'An kashe mutum sama da 900 a Gaza a wannan shekarar'
Fiye da mutane 900 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a Gaza a wannan shekara duk da yarjejeniyar tsagaita wuta, a cewar sabbin alƙaluman da Ma’aikatar Lafiya ta Gaza mai alaƙa da Hamas ta fitar.
Hakan ya kai jimillar Falasɗinawan da aka kashe a Zirin Gaza tun bayan da aka ayyana tsagaita wuta a ranar 10 ga Oktoba zuwa sama da 1,300, ciki har da yara 301, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin.
Hamas da Isra’ila sun amince da dakatar da yaƙin bayan sun karɓi shirin zaman lafiya mai maki 20 na Shugaban Amurka Donald Trump.
Shirin ya haɗa da dakatar da dukkan ayyukan soji, ciki har da hare-haren sama da luguden wuta ta manyan bindigogi.
Tun daga lokacin, sashen BBC Verify ya yi nazarin bidiyo da dama da ke nuna illolin hare-haren Isra’ila a wurare daban-daban, ciki har da wani gidan shan shayi da ke bakin teku, tantunan da mutanen da suka rasa matsugunansu ke zaune, da kuma wani jerin gwanon jana’iza da aka ruwaito a tsakiyar Gaza.
Bayanan sun nuna cewa watannin baya-bayan nan sun kasance daga cikin mafi muni, inda aka rubuta mutuwar fiye da mutane 100 a kowane wata tsakanin Afrilu da Agusta.
Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta danganta waɗannan mace-macen kai tsaye ga hare-haren sojin Isra’ila, sai dai ba ta bambance tsakanin fararen hula da mayaƙa a cikin alƙaluman da take fitarwa ba.