Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa malaman makaranta ke zanga-zanga a jihar Oyo?
Ɗaruruwan malaman makaranta da iyaye da ƙungiyoyin matasa ne suka fantsama kan titunan jihar Oyo domin yin zanga-zanga kan abin da suka kira rashin taɓuka komai daga gwamnati don ceto ɗalibai da wasu malamansu da ƴanbindiga suka sace makwanni biyu da suka gabata.
Masu zanga-zangar ɗauke da alluna ɗauke da hotunan yara, wasu cikin tsoro wasu kuma na nuna jikinsu da tabbai.
Wasu yara ƴan shekara 12 zuwa 15 su ma sun bi sahun masu zanga-zangar.
Zanga-zangar wani ɓangare ne na matakan malaman makarantun gwamnati karƙashin ƙungiyar malamai ta NUT na matsa wa gwamnati lamba ta kuɓutar da ɗalibai da malamansu da aka sace a watan da ya gabata.
Abin da ya faru
A ranar Juma'a ta 15 ga watan Mayu ne dai wasu ƴan bindiga suka sace ɗalibai ƴan firamare 39 ciki har da ɗan shekara biyu da haihuwa da malamansu guda 7 daga makarantun da ke garin Ahoro-Esinele da ke jihar Oyo.
Hukumar kula da harkokin ƙananan makarantu sun bayar da umarnin rufe makarantun da ke kusa da garuruwan da aka sace daliban, har sai abin da hali ya yi.
Hukumomi sun tabbatar wa da iyaye cewa ba za su sarara ba har sai sun tabbatar da dawo da dukkanin yaran da aka sace.
To sai dai har yanzu yaran ba su koma ga iyayensu ba sannan wani daga cikin malaman da aka sace tare da yaran sun rasa ransu a hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
An dai fi alaƙanta zanga-zangar da kisan daya daga cikin malaman tun bayan fitar wani bidiyo da ya rinƙa waɗari a shafukan sada zumunta da ke nuna yadda waɗanda suka yi garkuwar da shi suka kashe shi.
Tinubu ya aike da tawaga Oyo
Yajin aikin na ƙungiyar malaman makaranta ta jihar Oyo na faruwa ne kwana ɗaya bayan da wata tawagar da shugaba Tinubu ta ziyarci garin da aka sace yaran sannan ta jajanta wa iyayen wadanda abin ya shafa.
Tawagar ta ƙunshi shugaban ma'aikatan Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribaɗu da ministan tsaro, Christopher Musa da Sifeton Janar na ƴansanda, Tunji Disu.
Da yake jawabi ga al'ummar da abin ya shafa a Ogbomosho, ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa ya sanar da cewa shugaba Tinubu ya amince da ɗaukar dakarun kare dazuka guda 1000.
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ɗaukar dakarun kare dazuka guda 1000 a jihar Oyo".
Ina ɗalibai 50 da aka sace a Borno?
A irin wannan rana ne ta Juma'a 15 ga watan Mayu wasu da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram ne a jihar Borno suka yi garkuwa da ɗalibai guda 50 daga makarantar firamare ta Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira-Uba.
Har kawo yanzu babu bayani dangane da makomar yaran sannan babu wani hoɓɓasa da ake yi wajen nemo su saɓanin abin da ke faruwa dangane da ɗaliban jihar Oyo da ake ta zanga-zanga a kansu.
Babu wata jinjinar magana daga gwamnatin jihar Borno da ma Najeriya dangane da yaran guda 50 sannan za a iya cewa hankalin kafafen watsa labarai ya kau daga kansu saɓanin takwarorinsu na jihar ta Oyo.
Za a iya cewa a jihar Bornon ne aka dasa ɗan-ba na satar ƴan makaranta a Najeriya inda a 2014, ƴan ƙungiyar Boko Haram suka yi garkuwa da ɗalibai sama da 270 kuma har kawo yanzu ba a san makomar fiye da 90 ba, shekaru 12 da suka gabata.