Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alamomin cutar mashaƙo da ake fama da ita a Kano da Katsina
A Najeriya musamman wasu jihohin arewacin ƙasar ana samun ɓarkewar cutar mashaƙo wadda ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60.
Sai dai hukumar da ke daƙile cutuka masu bazuwa ta Najeriya, NCDC ta tabbatar da kamuwar mutum fiye da 10,000.
Jihohin Kano da Katsina da Plateau na ta faman kiraye-kiraye ga al'ummarsu da su yi dafifi wajen karɓar alllurar rigakafi da gwamnatin tarayya ta kai musu duk da cewa jihohin na ƙorafin rigakafin sun yi kaɗan.
Shin mece ce cutar ta Mashaƙo kuma waɗanne ne alamominta da za ku gani domin kiyayewa?
Mece ce mashaƙo
Yadda cutar ke kama mutum
Tsohon shugaban hukumar yaki da cutuka masu yaɗuwa ta Najeriyar Farfesa Abdussalam Nasidi, ya shaida wa BBC cewa cutar mashaƙo, na kama maƙogoro ne, tare da hana mutum sakat.
Ya ce: ''Idan ta kama mutum za ta riƙe masa wuya kamar an shaƙe ka, idan ta kama yaro idan ba Allah ne ya kiyaye ba a gaban iyayensa za a rasa shi, don haka babbar barazana ce''.
"Cutar mashako dai wata cuta ce da ke kama yara waɗanda suka kai shekara biyar da kuma manya da suka haura shekara 60. Tana kama garkuwar jikin ɗan adam ta yi mata mummunar illa.," in ji Dr Usman Bashir, likitan kula da lafiyar al'umma ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu da ke Kano kamar yadda ya shaida wa BBC a 2023.
Dr Usman ya ce an fi samunta a wuraren da ba a fiya yin alluran rigakafi ba.
Likitan ya ce cutar tana saurin kisa saboda ba a gane ta da wuri idan an kamu, kuma a mafi yawan lokuta sai ta kai ga yaro ya fara numfashi cikin wahala, ko kumaya gaza cin abinci ko ya kamu da zazzabi mai tsanani ko kuma yawan tari.
Ya ce cutar na yaɗuwa ne ta hanyar zama cikin cunkoso a ɗaki ɗaya, musamman wanda aka rufe tagoginsa babu wajen shan iska da kuma waɗanda ba a yi wa allurar rigakafi ba wadda ke bayar da garkuwa ga kwayoyin halittar ɗan adam da ke yaƙar kwayoyin cutar.
Ya kuma ce tana ɗaya daga cikin cutukan yara da ke saurin kisa, sannan tafi tashi a lokacin sanyi.
Alamomin cutar mashaƙo
Dr Usman Bashir ya ce alamomin cutar na fara bayyana a jiki ne cikin kwanaki biyu zuwa biyar.
Ga dai wasu daga cikin alamomin cutar:
- Tari
- Zazzabi mai zafi
- Rashin cin abinci
- Kumburin cikin baki.
- Numfashi sama-sama
- Yoyon hanci
- Gajiya
Yadda za a kaucewa kamuwa da cutar mashaƙo
Likitan ya ce hanya ɗaya ta kaucewa kamuwa da cutar mashaƙo ga manya da ƙananan yara ita ce yin allurar rigakafi saboda za ta kashe ƙwayoyin cutar da ke jikin mutum.
Ya ce yana da muhimmanci a wayar da kan al'umma wajen yi wa yara allurar rigakafi domin hakan zai iya magance ta ba wai mashaƙo kaɗai ba har da cutar sarƙewar haƙora da ƙyanda da sauransu.