'Abin da ya sa kakana ya shiga yaƙin Biyafara'

    • Marubuci, Tamasin Ford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa Eye
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

Meji Alabi darakta ne na wasu manyan mawaƙa da suka yi suna a duniya: Beyonce, Burna Boy, Davido da Stormzy. To amma akwai wani babban abu da ya sanya ya yanke shawarar yin rahoto na musamman kan yaƙin basasar Najeriya.

Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da abubuwan da za su iya tayar da hankalin mai karatu.

Yadda muka yi rayuwa har ƙarshen yaƙin Biyafara: Bayanai daga mutanen da suka shaida yaƙin Biyafara, wanda sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya shirya, ya ƙunshi wasu bidiyoyin yaƙin da ba a taɓa gani ba a baya, yaƙin da aka yi daga shekarar 1967 zuwa 1970, lokacin da bambancin ƙabilanci ya kusa raba ƙasar ta Yammacin Afirka.

"Abu ne da ya buɗe mani ido sosai. Na girma ba tare da sanin abubuwa da dama ba game da yaƙin, wane ne ya yaƙi wa?" in ji Alabi mai shekara 37 wanda iyayensa ƴan Najeriya suka haifa a birnin Landan na Birtaniya kafin ya koma Texas ta ƙasar Amurka domin yin karatu.

Shahara mafi girma da ya samu ita ce a shekara biyar da suka gabata, lokacin da ya lashe kyautar Grammy a kan aikin da ya yi na kasancewa ɗaya daga cikin waɗanda suka bayar da umarnin bidiyon waƙar Beyonce mai taken 'Brown Skin Girl'.

Kafin daga baya ya haɗa hannu da baffansa Leke Alabi-Isama, wanda shi ma mashiryin fina-finai ne kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kirƙiri kamfanin haɗa fim na PriorGold Pictures, domin haɗa rahoto na musamman kan babban abin baƙin ciki da ya faru a tarihin Najeriya.

Ɗan abin da suka sani sun san shi ta bakin mahaifin Leke, kuma kakan Meji, wato Godwin Alabi-Isama, tsohon kwamanda, wanda ya yi yaƙin a ɓangaren rundunar sojin Najeriya domin kakkaɓe ƴan awaren Ibo da suka ɓalle a kudu maso gabashin ƙasar, suka raɗa wa yankin suna Biyafara.

"Na kalli abin ne kawai ta ɓangaren Najeriya," in ji Leke. "Ban taɓa sanin irin tashin hankalin da ya faru ba. Ban taɓa sanin uƙubar da aka fuskanta a ɗaya ɓangaren ba."

A tsawon rahoton na musamman na Africa Eye, waɗanda suka tsira daga yaƙin, waɗanda yanzu suke da shekara kimanin 70 zuwa 80, sun yi bayani kan rayuwarsu a lokacin da ake yaƙin da yadda aka yi yaƙin da yadda lamarin ya sauya rayuwar miliyoyin mutane, kuma abin ke tasiri har yanzu.

Rikicin, wanda ake yi wa laƙabi da yaƙin Biyafara, ya samo asali ne bayan wasu jerin juyin mulkin soji da kuma watanni na kashe-kashen ƴan kabilar Ibo a arewacin Najeriya.

"Kimanin ƴan ƙabilar Ibo miliyan ɗaya ne suka koma yankinsu na asali, kudu maso gabashin ƙasar, inda jihohi uku suka ɓalle suka kafa ƙasar Biyafara.

Daga nan sai gwamnatin Najeriya ta ayyana yaƙi - ɗaya daga cikin yaƙi mafi ƙazancewa da rarraba kawunan al'umma a nahiyar Afirka.

An yi ƙiyasin cewa kimanin mutum 500,000 zuwa miliyan uku ne suka mutu, mafi yawa a cikinsu yara ne, kuma yaƙin ya zamo na farko a duniya da aka yaɗa mummunan halin da aka shiga ciki ta kafar talabijin.

An yaɗa mummunan hoton yadda yara suka faɗa cikin ƙangin yunwa a kafafen talabijin na ƙasar, a karon farko. Bayan shafe wata 30 ana yaƙi, yankin Biyafara ya miƙa wuya.

Mafi yawan ƴan Najeriya sun ji labarin yaƙin Biyafara ne ta hanyar labaran da kakanninsu suka ba su.

Gabanin watan Satumban 2025, an kwashe kimanin shekara 10 ba tare da darasin tarihi ba a cikin manhajar koyarwa ta makarantun Najeriya ba.

Ga Leke, ɗan shekara 44, wanda aka haifa kuma ya girma a garin Abeokuta na jihar Ogun a kudu maso yammacin ƙasar, "layi ɗaya ne kawai ko layi biyu a cikin littafi".

"Har yanzu babu cikakken labarin, cikakken bayani kan uƙubar. Kuma ina ganin Najeriya tana tsoron fuskantar gaskiyar da ta shafe ta ne," in ji shi.

Leke da sauran ƴan'uwansa 23 sun girma suna jin labaran yaƙe-yaƙe daga mahaifinsu Godwin Alabi-Isama, wanda ya kasance shugaban ma'aikata na Birgediya Janar Benjamin Adekunle, na runduna ta musamman ta uku a lokacin yaƙin.

"Ya zama tamkar shi mahaifina an san shi ne a matsayin wanda ya taimaka wajen ƴanto wannan gari da kuma waɗannan ƙauyuka. Ina kallon shi a matsayin jarumin yaƙi," in ji shi.

Sai bayan ya kai shekara 30 ne Leke ya fara bincike kan abubuwan da suka faru a lokacin yaƙin, inda ya gane mummunar yunwar da aka shiga a yankin Biyafara, da rawar da mahaifinsa ya taka kan yaƙin mai cike da taƙaddama da kuma gaskiyar wahalar da aka sha.

Sojojin Najeriya, ciki har da rundunoni uku sun fuskanci zarge-zargen aikata laifin yaƙi a yankin Biyafara, ciki har da kisan fararen hula.

"Lokaci na farko da na fara ganin bidiyon mutane da yara cikin ƙangin yunwa... abin akwai ban-tsoro. Kuma na yi tunanin wannan lokaci ne da na gano gaskiya," in ji Leke.

"A gare ni, wannan ne lokacin da gaskiyar abubuwan da suka faru a yaƙin suka fito fili. Kamar dai, tabbas wani mummunan abu ya faru, kuma mahaifina na ɗaya ɓangaren.

"Lokacin da ka gano hakan, za ka san cewa gaskiyar da ka sani ba ita kaɗai ce gaskiya ba, lokaci ne na ƙanƙan da kai."

Leke da Meji sun kasa fahimtar me ya sa ƴan Najeriya ba su yi rahotannin bidiyo masu yawa ba kan yaƙin, inda suka bayyana wahala da suka sha wajen samo bayanan gaskiya na abubuwan da suka faru.

Wannan ne dalilin da ya sa mutanen biyu waɗanda suke aiki da manyan mawaƙan duniya suka yanke sahawarar yin wannan rahoto na musamman na bidiyo.

"Abu ne da ba a maganarsa a fili," in ji Meji, wanda bidiyoyin waƙoƙin da ya haɗa suka taimaka wajen haskaka waƙoƙin Najeriya a idon duniya, waɗanda ke da abubuwa da ke ƙayatar da miliyoyin makallata.

"Ba a yi bayani kansa ba kai-tsaye sannan kuma matasa ba su yi tambayoyi sosai domin gano gaskiya ba kamar wannan karo," in ji.

Rahoton na musamman ya haɗo fasihai da dama daga yankin - inda Meji ya shawo kan mai haɗa kiɗan nan ɗan ƙasar Ghana Ray Michael Djan Jr, wanda ya haɗa sautin fim ɗin Black Panther: Wakanda Forever, domin ya haɗa waƙar.

Haka nan ya kuma yi amfani da sashen harshen Ibo na BBC, da masanan tarihi yan ƙabilar Ibo da kuma labaran da aka samu daga ganau waɗanda suke raye lokacin yaƙin, waɗanda a baya ba su taɓa faɗa wa wani irin tashin hankalin da suka gani ba.

"Mutanen suna ƙarewa a hankali a hankali, kuma idan ba mu tattara bayanansu ba yanzu, muna cikin yin asarar taskace abubuwan da suka sani, amma dama ce ta tattara duk tarihin ta yadda zai taimaka wajen fahimta da kuma warkar da raunin da abin ya bari," in ji Leke.

Biyu daga cikin manyan waɗanda suka bayar da labarin tsoffin sojoji ne mata, waɗanda suka yi yaƙi a ɓangare daban-daban. Akwai kuma tattaunawa da wani ma'aikacin agaji da tsohon wakilin BBC Martin Bell, waɗanda dukkaninsu sun soki martanin da ƙasashen duniya suka mayar kan rikicin.

Yayin da Leke da Meji suka samu labaran yaƙi da dama daga Godwin Alabi-Isama a baya, ba su taɓa samun damar yi masa muhimman tambayoyi ba.

Tawagar wakilan BBC ta jagoranci tattaunawar domin tabbatar da cewa an yi wa tsohon kwamandan tambayoyin da suka shafi zarge-zargen laifukan yaƙi da aka yi wa runduna ta uku ta musamman ta yaƙin.

A lokacin yaƙin, gwamnatin Najeriya ta toshe hanyar shigar Abinci zuwa yankin Biyafara - ta datse hanyar da yankin ke da shi zuwa bakin teku da filayen jiragen sama da kuma duk wata hanyar samun tallafi daga waje.

Toshewar ta haifar da tsananin yunwa kuma ana tunanin tsananin yunwar ce ta haifar da mutuwar ɗaruruwan mutane.

Leke ya bayyana yanayin, inda ya nuna wa babansa wani bidiyo maras kala na tamuƙaƙƙun yara, ya ce a tsawon rayuwarsa ta shekara 43, bai taɓa jin muryar babansa ta yi rawa irin haka ba.

"Duk lokacin da na sake kallo, idan aka zo daidai wurin, sai tsikar jikina ta tashi," in ji shi.

A lokacin tattaunawar, mahaifin nasa ya bayyana yadda a cikin rashin sani a lokacin yaƙin, ya ci naman mutum. Lokacin da suka ci naman mutum ya faru ne a lokacin da wasu ƙauyawa suka bai wa rundunarsa abinci a wani yankin Biyafara da aka mamaye.

A matsayin martani ga wannan rahoton bidiyo na musamman, gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran wannan ya zamo tunatarwa kan doguwar tafiyar da Najeriya ta shawo cikin shekara 59 da suka gabata "da kuma muhimmancin ci gaba da tattaunawa, da sulhuntawa da kuma abubuwan da suka haɗa al'ummar wuri ɗaya domin gina ƙasa mai inganci don amfanin waɗanda za su zo daga baya."

Leke da Meji da ma wasu da dama za su so hakan.

"Burina shi ne wannan rahoton bidiyo na musamman ya ƙarfafa wa ƴan Najeriya gwiwa sun yi tunani kan mummunan tarihin da muka baro baya da nufin magance shi cikin gaskiya, da nuna nadama da tausayi. Ya rage gare mu mu yi hakan."

Ƙarin bayani daga Charlie Northcott, Izzy Fleming da Adline Okere