Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/8/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 29 ga watan Agustan 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Rediyo da talabijin na Nijar sun koma aiki bayan katsewa na dan lokaci

    Mazauna birnin Niamey sun shaida wa BBC cewa gidajen rediyo da talabijin na gwamnatin Nijar sun koma bakin aiki bayan katsewar dan lokaci.

    Rahotanni sun ce kafafen sun koma aiki da misalin karfe 10:30 na safe agogon ƙasar, bayan sun katse shirye-shiryensu da misalin karfe 9:00 na safe.

    Katsewar ta zo ne a daidai lokacin da aka ruwaito karar harbe-harbe da fashe-fashe a wasu sassan Niamey, ciki har da yankin filin jirgin sama na Diori Hamani, wani sansanin soja da kuma kusa da fadar shugaban ƙasa.

    Mahukuntan Nijar sun yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu, amma har yanzu ba su yi karin bayani kan abin da ya faru ba.

  2. Iran ta musanta iƙirarin Trump kan buɗe mashigar Hormuz

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta musanta kalaman shugaban Amurka Donald Trump cewa mashigar Hormuz tana a buɗe, suna masu cewa har yanzu ba a bar jiragen ruwa su ratsa ba tare da amincewar hukumomin Iran ba.

    Rundunar ta bayyana kalaman jami'an Amurka a matsayin "ƙarya ƙarara", tana mai cewa an yi su ne domin tasiri kan farashin man fetur da kuma ɓoye abin da ta kira gazawar Amurka.

    IRGC ta kuma yi iƙirarin cewa har yanzu ita ce ke da cikakken iko kan mashigar Hormuz, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da aiwatar da wannan mataki har sai an kawo ƙarshen ayyukan sojin Amurka kan Iran da kuma cika sharudan da Tehran ke nema.

  3. Gwamnatin Kwara ta haɗa mutum 146 da aka sace a Woro da iyalansu

    Gwamnatin Jihar Kwara ta sanar da cewa ta haɗa mutum 146 da aka sace daga ƙauyen Woro da iyalansu bayan sun shafe kwanaki 21 a cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa da farfaɗo da su daga abin da suka fuskanta.

    An kai hari ƙauyen Woro ne a ranar 3 ga Fabrairu, inda aka yi garkuwa da mutum 146, kafin daga bisani aka kuɓutar da su a ranar 5 ga Agusta.

    Gwamnatin jihar ta kuma ba waɗanda aka kuɓutar tallafin kuɗi, inda manya suka samu naira miliyan ɗaya kowannensu, matasa naira dubu 500,000, yayin da yara suka samu naira dubu 200,000 domin taimaka musu su fara rayuwa ta sabo.

    Shugaban ƙaramar hukumar Kaiama, Abubakar Abdullahi Danladi, ya yaba wa Shugaba Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan rawar da suka taka wajen ceto da kuma kula da waɗanda aka sace.

    Sai dai shugaban kwamitin da ke hulɗa tsakanin gwamnati da al'ummar Woro, Ahmed Ibn Ahmed, ya ce har yanzu mutum 13 na hannun masu garkuwa da mutane, tare da kira ga gwamnati ta ƙara ƙoƙari domin ceto su.

  4. Muna buƙatar haɗin kan al'ummar Iran - Mojtaba Khamenei

    Jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei, a wani saƙo da aka danganta da shi, ya jaddada goyon baya ga gwamnatin Shugaban kasar, Massoud Pezeshkian tare da kira ga haɗin kan al'umma da kauce wa duk wani abu da zai haddasa rarrabuwar kawuna.

    Bayan saƙon ne kuma wasu manyan jami'an Iran suka sake jaddada kira da a ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

    Mohsen Rezaei, sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa, ya ce haɗin kan al'umma na daga cikin muhimman ginshiƙan ƙarfi da tsaron ƙasa.

    Shi ma shugaban majalisar dokoki, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce ya kamata jami'ai su guji duk wani abu da zai haifar da sabani a tsakanin al'umma, yana mai cewa duk wani aiki da zai raunana haɗin kai bai dace ba.

    Ministan Al'adu, Abbas Salehi, ya ce saƙon ya nuna cikakken goyon baya ga shugaban ƙasar, tare da rage damar masu son haddasa rarrabuwar kawuna ta siyasa, al'adu ko zamantakewa.

  5. Iran ta ce za ta kai hari kan dukkan wuraren Amurka idan yaƙi ya ci gaba

    Iran ta yi gargaɗin cewa za ta kai hare-hare kan dukkan sansanonin soja da sauran wuraren Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya idan yaƙin da ake yi ya ci gaba.

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce Tehran ta riga ta sanar da ƙasashen yankin cewa duk wani hari da Amurka ta kai wa Iran zai fuskanci martani kai tsaye kan muradun Amurka a yankin.

    Ya kuma bayyana hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai Iran ba bisa ka'ida bane, yayin da ya ce Iran za ta mayar da martani ne domin kare kanta.

    Araqchi ya ce makamai masu linzamin Iran sun nuna ƙarfinsu a yaƙin baya-bayan nan, yana mai iƙirarin cewa Amurka da Isra'ila sun kasa dakile su yadda ya kamata.

    Haka kuma ya ce Iran na son inganta dangantaka da ƙasashen Musulmi da maƙwabtanta, ciki har da Masar da Lebanon.

  6. Amurka ta samu iko da fiye da rabin man fetur ɗin Venezuela - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa Amurka ta samu iko da fiye da rabin arzikin man fetur na Venezuela, yana mai cewa hakan ya ƙarfafa tasirin Washington a fannin makamashi a yankin.

    Trump ya bayyana haka ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan manufofin makamashi da dangantakar Amurka da ƙasashen Latin Amurka.

    Sai dai bai yi cikakken bayani kan yadda Amurka ta samu wannan iko ba.

    Venezuela na ɗaya daga cikin kasashen masu manyan arzikin man fetur a duniya, kuma albarkatun makamashinta na ci gaba da kasancewa muhimmin batu a siyasa da tattalin arzikin duniya.

  7. Iran ta ce tana da wadataccen mai da zai samar mata kuɗaɗen kasafi

    Iran ta ce tana da isasshen man fetur da za ta sayar domin samar da kuɗaɗen da ake buƙata a kasafin kuɗinta duk da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ta yi kamar yadda kamfanin dillanacin labaran Fars ya ruwaito.

    Fars ya ce ma’aikatar man tetur ta ƙasar ta ce kuɗaɗen da aka samu daga man fetur a watanni huɗun farko na shekarar nan sun kai kashi 99 cikin 100 na abin da aka tsara a kasafin kuɗi.

    Haka kuma, ma’aikatar ta ce ta tura dala biliyan 7.5 da aka samu daga sayar da man fetur zuwa Babban Bankin Iran a cikin watanni huɗun farko na shekarar, kuma ana sa ran kuɗaɗen za su taimaka wajen biyan buƙatun kuɗaɗen musayar ƙasashen waje na gwamnati daga watan Afrilu zuwa Janairu.

  8. Assalamu alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance da ku daga yanzu zuwa yamma.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.