Yadda Fulani ke mutuwa a wani sansani da aka tsare su a jihar Kwara - Amnesty

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'Adam ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta hanzarta gudanar da bincike game da rahotannin da ke cewa akalla mutum 150, galibi yara ƙanana, sun mutu a wani sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima ( NYSC) da ke Yikpata a jihar Kwara.
Amnesty ta ce mutanen sun rasu ne sakamakon mummunan yanayi da wahalhalu da suke ciki.
Sai dai hukumomin sojan Najeriya sun yi watsi da wannan zargi da cewa ba shi da makama.
Mutanen da suka rasu na cikin Fulani makiyaya kimanin 1500, wadanda aka killace a sansanin na NYSC, bayan da aka sami karuwar hare-haren 'yan bindiga.
Isa Sanusi, wanda shi ne daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, ya ce lamarin dai ya yi ƙamari ne bayan da sojojin Najeriya sun bayar da wani umarni a cikin watan Janairu, saboda yadda tsaro yake sake taɓarɓarewa a jihar Kwara.
Sojojin ya ce sun umarci al'ummar Fulani makiyaya da ke cikin ƙauyukan da dazuka da su futo idan har sun san su ba yan bindiga ba ne su taru a waje guda.
"Da suka futo a waje daya da iya abin da suka iya dauka na dukiyoyinsu, aka kwashe su aka kai su wajen sansanin masu bautawa ƙasa yau fiye da wata uku, kuma daga bayanan da muke samu, daga wajen lamarin babu daɗi," a cewar Isa Sanusi.
Isa Sanusi ya ce bincikensu ya gano cewar Fulanin na zaune ne cikin yanayin cunkoso da ƙarancin kulawa ta lafiya, da rashin tsafta da rashin isashen abinci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Yara da yawa na kamuwa da cutar yunwa, cikin mutum ɗari da hamsin da suka mutu, sittin daga cikinsu yara ne ƙananan. Sannan akwai mata da muka tantance kusan su 100 da suke da juna biyu a sansanin, wadanda kuma akwai haɗarin ba za su sami kulawar da mace mai juna biyu ke buƙata ba, ita da abin da ta ke dauke da shi ba kafin da bayan sun haihu," in ji shugaban na Amnesty.
Haka kuma Isa Sanusi ya ce duk da cewar ana cewar an killace su a wannan sansani ne saboda tsaro, in dai don matslar tsaro ne ya kamata a ce tun daga watan Janairu zuwa yanzu an kammala bincike ko shawo kan al'amarin, amma sun rasa me ya sa har yanzu aka ajiye su a inda suke a halin yanzu.
"Mutanen nan sun bar gidajensu, da shanunsu, da sauran dukiyoyinsu, bai kamata a ce suna hannun gwamnati amma su tsinci kansu a cikin mawuyacin hali ba haka, wanda doka cewa ta yi bai kamata a tsare mutum sama da sa'o'i 24 ba, ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, wannan zalunci ne," in ji Isa Sanusin.
Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kai wa Fulanin dauki, musmaman ganin su ma sun fuskanci tsangwama da hare-hare daga 'yan bidiga da ke satar mutane don neman kuɗin fansa
Ko a farkon watan Afirilu da ya kare sai da wasu al'ummomin Fulani a yankin Lafiagi da Patigi da Gugu a jihar ta Kwara suka koka kan yadda suke fuskantar barazanar kora daga muhallinsu na iyaye da kakanni.
A lokacin an bai wa al'ummomin Fulanin wa'adin zuwa ranar 14 ga watan Afirilun da ya wuce da su fice su bar wuraren, idan kuma ba haka ba duk abin da ya same su, su suka nema a cewar shugaban matasan Fulatanin yankin.











