Yadda AI ke taimaka wa maza gano ƙwayoyin maniyyi da ke ɓoye

....

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Krupa Padhy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wata sabuwar fasaha mai amfani da basirar AI tana taimakawa wajen gano ƙwayoyin maniyyi a jikin mazan da aka gaya musu cewa ba su da maniyyi kwata-kwata.

Hakan na ba wasu ma'aurata da suka shafe shekaru suna ƙoƙarin samun haihuwa wata sabuwar dama ta samun ɗa.

A farkon watan Nuwamban 2025 ne Penelope ta samu kira daga likitanta yayin da take komawa gida daga aiki a jihar New Jersey. Likitan ya sanar da ita labarin da ta daɗe tana jira, cewa tana da juna biyu bayan shekaru biyu da rabi na ƙoƙarin samun ciki.

Bayan gwaje-gwaje da dama, Penelope da mijinta Samuel sun gano cewa yana fama da cutar Klinefelter syndrome, wata matsalar gado da ke shafar maza masu ƙarin X chromosome.

Sau da yawa, masu wannan matsala ba sa samar da isasshen maniyyi ko kuma ba sa da maniyyin gaba ɗaya abin da ake kira azoospermia. Kimanin kashi 10 cikin 100 na mazan da ke fama da rashin haihuwa suna da wannan matsala.

Cikin farin ciki da mamaki, Penelope ta jira har Samuel ya dawo gida kafin ta sanar da shi labarin. Ta ce mijinta ya fashe da kuka saboda wahalhalu da lokaci da binciken da suka yi kafin su kai wannan mataki. Ta kuma ce suna da ƙwayar amfrayo guda ɗaya kacal, amma cikin ikon Allah ta yi nasarar samun juna biyu.

An samu wannan nasara ne ta hanyar wata sabuwar dabara mai suna Star, wato "Sperm Track and Recovery", da jami'ar Columbia ta ƙirƙira domin gano ɓoyayyun ƙwayoyin maniyyi a jikin mazan da ke fama da azoospermia. Fasahar na amfani da AI wajen gano kaɗan daga cikin ƙwayoyin maniyyin da suke ɓoye.

Samuel ya ce ya taɓa jin tsoron ba zai iya samun ɗan cikinsa ba, musamman bayan likitoci sun gaya masa cewa yana da damar kashi 20 cikin 100 ne kawai na samun ɗan cikinsa.

...

Asalin hoton, Columbia University Fertility Center

Bayanan hoto, Tsarin Star mai amfani da fasahar AI na iya gano da cire ƙwayar maniyyi ɗaya cikin ƙanƙanin lokaci sosai.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rashin haihuwa na shafar miliyoyin mutane a duniya, inda kusan mutum ɗaya cikin shida na shekarun haihuwa ke fuskantar matsalar samun ciki aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu.

Rashin haihuwa a ɓangaren maza na taka rawa a kusan kashi 50 cikin 100 na irin waɗannan lokuta, kuma kusan kashi 1 cikin 100 na maza na fama da lalurar azoospermia, wato rashin samun maniyyi a jikin su.

Wannan na nufin akwai miliyoyin maza a duniya da adadin maniyyinsu ya yi ƙasa matuƙa, har ta kai ana wahalar gano ƙwayoyin maniyyinsu ɗaya-ɗaya. Amma amfani da fasahar AI na ba da sabon fata wajen gano waɗannan ƙwayoyin maniyyi da ke ɓoye, wanda zai iya taimaka wa mutane su samu damar zama iyaye.

A ƙarshen shekarar da ta gabata, bayan shekaru biyar ana aikin gwaji, an samu haihuwar jariri na farko ta amfani da tsarin Star system.

Wannan ya ba wani ma'aurata da suka shafe kusan shekaru 20 suna fama da rashin haihuwa damar samun ɗa cikinsu. Daraktan Cibiyar Kula da Haihuwa ta Jami'ar Columbia, Zev Williams, ya bayyana cewa hakan ya kasance abin farin ciki matuƙa ga tawagarsu.

Bayan fara amfani da wannan fasaha, cibiyar ta fara karɓar mutane daga sassa daban-daban na duniya, inda jerin masu jira ya kai ɗaruruwa. Daga binciken mutane 175 na baya-bayan nan, an gano cewa ana samun maniyyi a kusan kashi 30 cikin 100 na lokuta, har ma a cikin mutanen da aka taɓa gaya musu cewa ba su da damar haihuwa ta amfani da maniyyinsu.

Binciken ya kuma nuna cewa wannan fasaha na iya gano maniyyi sau 40 fiye da yadda ƙwararren ma'aikaci zai iya yi da hannu ta amfani da microscope. Yawanci, samfurin maniyyi na ɗauke da miliyoyin ƙwayoyin maniyyi a millilita guda, amma a cikin masu lalurar azoospermia, wataƙila ƙwaya ɗaya kawai ce ke iya kasancewa a cikin duka samfurin, ko ma babu ko ɗaya. Saboda haka, binciken gano ƙwayar maniyyi ta hanyar gargajiya na da wahala sosai, amma fasahar AI na sauƙaƙa gano abin da a da ake ganin ba zai yiwu ba.

....

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kimanin mutum ɗaya cikin shida daga cikin mutane masu shekarun haihuwa na fuskantar matsalar samun ciki aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu.

Zev Williams ya samu ra'ayin amfani da wannan tsari ta Star system a shekarar 2020 bayan karanta yadda ake amfani da AI wajen gano sabbin taurari a sararin samaniya. Na'urorin hangen sama na zamani na tattara bayanai masu yawa da ɗan Adam ba zai iya bincikarsu da sauri ba, amma AI na iya yin hakan cikin mintuna.

Ya lura cewa hotunan sararin sama suna kama da abin da ake gani a samfurin maniyyi na maza da ake cewa ba su da shi. Wannan ya sa shi tunanin ko za a iya amfani da irin wannan fasaha wajen gano da ware ƙwayoyin maniyyi da ke da wahalar gani.

Shi da tawagarsa suna amfani da microfluid chips, ƙananan hanyoyi da aka zana a gilashi ko roba, inda samfurin maniyyi ke ratsa su yayin da na'urar ke ɗaukar hotuna har 300 a cikin daƙiƙa guda sai AI ta yi nazarin hotunan nan take domin gano ƙwayar maniyyi ko ɗaya a cikin ƙwayoyin jiki.

Idan an gano, fasahar AI na cire ƙwayar cikin daƙiƙa kaɗan ba tare da lalata ta ba. Williams ya ce tsarin na iya gano ko da ƙwayar maniyyi ɗaya ce idan tana cikin samfurin.

A lamarin Samuel mai fama da Klinefelter syndrome, likitoci sun ɗauki samfurin daga ƙwayar halittarsa bayan shirin magani na watanni tara. An tura samfurin zuwa Cibiyar Kula da Haihuwa ta Jami'ar Columbia

A lokaci guda kuma aka ɗauki ƙwayayen Penelope sai aka haɗa da ƙwayoyin maniyyi 8 na Samuel da aka gano ta amfani da fasahar AI inda ɗaya daga cikinsu ya zama amfrayo, wanda ya kai ga samun ciki. Ma'auratan sun ce wannan abu ne da ba su taɓa tsammani ba bayan dogon lokaci na gwaji da jira.

...

Asalin hoton, Columbia University Fertility Center

Bayanan hoto, Gano ƙwayar maniyyi a jikin maza masu azoospermia na da matuƙar wahala, amma AI na iya duba samfurin cikin sauri sosai ya kuma gano su cikin ɗan lokaci kaɗan.

Ba wai kawai gano ƙwayoyin maniyyi da ba a iya gani ba ne AI ke taimakawa a fannin maganin haihuwa ba. Ana kuma amfani da shi wajen inganta sauran matakai na jinyar rashin haihuwa.

Misali, a lokacin IVF, wato tsarin taimaka wa haihuwa ta hanyar dashen jariri, ana amfani da AI wajen tsara yadda za a ba mace maganin gonadotropin domin taimaka wa mahaifa su samar da ƙwayayen haihuwa da yawa. Wannan yana sa magani ya zama na musamman ga kowace marar lafiya, ba irin na gama-gari ba.

Haka kuma, ana amfani da fasahar deep learning wajen zaɓar ƙwayayen haihuwa (gametes) da amfrayo mafi inganci, domin ƙara damar samun ciki mai nasara.

Duk da haka, masana suna cewa har yanzu ana buƙatar manyan bincike na asibiti domin tabbatar da sakamako na dogon lokaci. Suna kuma nuna muhimmancin kula da bayanan lafiya da sirri, da kuma yadda za a ɗauki alhakin sakamako idan matsala ta faru.

Akwai kuma gargadi cewa sabbin fasahohin AI na iya ba mutane fata fiye da kima. Siobhan Quenby, farfesa a fannin haihuwa a jami'ar Warwick ta Birtaniya, ta ce ma'aurata da ke fama da rashin haihuwa na iya shiga halin tsananin buri, wanda zai sa su shiga yanayi na damuwa.

....

Asalin hoton, Getty Images

"Abin farin ciki ne cewa an haɗa fasahar zamani domin samar da sabon mafita ga matsanancin matsalar rashin haihuwa a ɓangaren maza," in ji ta. Ta ƙara da cewa samun ciki guda ɗaya mai nasara muhimmin mataki ne, amma har yanzu ana buƙatar ƙarin bincike a kan marasa lafiya da yawa kafin a tabbatar da cikakken amfanin wannan sabon magani.

Ga Samuel kuwa, yiwuwar amfani da wannan fasahar AI ɗin don ƙara samun 'ya'ya a nan gaba na ba shi ƙwarin gwiwa. Ya ce yanzu suna fatan samun wani ɗa a gaba, amma za su sake shiga irin wannan tsari domin ba su da wani abin ajiya sai ƙwayayen da aka riga aka tattara.

Duk da haka, ya ce yanzu sun samu fata inda da can babu shi, abin da ya ba su sabon salo na rayuwa da fata a nan gaba.