Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Sanata Shehu Buba da ya musanta zargin ɗaukar nauyin ƴanbindiga?
Sanata Shehu Buba Umar, mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Bauchi ta Kudu, ya yi watsi da zarge-zarge da kuma bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta da ke danganta shi da wasu da ake zargin shugabannin ƴan bindiga ne.
Buba, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kiwon Dabbobi da Samar da Kayan Dabbobi, kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi a jam'iyyar PRP, ya fuskanci zarge-zarge daban-daban na goyon baya ga ƴan bindiga, zarge-zargen da ya ci gaba da musantawa.
Tuni dai wasu ƴan Najeriya suka fara kiraye-kiraye ga hukumomin da al'amarin ya shafa da su fara bincike domin gano haƙiƙanin gaskiyar al'amari kan zarge-zargen.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake yi wa wani mai riƙe da muƙamin gwamnati ko siyasa zargin hannu a tallafa wa ta'addanci ba.
Masu sharhi na alaƙanta irin waɗannan zarge-zarge da gazawar gwamnati kasancewar hukumomi ba sa bincikar zarge-zargen ko kuma idan sun ƙaddamar da bincike ba sa bayyana wa ƴan ƙasa sakamakon abin da ke sa jama'a ke ta hasashe da ci gaba da zargi.
Zarge-zarge kan Sanata Shehu Buba Umar
Sanata Buba Shehu dai ya fuskanci zarge-zarge daban-daban na goyon baya ga ƴan bindiga, zarge-zargen da ya ci gaba da musantawa.
Sabon zargin ya fito ne daga wani wanda ya bayyana kansa a matsayin mazaunin gidan sanatan mai suna Hassan, wanda a wata hira da ya yi da shahararren mai yaɗa labarai a kafafen sada zumunta, D English Alhaji Media , ya yi iƙirarin cewa Sanata Buba na cikin ƴan siyasar da ke taimaka wa ƴan bindiga.
Hassan ya kuma yi zargin cewa an kai wasu mutane da ake alaƙantawa da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide, zuwa Abuja domin samun horo na musamman, wanda ya ce ɗaya daga cikin hadiman Sanatan ne ya shirya musu.
A 2025 ma wani rahoton Sahara Reporters ya yi zargin cewa Sanata Shehu Buba ya taka rawa wajen samar da wata yarjejeniyar zaman lafiya da fitaccen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, wanda hukumomi ke nema ruwa a jallo.
Bugu da ƙari, a watan Satumban 2024 gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya zargi Sanata Shehu Buba da cewa, ta hannun babban hadiminsa na majalisa, Yahaya Ibrahim, ya yi wa wani da ake zargin ɗan bindiga ne daga Jihar Zamfara mai suna Abubakar Idris da kuma wata Zainab Gado rajista tare da ɗaukar nauyin aikin Hajji ta Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Bauchi.
Gwamnan ya ce daga baya jami'an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama tare da tsare Idris bayan sun gano zargin cewa yana da hannu a ayyukan ƴan bindiga da kuma garkuwa da mutane a Jihar Zamfara.
Martanin Sanata Shehu Buba Umar
Sanata Buba ya bayyana zarge-zargen a matsayin ƙarya, mugunta da kuma wani tsari na yaɗa farfaganda da aka shirya domin cimma wasu muradun siyasa, ba wai don neman gaskiya ko tabbatar da adalci ba.
Ya kuma yi watsi da bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta da kuma zarge-zargen da ke danganta shi da fitattun shugabannin ƴan bindiga, yana mai cewa an ƙirƙire su ne gaba ɗaya.
A cikin wata sanarwa mai taken "Bayyana Gaskiyar Lamari", sanatan ya bayyana cewa binciken tantance gaskiya ya nuna bidiyon da ake yaɗawa ya haɗa wasu bidiyo guda biyu da ba su da alaƙa da juna.
A cewarsa, ɗaya daga cikin bidiyon ya nuna wasu Alhazan da suka koma Najeriya daga aikin Hajji daga Jihar Kaduna waɗanda suka ziyarci gidansa a shekarar 2023 kuma suke magana da harshen Fulfulde, yayin da ɗaya bidiyon ya nuna wasu daban suna nuna fasfo-fasfo ɗinsu tare da magana da Turanci.
Ya ce an sarrafa tare da haɗa waɗannan bidiyoyin ne da gangan domin yaudarar jama'a da ƙoƙarin nuna cewa wasu ƴan bindiga ne ke kai masa ziyara a gidansa.
Buba ya yi kira ga 'yan jarida, masu tantance gaskiyar labarai, ƙungiyoyin farar hula da jagororin jama'a da su yi nazari mai zurfi kan zarge-zargen bisa ƙa'idojin aikin jarida da ƙwarewa.
Ya buƙace su da su tantance sahihancin bidiyoyin da ake yaɗawa, su tabbatar da haƙiƙanin mutanen da ke cikin bidiyoyin, su duba bayanan kotuna da suka dace, tare da tuntuɓar hukumomin tsaro domin tabbatar da gaskiyar lamarin kafin yanke hukunci.
Wane ne Sanata Shehu Buba Umar?
Sanata Shehu Buba Umar ɗan siyasa ne mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya.
Ya kasance tsohon shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Ƙasa da Harkokin Leken Asiri, sannan a halin yanzu shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kiwon Dabbobi.
Haka kuma, Shehu Buba shi ne ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi na jam'iyyar PRP gabanin zaɓen 2027, bayan ficewarsa daga jam'iyyar APC.
Bayanan da suke a fili sun nuna cewa an haifi Sanata Buba Umar a shekarar 1976 a ƙauyen Nabordo da ke ƙaramar hukumar Toro ta jihar Bauchi.