Barcelona za ta maye gurbin Lewandowski da Pedro, Aston Villa na son Mbaye

Asalin hoton, Reuters
Barcelona ta fi son sayen dan wasan Chelsea da Brazil Joao Pedro, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Robert Lewandowski dan Poland, mai shekara 37, wanda zai bar kungiyar a karshen kaka. (Marca)
Aston Villa na sa ido a kan matashin dan wasan gaba na Paris St-Germain da Senegal Ibrahim Mbaye, mai shekara 18, kasancewar kungiyar ta Firmiya ta shirya mayar da hankali kan matasan 'yan wasa a bazaran nan. (Mail, external)
Watakila Barcelona ta mayar da hankalinta kan dan bayan Tottenham da Argentina Cristian Romero idan yunkurinta na sayen dan bayan Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 27, daga Inter Milan bai tabbata ba. (AS)
A shirye Aston Villa take ta sayar da dan wasanta na gaba na gefe Tommi O'Reilly, na Ingila mai shekara 22, wanda yake zaman aro a kungiyar Crewe Alexandra, a karamar gasar Faransa ta League Two, saboda bukatarsa da kungiyoyi irin su Oxford United, da Portsmouth da Huddersfield Town, suke yi. (Mail)
Coventry City, wadda ta yi nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya za ta yi gogayya da Leeds United, wajen sayen dan wasan gaba na Belgium da RB Leipzig Lois Openda, mai shekara 26, wanda ke zaman aro a Juventus. (Sport Witness)
Kungiyar Newcastle na tattaunawa da Bayern Munich tsawon watanni a kan dan wasan gaba na gefe Anthony Gordon, dn Ingila, inda kociyan Bayern Munich, Vincent Kompany ya bayar da damar sayen dan wasan mai shekara 25. (Florian Plettenberg)
Hayden Hackney ya kusa komawa gasar Firmiya, inda Brighton suka bi sahun Nottingham Forest wajen ganin sun yi nasarar sayen tsohon dan tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21, daga kungiyar Middlesbrough. (Football Insider)
Nottingham Forest, da Aston Villa da Crystal Palace duka suna fafutukar sayen matashin dan wasan tsakiya na Rangers Bailey Rice, dan Scotland mai shekara 19. (Teamtalk)
Aston Villa za ta dage a kokarin da take yi na sayen mai tsaron ragar Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekara 23, a matsayin wanda zai maye gurbin golanta Emiliano Martinez, dan Argentina mai shekara 33. (Football Insider)
Hansi Flick, mai shekara 61, zai kulla sabuwar yarjejeniya ta karin shekara biyu a matsayin mai horad da Barcelonainda za a kammala wasu bayanai na kwantiragin nasa a mako mai zuwa. (Mundo Deportivo)









