HPV: Cutar da ta fi yaɗuwa ta hanyar saduwa - mece ce rigakafinta?

Asalin hoton, Getty Images
Bincike ya nuna cewa idan aka yi wa mace allurar rigakafin HPV, ana iya rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mahaifa da kusan kashi 90 cikin 100.
Cutar kansar mahaifa ita ce ta huɗu cikin cututtukan daji da suka fi addabar mata a duniya, inda take kashe fiye da mutum 300,000 a kowace shekara.
Ta wace hanya allurar rigakafin HPV ke kare mutum daga cutar sankarar mahaifa?
Allurar rigakafin HPV tana ba da kariya daga nau'o'i tara na ƙwayar cutar kansar mahaifa.
Waɗannan sun haɗa da nau'o'in ƙwayoyin cutar guda biyu da ke haddasa kusan dukkan cutukan sankarar mahaifa, da kuma mafi yawan kansar dubura, da wasu nau'ikan kansa da ke fitowa a al'aura da kai ko wuya.
Bincike ya nuna cewa allurar na ba da kariya daga kamuwa da ƙwayar HPV na aƙalla shekaru 10, ko da yake masana sun yi ƙiyasin kariyar za ta iya ɗaukar lokaci mai tsawo fiye da haka.
Bincike ya nuna cewa yin allurar rigakafin HPV na rage yawan kamuwa da cutar sankarar mahaifa da kusan kashi 90 cikin 100.
Wa ya kamata a yi wa allurar rigakafin?
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce wɗanda aka fi so a bai wa fifiko wajen yin allurar rigakafin HPV su ne yara masu shekaru tsakanin 9 zuwa 14.
Masana sun ce allurar ta fi yin tasiri idan aka yi wa yara mata da maza ita kafin su kamu da ƙwayar cutar HPV.
Sun ce allurar na hana kamuwa da cutar ne kawai, amma ba ta iya kawar da ƙwayar cutar daga jikin wanda ya riga ya kamu da ita.
Saboda yawaitar ƙwayar cutar HPV a duniya, ana ba da shawarar a yi wa yara allurar tun kafin su fara jima'i.
WHO ta ce ana iya yin allurar sau ɗaya ko biyu, gwargwadon tsarin da ake bi. Sai dai mutanen da garkuwar jikinsu ba ta da ƙarfi suna iya buƙatar allurar sau biyu zuwa uku domin samun cikakkiyar kariya.
Mene ne HPV?
HPV, wanda a turance shi ne (Human Papillomavirus), wasu ƙwayoyin cuta ne da ke yawo a tsakanin jama'a.
Akwai nau'o'in HPV sama da 100, kuma galibin masu kamuwa da su ba sa nuna wata alama ta rashin lafiya. Sai dai wasu nau'o'in na iya haddasa ƙuraje ko tsiro a fata da a hannu ko ƙafa ko al'aura ko a cikin baki.
Yawancin mutanen da suka kamu da HPV ba sa ma sanin suna ɗauke da ita, domin garkuwar jikinsu kan kawar da ƙwayar cutar ba tare da sun nemi magani ba.
Sai dai akwai wasu nau'o'in HPV da suka fi haɗari waɗanda ke iya haifar da sauye-sauye a ƙwayoyin halitta inda daga baya sukan rikiɗe su zama kansa.
Shin ana iya kamuwa da cutar ta hanyar saduwa?
Ana iya kamuwa da ƙwayar cutar HPV ta hanyar cuɗanya da juna kuma tana saurin yaɗuwa.
Kusan kashi 80 cikin 100 na mutane na iya kamuwa da HPV kafin su kai shekaru 25.
A mafi yawan lokuta, ana kamuwa da ƙwayar cutar na tsawon watanni 18 zuwa shekaru biyu.
Sai dai babu wata hujja a kimiyyance da ke nuna cewa ƙwayoyin cutar HPV na iya yaɗuwa ta hanyar saduwa kamar irin su cutar sanyi ta goloriya (gonorrhoea).
Amma akwai yiwuwar a kamu da cutar yayin saduwa tsakanin namiji da mace.
Ko rigakafin HPV ta wadata a duniya?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Binciken baya-bayan nan da mujallar British Medical Journal ta wallafa ya nuna cewa sama da kashi 85 cikin 100 na mace-macen da cutar sankarar mahaifa ke haifarwa na faruwa ne a ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi.
A irin waɗannan ƙasashe, galibi ba a gano cutar da wuri, sai bayan ta yi tasiri sosai kuma alamunta sun fara bayyana.
A baya, WHO ta bayyana cewa tana fatan kawar da cutar sankarar mahaifa a cikin ƙarni mai zuwa ta hanyar tabbatar da cewa kashi 90 cikin 100 na mutane sun karɓi allurar rigakafin HPV kafin shekarar 2030.
Ta ce yanzu ƙasashe 165 sun fara amfani da allurar rigakafin HPV, yayin da kashi 31 cikin 100 na yara mata suka karɓi aƙalla kashi na farko na allurar.
Ƙasashen Burundi da Ukraine na daga cikin sabbin ƙasashen da suka shigar da allurar HPV cikin rigakafin cututtuka na ƙasashensu.
WHO ta ce yankin Afirka da ke kudancin hamadar Sahara ne ke da mafi yawan mata masu ɗauke da ƙwayar cutar HPV da ke haddasa sankarar mahaifa, inda yawan ya kai kashi 24 cikin 100.
Yankin Latin Amurka da Caribbean ne na biyu da ke da kashi 16 cikin 100, sai Gabashin Turai da kashi 14 cikin 100 da kuma Kudu maso Gabashin Asiya da kashi 14 cikin 100.
Masana sun ce ƙarancin gudanar da gwajin gano cutar da wuri, da rashin samun damar jinya da kuma shakku kan allurar rigakafi na daga cikin abubuwan da ke haddasa yawaitar cutar a waɗannan yankuna.
Ƙasar Rwanda na daga cikin ƙasashen Afirka na farko da suka fara wayar da kai game da rigakafin HPV. A shekarar 2011, ƙasar ta ƙaddamar da wani shiri na yi wa yara mata allurar rigakafi tun suna ƙanana tare da samar da gwaje-gwajen gano sankarar mahaifa ga mata.
A shekarar farko, Rwanda ta yi wa yara mata tara cikin goma allurar rigakafin. Masana na kallon wannan nasara a matsayin abin koyi ga sauran ƙasashe.
A yanzu Rwanda tana da burin kawar da cutar sankarar mahaifa gaba ɗaya nan da shekarar 2027.
Duk da cewa allurar rigakafin HPV na rage yiwuwar kamuwa da sankarar mahaifa sosai, ba za ta iya ba da kariya daga dukkan nau'o'in ƙwayar cutar HPV.
Saboda haka masana suna shawartar mata da su riƙa yin gwajin mahaifa akai-akai bayan sun kai shekaru 25 domin gano duk wata matsala da wuri da kuma fara magani cikin lokaci.











