Yadda aka ba Fulani wa'adi su bar wasu garuruwa a jihar Kwara

Wani Bafulatani makiyayi da shanunsa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A jihar Kwara da ke cikin yankin kudancin Najeriya, wasu al'ummomin Fulani a yankin Lahiyaje da Patigi da Gugu sun ce suna fuskantar barazanar kora daga muhallinsu na iyaye da kakanni.

An baiwa al'ummomin Fulanin wa'adin kwana uku da ke karewa a ranar Talatar nan 14 ga watan Afirilu, 2026 da su fice su bar wuraren, idan kuma ba haka ba duk abin da ya same su, su suka nema a cewar shugaban matasan Fulatanin yankin, Abdulahi Mohammed a tattaunawar da ya yi da BBC.

Ya ce a dalilin haka tuni suka shiga yanayi na tashin hankali ganin yadda har aka shiga kone muhallinsu.

''Fulaninmu da ke yankin gaba daya an ba mu kwana biyu zuwa uku, an ce mu tashi, kuma duk wanda bai tashi ba an ce to yana cikin matsala kuma duk abin da ya same shi to ya kuka da kanshi.

''Kuma mutanenmu in sun taho za su shiga gari, mutum ba mai laifi ba, zai je gari ya yi larurarsa sai ma'aikata - sojoji da 'yanbanga su hadu da kai su caje ka su tafi da kai su je su kashe kuma kai ba mai laifi ba.

''Gaba daya Fulaninmu an cinye musu abinci an kone musu gidaje, sun tarwatse. Mutanenmu suna nan suna ta gudu. Tun daga ranar Lahadi mutanenmu su duk sun tarwatse, mutanenmu suna nan suna ta gudu,'' in ji shi.

Shugaban ya kara da cewa su ba baki ba ne, wasunsu sun kai shekara talatin zuwa arba'in a wannan yanki amma duk an ba su umarni a kan su tashi.

Haka nan shi ma wani Bafulatanin ya ce su a nan wajen ma aka haife su, amma duk da haka an watsa su.

''Ina tare da iyalina, amma dai duk an ce mu tashi, mutane suna ta gudu. Abubuwan ba dadi. Idan abin ya yi kamari dole mu gudu mu ma. Abubuwan ne babu dadi.'' A cewarsa.

Dangane da cewa ko sun sanar da hukumomi a halin da suke ciki. Sai ya ce:

''To shugabannin namu ma, in dai ba na cikin gari ba, duk wanda yake cikin daji kowa ya gudu. Mu ma ai dole mu gudu, tun da mutum ba zai tsaya ba, ai dole ya gudu.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana dai zargin Fulanin suna bayar da mafaka ga Fulani masu kai hare-hare kan al'ummomin a wannan yanki na jihar ta Kwara.

A kan wannan zargi sai ya ce: ''Wallahi wadanda ke kai hare-haren nan fa, akwai su, amma kuma wadanda ake yi wa wanga shashanshi wallahi ba masu kai hare-haren ne ba. Masu kai hare-haren nan wallahi ba a zuwa wajensu.''

''To yanzu mutum ya fi karfinka ya za kai da shi? Ka na da ikon da ka ka kora tai?''

Game da maganar ko suna sanar da hukumomi idan sun ga miyagun sun zo sun zauna a inda suke, sai ya ce: ''To ko da mun gaya wa hukuma, ma'aikaci ya zo ya na harba bindiga daga nesa, su kuma miyagun sun gudu. Kai da ka kira ma'aikatan sun dawo sun kashe ka, to me ka yi?''

Daga ɓangaren hukumomin Fulanin dai, suna kira ga hukumomi da su kawo musu ɗauki don gyara wannan lamari na wannan mawuyacin hali da Fulanin suka ce suna ciki a kan wannan umarni da aka ba su, su tashi.

Duk wani ƙoƙari da BBC ta yi na kira domin ji daga hukumomin tsaro na 'yansanda dangane da wannan lamari ya ci tura, kasancewar duk wayar da aka buga musu sun ki dauka.