Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 05/09/2026.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Mutum 60 sun rasu a arangamar yau a Yemen

    Arangamar da aka yi tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da Saudiyya ke goyon baya da kuma mayaƙan Houthi ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 60, kamar yadda majiyoyin lafiya da na soji suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Rahoton ya ce fararen hula ma na cikin waɗanda suka mutu.

    AFP ta ruwaito cewa dakarun gwamnati 26 sun mutu a cikin sa'o'i da dama na faɗa a yankin kudu maso yammacin Yemen.

    Majiyoyin lafiya da na soji na ƙungiyar Houthi, wadda Iran ke goyon baya, sun kuma ce an kashe mayaƙansu 31 a arangamar.

    Wata majiya daga ɓangaren lafiya a birnin Taiz, wanda ke ƙarƙashin ikon gwamnati, ta ce wani hari da makami mai linzami ya kai wa wata motar bas ya kashe fararen hula shida tare da raunata wasu bakwai.

    Ƙungiyar Houthi, wadda ke kiran kanta Ansar Allah, tana iko da wani babban yanki na arewaci da gaɓar tekun Yemen da ke kan Tekun Bahar Maliya, tare da babban birnin ƙasar, Sanaa.

    Kwamitin Shugabancin Yemen, wanda ƙasashen duniya suka amince da shi a matsayin gwamnatin ƙasar, na samun goyon bayan Saudiyya. Yana iko da gabashin Yemen da kuma gaɓar tekun kudancin kasar, ciki har da tashar jiragen ruwa ta Aden.

  2. Rasha ta dakatar da hare-hare a Ukraine na kwana uku saboda ziyarar wakilan Trump

    Fadar gwamnatin Rasha, Kremlin, ta ce Shugaba Vladimir Putin ya bayar da umarnin dakatar da kai hare-hare kan Kyiv na tsawon kwanaki uku, gabanin ziyarar da wakilan Shugaban Amurka Donald Trump za su kai babban birnin Ukraine domin tattauna batun kawo ƙarshen yaƙin.

    Masu tattaunawar, Steve Witkoff da surukin Mista Trump, Jared Kushner, suna Moscow a halin yanzu, inda ake sa ran za su gana da Shugaba Putin daga baya, a wani sabon yunƙurin da Donald Trump ke jagoranta na tabbatar da sulhu a tsakanin ƙasashen biyu.

    Mista Trump ya nuna a ranar Juma'a cewa suna da sabbin shawarwari na samar da zaman lafiya, amma bai bayyana cikakkun bayanai ba.

    Mista Kushner da Mista Witkoff sun ziyarci Rasha sau da dama, amma tattaunawar da za su yi da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky za ta kasance irinta ta farko da za su gudanar a cikin Ukraine.

  3. An gano "gawa a cikin akwati" ashe yar tsana ce mai kama da mutum

    Ƴan sandan Australia da aka kira domin bincike kan wata gawa da aka samu a cikin wani akwati sun kammala da cewa "gawar" a zahiri yar tsana ce mai kama da mutum.

    Mutane biyu ne suka gano akwatin a gefen hanya kusa da ƙaramar ƙauyen Oallen, mai nisan kusan kilomita 230 (mil 143) kudu-maso-yamma da Sydney.

    Ƴan sanda sun sanar da fara binciken kisan kai, lamarin da ya ja hankali matuƙa a kan batun, amma sa'o'i kaɗan bayan nan suka janye wannan matsaya, suka ce gwaje-gwajen kwararru ya tabbatar da cewa abin da ke cikin akwatin ba mutum ba ne.

  4. Nijar ta zargi Faransa ta kitsa juyin mulki a ƙasar

    Hukumomin Nijar sun zargi Faransa a hukumance da goyon bayan abin da suka bayyana a matsayin “yunkurin kawo hargitsa ƙasar a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta.”

    A cikin wata sanarwa, gwamnatin Nijar ta ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai, tana da “alaƙa da ƙasashen duniya”, tana mai cewa “an tattara ƙwararan shaidu masu yawa dangane da hari, kuma ana tunanin kai ƙarar gaban kotunan ƙasa da ƙasa.”

    Sanarwar ta kuma ce “Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ke jagorantar wata babbar kafa ta mutane da ƙungiyoyi da ke goyon bayan wannan aiki,” yayin da ta kuma yi zargin cewa wasu ƙasashen Afirka da ba a bayyana sunayensu ba sun taka rawa a matsayin masu shiga tsakani.

    Sai dai zuwa yanzu, gwamnatin Nijar ba ta gabatar da wata shaida da za ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.

    Sansanin sojin sama na 101, wanda aka kai wa hari a ranar 29 ga watan Agusta, wani ɓangare ne na rukunin filin jirgin saman Diori Hamani. A wurin ne ake ajiye jiragen yaƙin sojin Nijar da jirage marasa matuƙa, tare da wata rundunar yaƙi da ta'addanci ta ƙawancen ƙasashen Sahel.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, sojojin Rasha da na Italiya ma suna da sansani a wurin.

    Nijar ta ce baya ga Rasha, ta kuma samu taimako daga Aljeriya.

    Rasha ta tabbatar da cewa dakarunta sun taimaka wajen dakile abin da aka bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki da aka yi ranar Asabar a Nijar.

  5. 'Zanga-zangar da aka yi a Iran ta fi yaƙe-yaƙe ɗaga mana hankali'

    A wata hira da aka yi da mai magana da yawun gwamnatin Iran a gidan talabijin kan zanga-zangar hunturun da ya gabata, ta ce: “Hatta yaƙe-yaƙen guda biyu da muka fuskanta ba su kai zanga-zangar Janairu ba.”

    Da take bayyana abubuwan da suka faru a watan Janairu, Fatemeh Mohajerani ta ce: “Waɗannan kwanaki ne masu matuƙar wahala, irin waɗanda ban taɓa fuskanta a rayuwata ba,” inda ta jaddada cewa: “Kwanakin Janairu na 1404 su ne kwanakin da suka fi zama masu ɗaci a rayuwata.”

    Fatemeh Mohajerani ta ce a taron farko na majalisar ministocin Iran bayan zanga-zangar da aka gudanar a ranar 8 da 9 ga Janairu, ta tambayi Shugaba Masoud Pezeshkian cewa:

    “Saboda wasu dalilai da ban sani ba, kuma wataƙila bai kamata in sani ba, mun rasa ƴan’uwanmu da dama. Don Allah a ba da umarnin gudanar da bincike kan dalilin da ya sa aka samu tashin hankali mai yawa, da kuma abin da ya faru har ya kai ga al’umma wannan matsayi?”

    An bayyana murƙushe zanga-zangar watan Janairu cikin zubar da jini a matsayin mafi muni da aka taɓa samu a tarihin Iran na wannan zamani.

    Sai dai gwamnatin Iran ta bayyana zanga-zangar a matsayin “yunƙurin juyin mulki” da kuma wani shiri da “ƙasashen waje” suka shirya.

  6. Yau wakilan Trump za su gana da Rasha da Ukraine domin kawo ƙarshen yaƙi

    Ana sa ran nan gaba a yau jakadun shugaba Donald Trump, da suka hada da surukinsa Jared Kushner da kuma Steve Witkoff, za su isa birnin Moscow a wani sabon yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin da ake tsakanin Rasha da Ukraine.

    Mista Trump ya bayyana cewa wakilan nasa za su gabatar da sabbin shawarwari na zaman lafiya, sai dai bai yi cikakken bayani kan abin da shawarwarin suka ƙunsa ba.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce daga nan wakilan na Amurka za su ziyarci birnin Kyiv a gobe Lahadi, duk da cewa har yanzu Washington ba ta tabbatar da hakan ba. Mista Zelensky ya kuma gabatar da shawarwari na tsagaita wuta na ɗan lokaci a ƙarshen mako.

    A gefe guda kuma, jami'an Ukraine sun ce Rasha ta kai hari kan wata cibiyar masana’antu a yankin Dnipropetrovsk cikin dare, inda mutum huɗu suka mutu sannan wasu biyar suka jikkata.

  7. Arangama tsakanin mayaƙan Houthi da dakarun gwamnati ta yi ajalin mutum 122

    An yi mummunar arangama tsakanin mayaƙan Houthi da dakarun gwamnati a Yemen, lamarin da ya sanya fargabar cewa rikicin da aka jima ana yi a ƙasar zai iya sake rikidewa zuwa yaƙi.

    Tun bayan da mayaƙan Houthi suka ƙaddamar da hari a yankunan bakin teku ranar Alhamis, rahotanni sun ce aƙalla mutum 122 sun rasa rayukansu.

    Wata majiya daga sojojin ta ce mayaƙan Houthi, waɗanda Iran ke marawa baya, na son ƙwace iko da tashar jiragen ruwa ta Mokha, wadda idan suka mallake ta za su iya ƙara ƙarfafa ikonsu a mashigar ruwan Bab al-Mandeb.

    Wakilin BBC ya ce jiragen ruwan da ke dakon mai na Saudiyya na amfani da wannan mashigar ruwa a matsayin wata hanya a madadin mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga harkokin jigilar mai a yankin.

  8. Hare-haren Isra'ila sun kashe mutum uku da jikkata 20 a Lebanon

    Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce mutum uku sun mutu yayin da wasu fiye da mutum 20 kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra’ila ta kai a kudanci da gabashin ƙasar.

    Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hare-haren ne a matsayin martanin wani harin jirgin sama marar matuki da ƙungiyar Hezbollah ta kai kan sojojinsu da ke Lebanon.

    Isra’ila na ci gaba da kasancewa da sojojinta a wasu yankuna na kudancin Lebanon tun bayan kaddamar da wani gagarumin farmaki kan Hezbollah a watan Maris, bayan da ƙungiyar ta kai hari da jirage marasa matuƙa zuwa Isra’ila domin nuna goyon baya ga Iran.

    Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta taimaka wajen kulla wa, Isra’ila da Hezbollah na ci gaba da kai wa juna hare-hare akai-akai a cikin ƙasar Lebanon.

  9. Amurka za ta sayar wa Saudiyya makamai na dala biliyan 5

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da amincewa da wata yarjejeniya ta sayar wa Saudiyya kayan makamai da darajarsu ta kai dala biliyan 5.

    A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta amince da buƙatar Saudiyya na sayen dubban bama-bamai da kuma na’urorin jagorantar makamai masu linzami masu dogon zango.

    A cewar ma’aikatar, ban da makaman, yarjejeniyar za ta haɗa da manyan makamai da kayayyakin gyara da sinadarai da kuma ayyukan tallafin fasaha da dabarun sufuri da samar da kayayyaki.

    Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani mataki na inganta tsaron wata muhimmiyar ƙawarta, tare da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiyar siyasa da ci gaban tattalin arziki a yankin Tekun Fasha.

    Sanarwar ta kuma jaddada cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa ƙarfin tsaron sararin samaniyar Saudiyya domin fuskantar barazanar da ake samu a yankin a halin yanzu.

  10. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Asabar daga nan sashen Hausa na BBC.

    Yau ma mun dawo kamar kullum da labarai da rahotanni da sharhi kan muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasance da wannan shafi na kai tsaye na sashen Hausa na BBC. Ka da ku manta za ku iya leƙawa sauran shafukan namu na sada zumunta domin samun ƙarin labarai da rahotanni da ma hirarraki.