''To kuma a baya-bayan nan an fi amfani da hanyar biyan kuɗin fansar a duk lokacin da aka sace mutum'', in ji shi.

Gwamnati na biyan kuɗin fansa?

Buhunan kuɗi

Asalin hoton, EFCC

La'akari da yawan kuɗin da cibiyar SBM Intelligence ta fitar sun zarce tunanin cewa ɗaiɗaikun mutane ne suka biya wannan kuɗi.

Cibiyar ta ce kuɗin fansar da aka biya lokacin sace mutane masu yawa a jihar Borno ne kan gaba a yawan adadin da aka samu na biyan kuɗin fansa.

Dr Kabiru Adamu ya ce idan ka duba duka lokutan biyu da aka kuɓutar da mutanen masu yawa na jihar Borno, gwamnati ce ta ce ta kuɓutar da mutanen, don haka akwai yiwuwar biyan kuɗin fansar.

''Duk da yake gwamnati na musanta biyan kuɗin fansa, amma bisa ga bayanan wannan cibiyar ta SMB Intelligence, gwamnati na biyan kuɗin fansa, duk da yake ba ta fito da hujjojin hakan a rahoton nata ba'', in ji shi.

Wace ƙungiya ce ta fi karɓar kuɗin fansar?

Boko Haram

Asalin hoton, Others

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahoton na SBM Intelligence ya ce ,ƙungiyar Boko Haram da ke ayyukanta a yankin arewa maso gabashin ƙasar ce kan gaba wajen karɓar kuɗin fansar.

''Boko Haram ce ta karbi kashi 90 na waɗannan kuɗaɗe a yankin arewa maso gabashi'', in ji rahoton.

SBM ta yi ƙiyasin cewa ƙungiyar Boko Haram, ta karɓi kusan naira biliyan bakwai , daga garkuwa da mutane da suka yi sau biyu, inda a kowane suka sace fiye da mutum 300.

Rahoton ya kuma ta kuma alaƙanta ƙungiyar ta Boko Haram da sace ɗaliban makarantar Papiri da ke jihar Neja a watan Nuwamban bara.

"An sake samun ƙaruwar sace ɗalibai daga makarantu, inda harin Papiri ya sake nuna yadda illolin hakan ke shafar ilimi da noma da kuma amincewar jama'a ga hukumomi," a cewar rahoton na SBM.

Baya ga Boko Haram, ƙungiyoyin ƴnbindiga da ke ayyukansu a yankin arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya ne ke matsayi na biyu wajen karɓar kuɗin fansa.

Sai dai rahoton bai bayyana adadin kuɗaɗen da ƙungiyoyin suka karɓa ba.

Dr Kabiru Adamu ya ce dalilin da ya sa ƙungiyar Boko Haram ta fi sauran ƙungiyoyin karɓar kudin fansa shi ne yadda take sace mutane masu yawa a lokaci guda fiye da sauran ƙungiyoyin ƴanbindiga a ƙasar.

Mutum nawa aka sace?

wani ɗanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar SBM Intelligence ta Najeriya ta ce an yi garkuwa da mutane 7,825 tsakanin watan Yulin 2025 da Yunin 2026, wanda ya nuna ƙaruwa da kashi 66 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

''Aƙalla mutum 1,142 ne suka rasa rayukansu a wannan lokaci, yayin da adadin kuɗaɗen fansar da aka tabbatar an biya ya ninka fiye da sau uku'', in ji rahoton

SBM Intelligence ta ce ta tattara waɗannan alƙaluma ne daga rahotannin kafafen yaɗa labarai da tattaunawa da mutane daban-daban, da kuma bayanan da ta samu daga jama'a.

Sai dai SBM ta ce waɗannan alƙaluma na iya kasancewa sama da ainihin adadin, saboda yawancin kuɗaɗen fansar da ake biya ba a bayyana su ga jama'a ba.

Za a iya hana ƙungiyoyin karɓar kuɗin fansa?

Ƴanbindiga

Asalin hoton, Getty Images

Bisa dokokin Najeriya babban laifi ne biyan kuɗin fansa.

SBM Intelligence ta ce yana da kyau hukumomin ƙasar su tsara yadda za a kawar da wannan matsala.

"Idan ba a tsara wata haɗaɗɗiyar dabarar da za ta hana waɗannan ƙungiyoyi aikata wannan laifi ba tare da magance tushen matsalar, Najeriya na fuskantar barazanar mayar da garkuwa da mutane wata muhimmiyar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga ƙungiyoyin da suka fi barazana ga zaman lafiyar ƙasar," in ji SBM.

A nasa ɓangare Dr Kabiru Adamu ya ce hanyar kawai da a bi don hana biyan kuɗin fansa ita ce a hana sace mutane.

''Idan har za a bari a sace mutane to babu wata mafita sai guda biyu, kodai amfani da ƙarfi ko kuma biyan kuɗin fansa'', in ji shi.

Sai dai ya gargaɗin cewa amfani da ƙarfin na da hatsarin da zai iya kai wa ga yi wa wanda aka sace lahani ko ma kisasa.

''Wani abu kuma shi ne muna fuskantar ƙarancin jami'an tsaron da za su iya kuɓutar da mutanen da aka sace'',.

Ya ce a matsayinsa na masanin tsaro ba ya goyon bayan biyan kuɗin fansa, to amma abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne hana ƴanbindigar sace mutane, domin idan har ana sace mutane to dole ƴan'uwansa su biya kuɗin fansa.

Masanin tsaron ya ce yana da kyau gwamnati ta tashi tsaye wajen hana garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta kowane hali.