KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Juma'a 01/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Juma'a 01/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Trump ya yi barazanar janye sojojin Amurka daga Sifaniya da Italiya saboda yaƙin Iran

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana duba yiwuwar janye sojojin ƙasarsa daga Italiya da Sifaniya, sakamakon adawa da yaƙin Iran da ƙasashen biyu ke yi.

    Mista Trump ya bayyana matakin ne kwana guda bayan irinsa da ya yi kan Jamus.

    Cikin wani jawabi da ya yi daga fadarsa, Shugaba Trump ya ce ''yana duba yiwuwar ɗaukar matakin, saboda babu wani taimako da Italiya ta bayar a yaƙin da Amurka ta yi da Iran, sannan ya bayyana Sifaniya a matsayin mafi muni''.

    Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa Amurka na duba yiwuwar rage yawan sojojinta a Jamus, yayin yake samun saɓani da shugaban gwamnatin ƙasar, Friedrich Merz kan yaƙin na Iran

  2. Zai ɗauki Iran shekara 20 kafin ta sake gina kanta - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya faɗa a wata hira da kafar yaɗa labaran Newsmax cewa cewa ''ƙasarsa ta yi nasara a yaƙin da take yi da Iran'' amma ya ce yana son nasarar ta kasance da ''gagarumin rinjaye''.

    A cewar kafar yaɗa labaran CBS, ƙawar hulɗar BBC a Amurka, Mista Trump ya yi iƙirarin cewa An lalata rundunonin sojin sama da na ruwan Iran da kuma tsarin shugabancin ƙasar, iƙirarin da jami'an gwamnatinsa ke yi tun bayan fara yaƙin.

    To amma jami'an Amurka da dama masu kusanci da hukumar leƙen asirin ƙasar sun shaida wa CBS cewa har yanzu Iran da na ƙarfin soji fiye da yadda White House ko ma'aikatar Pentagon ta sanar.

    A cewar wasu jami'ai uku, kusan rabin makaman linzamin Iran da na'urorin harba su sunan nan cikin shirin a lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara a farkon watan Afrilu.

    ''Mun lalata musu komai, kuma ko da mun bar yaƙin yanzu, zai ɗauke su shekara 20 kafin su sake gina kansu, idan ma za su iya'', in ji Shugaba Trump.

    Ya ƙara da cewa ''kuma hakan ma bai wadatar ba, za mu tabbatar ba su samu makamin nukiliya ba''.

  3. UAE ta umarci ƴanƙasarta su gaggauta ficewa daga Iran da Iraƙi da Lebonon

    Ƙasar Haɗaɗdiya Daular Larabawa ta gargaɗi ƴanƙasarta su gaggata ficewa daga ƙasashen Iran da Iraƙi da kuma Lebonon, sakamakon halin da ake ciki a ƙasashen.

    Sai dai ƙasar ba ta yi cikakken bayanin dalilan ficewar ba, kuma babu tabbas kan abin da sanarwar ke nufi.

  4. INEC ta mayar da sunan David Mark matsayin shugaban ADC a shafinta

    David Mark

    Asalin hoton, David Mark

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta mayar da sunan Sanata David Mark matsayin shugaban jam'iyyar ADC a shafinta na intanet.

    Matakin na zuwa ne bayan hukuncin Kotun Kolin ƙasar da ya soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ya buƙaci INEC ta cire sunan Davida Mark ɗin daga shafinta.

    A ranar Alhamis ne Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar ADC ɓangaren Sanata David Mark.

    A hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin mai shari'a Mohammed Lawal Garba, ta ce masu ƙarar su koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'ar da ake yi.

    Alƙalan sun kuma yi watsi da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na cewa a tsaya inda ake a shugabancin ADCn kafin shigar da ƙara da NAfiu Bala Gombe ya yi a gaban Babbar Kotun Tarayya.

  5. Iran ta mayar wa ƙasashen yankin Gulf martani

    Jakadan Iran na dindindin a Majlisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani ya mayar wa ƙasashen yankin Gulf martani kan wasiƙar da suka rubuta wa Babban Sakataren MDD domin nuna adawa da hare-haren da Iran ke kai musu.

    Mista Iravani ya ce ƙasashen na yankin Gulf sun taimaka wajen kai wa ƙasarsa hare-hare ta hanyar bai wa Amurka damar kafa sansanonin soji a ƙasashensu, waɗanda daga can ne take ƙaddamar da hare-harenta kan Iran.

    Cikin wasiƙar martanin da ya rubuta, jakadan na Iran ya ce ƙasarsa na aikata abin da ya kira ƴancinta na kare kai, kamar yadda dokokin MDD suka tanatar, ''domin mayar da martani ga hare-haren''.

    ''Ba Iran ce ta fara yaƙin ba, kuma bayar da dama a yi amfani da ƙasarsu ko ruwansu ko sararin samaniyarsu domin kai wa Iran hari, ya nuna cewa suna da hannu, kuma dole a rama musu biki'', kamar yadda Mista Iravani ya rubuta cikin wasiƙar martanin.

    Tun da farko, ƙasashen Saudiyya da Qatar da UAE da Jordan da Bahrain da Kuwait a cikin wasikar tasu ga Kwamitin tsaron na MDD sun zargi Iran da saɓa wa ƴancin ƙasshensu na kai musu hare-hare, tana mai kiran MDD ta yi Allah wadai da hare-haren.

  6. 'Amurka za ta ɗauki lokaci kafin sake ƙera manyan makaman da ta yi asara a yaƙin Iran'

    Sakataren tsaron Amurka

    Asalin hoton, EPA

    Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegsett ya bayyana wa mambobin majalisar dattawan Amurka cewa ƙasar za ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin ta sake ƙera manyan makaman da ta yi asara a yaƙin Iran da sauran hare-haren soji da ta riƙa kai wa a ƴan shekarun nan.

    Yayin da yake jawabi a zauren majalisar lokacin kare kasafin kuɗin ma'aikatarsa, Mista Hegsett ya ce zai iya ɗaukar ''watanni ko ma shekaru'' ya danganta da nau'in makaman.

    Sanata Mark Kelly daga jihar Arizona ya tambayi sakaten tsaron cewa, zuwa wane lokaci za a iya maye gurbin makaman da aka lalata a yaƙin?

    Mista Hegsett ya amsa da cewa ''a mafi yawan hare-haren, mun yi amfani da manyan makamai, da kuma na kakkaɓo makamai, don haka mun lalata da yawansu, kuma waɗannan ba makamai ba ne da za ka iya ƙerewa a rana guda ba''.

    Sanata Kelly ya ƙara da cewa buƙatar kasafin kuɗin da ma'aikatar ta gabatar wa majalisar ya nuna cewa ma'aikatar tsaron ƙasar na da hujjar hakan, sannan ya yi kiran samar da takamamman lokacin maye gurbin makaman.

    Sai dai sakataren tsaro ya jaddada cewa aikin zai ɗauki watanni zuwa shekaru, ya danganta ne kawai da nau'in makaman.

  7. 'Yaƙin Iran ya haifar da mummunar tsadar takin zamani a duniya'

    Manomi na zuba takin zamani a gona

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ɗaya daga cikin manyan kamfanonin samar da takin zamani a duniya, Svein Tore Holsether ya ce, katsewar da aka samu a aikewa da takin a sakamakon yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran na haifar da matsala ga harkar samar da a abinci a duniya.

    Shugaban kamfanin samar da taki na Yara ya faɗa wa BBC cewa a yanzu ba a iya yin takin zamanin, har tan rabin miliyan ba a duniya - kuma wannan zai fara shafar ƙasashe matalauta.

    Wajen kashi ɗaya bisa uku na kasuwancin takin zamani na duniya da kuma sinadaran da ake yin takin da su na wucewa ne ta Mashigar Hormuz - wadda har yanzu a iya cewa a rufe take sakamakon yaƙin.

    Farashin takin zamanin a yanzu ya ƙaru da kashi 80 cikin 100 tun bayan da yaƙin ya ɓarke.

  8. Wa'adin Trump na samun izinin majalisar Amurka don ci gaba da yaƙin Iran ya wuce

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images

    Wa'adin Donald Trump na samun izini daga majalisar dokokin Amurka, don ci gaba da yakin da yake yi da Iran ya wuce.

    A ƙarƙashin kundin tsarin mulkin Amurka, dole ne gwamnati ta samu amincewar majalisar dokokin cikin kwana 60, da shugaban ya sanar da majalisar kai hare-hare a kan Iran ko kuma, ya dakata da kai harin.

    To sai dai Sakataren tsaron ƙasar, Pete Hegseth, ya ce ba dole ba ne, Shugaban ya bi tanadin dokar ta yaƙi, saboda yarjejeniyr dakatar da buɗe wuta da aka yi da Iran, ta dakatar da lokacin, duk wani tanadi da wannan doka.

    Iran a nata ɓangaren ta ce ci gaba da Amurka ke yi da datse tashoshin jiragenta na ruwa, ya saɓa wa yarjejeniyar.

  9. Ƙasashen Sahel sun ce sun zafafa hare-hare kan JNIM a Mali

    Shugabannin mulkin sojin ƙasashen sahel

    Asalin hoton, @GoitaAssimi

    Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta ce wata rundunar haɗaka ta ƙasashe uku - Nijar da Burkina da Mali, na kai hare-hare masu tsanani ta sama a yankunan ƙasar Mali, a matsayin martani na hare-haren da mayaƙa masu ikirarin jihadi da Buzaye 'yan aware suka kai Mali.

    Akwai shakku a kan ƙarfin gwamnatin mulkin soji ta Mali, bayan da sojojin suka rasa iko da yankuna da dama masu muhimmanci.

    A wata sanarwa da ta fitar bayan taron majalisar zartarwa a babban birnin Nijar ɗin Yamai, gwamnatin Nijar ta ce, an fara kai hare-haren ne 'yan sa'o'i bayan da haɗakar ƙungiyoyin suka ƙaddamar da hari a kan Mali, inda suka kama yankuna da dama masu muhimmanci a ƙarshen mako.

    Dukkanin ƙasashen uku dai na ƙarƙashin mulkin soji ne.

    Kuma a shekarar da ta wuce ne suna ƙirƙiro wata rundunar soji ta haɗin gwiwa domin yaƙar masu tayar da ƙayar baya a ƙasashen nasu.

    Tun da farko ƙungiyar JNIM mai alaƙa da al-Qaeda ta yi kira ga al'ummar ƙasar ta Mali da ta haɗe kai domin kawo karshen gwamnatin sojin ƙasar.

  10. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirara da Hajji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.