Iraq ta sanar da ƴan wasan da za su buga mata kofin duniya, Gasar kofin duniya
Kocin Iraq, Graham Arnold, ya sanar ranar Litinin jerin ƴan wasa 26 da za su buga Kofin Duniya, inda ya dogara sosai da babban rukuni na ƴan wasan da suka taimaka wajen samun tikitin shiga gasar ta hanyar wasannin share fage a tsakanin nahiyoyi.
Ɗan wasan da ke buga gaba, Aymen Hussein ana sa ran zai jagoranci gurbin kai hare-hare a tawagar Iraq a wasannin da za ta buga a Arewacin Amurka. Wannan tsohon ɗan wasan, wanda ake kallonsa a matsayin gwarzo, shi ne zai jagoranci sahun gaba tare da Ali Al-Hamadi na Ipswich Town da kuma matasan ƴan wasa masu basira da ya haɗa da Ali Jassim da kuma Youssef Amyn.
Wani abin lura shi ne rashin sunan Dario Naamo daga cikin tawagar. An cire ɗan wasan Dundee, bayan da ya canza ƙasar da yake wakilta a wasannin ƙasa da ƙasa, bayan da ya taɓa bugawa Finland a matakin matasa.
Zaɓin ƴan wasan tsakiya na Arnold ya ƙunshi ƙwararru da suka saba da ƙwallon ƙafa a Turai, inda Zidane Iqbal na Utrecht da Aimar Sher na Heerenveen ke kan gaba a jerin.
Haka kuma, Arnold ya yanke shawarar barin mai tsaron raga, Kamil Saadi cikin tawagar atisaye a matsayin kariya idan aka samu rauni.
Iraq na komawa gasar Kofin Duniya a karon farko cikin shekaru 40, bayan ta doke Bolivia da ci 2-1 a watan Afrilu domin samun tikitin ƙarshe.
An saka su a Rukunin I tare da Faransa da Senegal da kuma Norway.
Masu tsare raga: Fahad Talib, Jalal Hassan, Ahmed Basil
Masu tsaren baya: Hussein Ali, Manaf Younis, Zaid Tahseen, Rebin Sulaka, Akam Hashem, Merchas Doski, Ahmed Yahya, Zaid Ismail, Frans Putros, Mustafa Saadoon
Masu buga tsakiya: Amir Al Ammari, Kevin Yakob, Zidane Iqbal, Aimar Sher, Ibrahim Bayesh, Ahmed Qasim, Youssef Amyn, Marko Farji Masu cin ƙwallaye: Ali Jassim, Ali Al Hamadi, Ali Yousef, Aymen Hussein, Mohanad Ali