Abin da ya sa kamfanin sufuri na Uber ya bar Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kamfanin sufurin motocin haya ta manhajar intanet, Uber, ya sanar da cewa zai daina gudanar da ayyukansa a Najeriya bayan kusan shekara 12 da fara aiki a faɗin ƙasar.

Kamfanin ya ce ya yanke wannan shawara ce, wadda ya bayyana da mataki "mai matuƙar nauyin ɗauka", amma ya ce ya zama dole ne saboda "wasu muhimman manufofinsa na kasuwanci".

An shafe wani lokaci ana yaɗa jita-jita a shafukan sada zumunta cewa Uber zai fice daga Najeriya, lamarin da ya sa BBC ta tuntuɓi kamfanin da wasu daga cikin abokan hulɗarsa, waɗanda suka tabbatar da batun.

Kamfanin ya tabbatar da cewa zai rufe ayyukansa a Najeriya, kuma masu amfani da manhajarsa ba za su ƙara samun damar amfani da ayyukansa da zarar ya rufe ayyukan baki ɗaya.

"Mun ɗauki wannan matakin na daina aiki ne Najeriya da Uganda. Su kaɗai ne ƙasashen da za mu daina aiki, amma matakin ba zai shafi ayyukan kamfaninm Uber ba a sauran ƙasashen Afirka."

Tuni wasu waɗanda suke amfani da motocin kamfanin suka bayyana rashin daɗinsu kan ficewar kamfanin daga Najeriya, inda suke cewa sun fi ji daɗin Uber, saboda a cewarsu farashinsu ya fi sauƙi.

Ayyukan Uber a Najeriya

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce zai dakatar da ayyukansa daga ranar 2 ga Satumba, 2026, wato jiya Laraba ke nan.

"Uber na sanar da cewa zai daina gudanar da ayyukansa a Najeriya da Uganda daga ranar 2 ga Satumba, 2026, bayan wani nazari kan sauye-sauyen manufofinsa na kasuwanci da tsarin zuba jari a faɗin Afirka."

Wasu daga cikin masu amfani da Uber a Najeriya sun ce sun samu saƙonnin imel daga kamfanin da ke sanar da su game da rufe ayyukan.

Kamfanin ya ce cibiyar bayar da taimako ga masu amfani da ayyukansa za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 24 ga Satumba domin amsa tambayoyi da warware wasu matsalolin da suka shafi rufe ayyukan.

"Har yanzu muna da cikakken ƙudurin ci gaba da kasancewa a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, inda muke ci gaba da ganin ci gaba mai kyau da damarmaki masu yawa."

"Za mu fi mayar da hankalinmu da jarinmu kan ƙasashen da muka yi imanin za mu fi samar da amfani ga direbobinmu, ta hanyar ba su damar samun kuɗin shiga a mataki mai girma tare da bai wa fasinjoji damar yin zirga-zirga cikin sauƙi da nishaɗi," in ji sanarwar.

Uber ya fara aiki a Najeriya ne tun a shekarar 2014, kuma daga baya ta faɗaɗa ayyukansa fiye da samar da motocin haya.

A Legas, kamfanin ya fara samar da ayyukan safarar ruwa a shekarar 2019, inda ya ce an ƙirƙiro wannan tsari ne domin taimakawa wajen rage cunkoson ababen hawa a birnin.

Kasuwar Najeriya ta kasance mai ƙalubale ga kamfanonin motocin haya ta manhajar intanet, inda direbobi suka sha gudanar da zanga-zanga a lokuta daban-daban cikin ƴan shekarun nan saboda ƙarancin kudin hawa da kuma yanayin aikin da suka ce ba su yi daidai ba.

Ƙungiyoyin da ke wakiltar direbobi sun buƙaci a ƙara kuɗin hawa, a rage kaso ko kuɗin da kamfanoni ke karɓa, sannan suka buƙaci a samar da ingantacciyar kariya ga direbobi.

Me ya sa Uber ke barin Najeriya?

Uber ya bayyana cewa wannan shawara ta shafi kasuwanninsa na Najeriya da Uganda ne kawai, kuma matakin ba zai shafi tasiri kan ayyukan kamfanin a sauran ƙasashen Afirka ba.

Kamfanin ya bayyana dalilin da ya sa yake ficewa daga Najeriya bayan kusan shekara 12 da gudanar da ayyuka a kasar.

Uber ya ce shawarar ta samo asali ne daga sauye-sauyen manufofinsa na kasuwanci da kuma inda yake son mayar da hankalinsa wajen zuba jari.

"Bayan dogon nazari, mun yanke shawara mai matuƙar wahala ta dakatar da ayyukanmu a Najeriya da Uganda a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen manufofin kasuwancinmu da tsarin zuba jari a faɗin nahiyar."

Kamfanin ya ce zai mayar da hankali wajen zuba jari a wuraren da yake ganin zai iya samar da mafi yawan amfani ga direbobinsa, domin su samu damar samun kuɗin shiga mai kyau.

Uber ya ce matakin da ya ɗauka har ya kai ga daina ayyukansa a Najeriya ba su da alaƙa da umarnin da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya, FAAN, ta bayar kwanan nan dangane da ayyukan motocin haya ta manhajar intanet a filayen jiragen sama na kasar.

Me zai faru da direbobin Uber?

Uber na da ma'aikata da dama a Najeriya, sannan yana da abokan hulɗa da yake gudanar da kasuwanci tare da su.

BBC ta tambayi kamfanin yadda rufe ayyukansa zai shafi ma'aikata, direbobi da kuma waɗanda ke dogaro da Uber wajen samun damar aiki.

"Muna ci gaba da tattaunawa kai tsaye cikin kulawa da waɗanda abin ya shafa, ciki har da ma'aikata, direbobi da fasinjoji, kan abin da wannan matakin zai haifar a gare su," in ji kamfanin.

Ko da yake wasu daga cikin masu amfani da Uber sun riga sun samu saƙonnin imel kan batun, kamfanin ya ce zai ci gaba da tallafa wa ma'aikatan da rufe ayyukan zai shafa.

"Mun kuɗuri aniyar tallafa wa ma'aikatan da abin ya shafa yayin wannan sauyi, kuma za mu tuntuɓe su kai tsaye kan shirye-shiryen da suka shafe su."