Yaƙin Iran da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 06/06/2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Ba mu fuskanci turjiya daga Rasha ba wajen ƙaddamar da harin St. Petersburg - Ukraine

    Kwamandan dakarun Ukraine da ya kai harin jirgin sama marar matuƙi a St. Petersburg da ƙauyukan kusa da shi ya ce babu wata turjuya da suka fuskanta daga Rasha a lokacin harin.

    Yevhen Karas ya ce cikin sauƙi suka ƙaddamar da hare-haren nasu, ba tare da wani martani daga Rasha ba.

    Wakilin BBC ya ce Rundunar sojin Ukraine ta ce harin nata ya faɗa kan wuraren ajiyar makamai da barikin sojin ruwa da kuma wata matatar mai a yayin harin. Ukraine dai ta harba ɗaruruwan makamai a cikin birni na biyu mafi girma a Rasha.

  2. Sojojin Najeriya sun ce sun tseratar da matafiya 23 daga masu garkuwa a Kogi

    Soja

    Asalin hoton, TWITTER/@HQNIGERIANARMY

    Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta ce jami'anta sun samu nasarar tseratar mutum 23, waɗanda ta ce matafiya ne da ƴanbindiga suka tare a babbar hanyar Ayegunle zuwa Bunu da ke jihar Kogi, kamar yadda jaridar Guardian mai zaman kanta ta ruwaito a ranar Asabar 6 ga Yuni.

    Rahotanni sun bayyana cewa ƴanbindiga sun tare hanyar ne domin sace mutane, amma sojoji suka kai agajin gaggawa bayan sun samu kiran kar-ta-kwana, inda suka isa wajen cikin lokaci suka fatattaki ƴanbindigar tare da tseratar da matafiyan.

    Rahoton ya ƙara da cewa maharan sun tsere da suka ga isowar sojoji, "amma duk da haka sojojin sun bi bayansu domin farautarsu a cikin dajin."

    Sai dai jaridar ta ruwaito cewa mutum biyu sun rasu harin, sannan wasu biyar sun samu rauni.

  3. KACRAN ta buƙaci manoma da makiya su zauna lafiya

    Khalil Moh’d Bello

    Asalin hoton, Khalil Moh’d Bello

    Ƙungiyar makiyaya ta Kulen Allah Cattle Rearers Association of Nigeria (KACRAN) ta yi kira ga manoma da makiya da su girmama ta hanyar kiyaye tsakanin gonaki da gandun daji da burtulai da aka ware domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar baki ɗaya.

    KACRAN ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannu Khalil Moh’d Bello, inda ta ce a shirye take ta cigaba da shigewa gaba domin samar da hanyoyin da za a zauna lafiya tsakanin manoma da makiya.

    "Daminar bana ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya. Wannan ya sa a matsayinmu na ƙungiya mai son zaman lafiya muke ta ƙoƙarin ganin mun wayar da kan mutane muhimman zaman lafiya," in ji shi.

    Ƙungiyar ta ce daga cikin hanyoyin da za a bi domin inganta zaman lafiya akwai girmama juna, inda ta ce akwai buƙatar, "manoma su guji cinye burtalai, sannan makiyaya su guji shiga gonaki," in ji ta, sannan ta ce hakan zai samar da zaman lafiya, sannan manoma su yi noma ƙasar ta samu abinci.

    A ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi su samar wa manoma da kayan noma cikin rahusa, sannan a ƙwato tare da sake mayar da gandun daji domin makiyaya su samu wurin kiwon dabbobinsu ba tare da shiga gonakin manoma ba.

  4. Dodannin raga – Ƴanwasan da ake sa ran za su fi zura ƙwallo a 2026

    Wasa

    Asalin hoton, BBC Sport

    Kylian Mbappe ya kasa yin murmushi a lokacin da yake karɓar ƙyautar takalmin zinare bayan kammala gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

    Tawagar Faransa ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Argentina, duk da cewa ya ci ƙwallo uku rigis a ranar. Cin ƙwallaye ba sa tabbatar da lashe kofi, amma suna da tasiri ga wanda ya zura su a raga da yawa a kowacce gasa.

  5. Iran ta zargi Amurka da hana 'ma'aikatan tawagar ƙwallonta' biza

    Iran ta zargi Amurka da hana wasu mutane da ta ce suna da "muhimmanci" bizar shiga ƙasarta domin halartar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya.

    Iran ta yi zargin ne awanni kaɗan bayan Washington ta amince ba ƴanwasan tawagar ƙasar damar shiga domi fafatawa a wasannin gasar.

    Hukumomin Amurka sun ce an ba ƴanwasan ne biza, sai kuma wasu waɗanda ta bayyana da "ma'aikatan da suka fi muhimmanci ga watagar," a ranar Juma'a, kimanin kwana 10 kafin wasan farko na Iran a birnin Los Angeles a ranar 15 ga watan Yuni.

    Haka kuma Amurka ta ce ba za ta bari Iran "ta shigar da ƴanta'adda ƙasarta ba."

    Ofishin jakadancin Iran na Turkiyya dai ya zargi Amurka da katsalanda a harkokin wasanni, inda ta ce an hana wasu muhimman mutane zuwa ƙasar domin taimakon tawagar.

  6. Wace ƙasa kuke goyon baya a gasar Kofin Duniya?

    Matan da ke aiki a BBC sun bayyana ƙasashen da suke goyon baya don lashe wannan babbar gasa.

    Bayanan bidiyo, Wace ƙasa kuke goyon baya a gasar Kofin Duniya?
  7. Iyalai 10 mafiya arziki a duniya

    Arziki

    Asalin hoton, Reuters

    Iyalai 10 mafi arziki a duniya sun mallaki ɗaruruwan biliyoyin daloli ta hanyar mallakar kamfanonin dillanci da saye da sayarwa, da ikon gudanar da dukiyar ƙasa da kuma mallakar manyan gine-gine na gani na faɗa.

    A cewar shafin Investopedia mai bibiyar harkokin kuɗi da zuba jari a duniya, tasirin iyalai masu arziki yana jaddada wata al'adar ta martaba kuɗi da dukiya a duniya.

    Waɗanda ke kan gaba a harkokin kasuwanci manya ne a idon mutane da yawa, kuma ana yanke masu hukunci ne kan dagewar su wajen ci gaba da nuna ɗaukaka ko kuma idan suka gaza yin hakan, saboda ana masu Kallon fitattu da suka kai ƙololuwar shahara.

  8. Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta

    Iran da Amurka

    Asalin hoton, Getty images/Tasnim

    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka ta kai a gaɓar tekun yankin Sirik da tsibirin Qeshm,” inda ta bayyana hakan a matsayin “keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta 10 ga Afrilu da aka cimma.

    A cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar ta ce “ci gaba da nuna ƙiyayya da tsokana daga gwamnatin Amurka” na nuna rashin bin dokokin ƙasa da ƙasa da kuma Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ta ƙara da cewa hakan na nuna cewa “Amurka ba ta da niyyar rage tashin hankali ko komawa hanyar zaman lafiya mai ɗorewa.”

    Sanarwar ta jaddada cewa Iran na da cikakken haƙƙin kare kanta, tare da kira ga ƙasashen yankin da su mutunta ƙa’idar kyakkyawar makwabtaka, tare da gargaɗin kada su bari “ɓangarorin da ke da mugun nufi” su yi amfani da “ƙasashensu ko wuraren aikinsu” wajen kai hare-hare.

    A gefe guda, dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari kan sansanin sojin Amurka da ke Kuwait da kuma hedikwatar Rukuni na Biyar na rundunar sojin ruwa ta Amurka a Bahrain da makamai masu linzami da jiragen marasa matuƙa.

    Sai dai sojojin Amurka, Kuwait da Bahrain sun ce sun yi nasarar kakkao dukkanin makaman da aka harba.

    Kuwait da Bahrain sun kuma yi allawadai da harin da Iran ta kai.

  9. Ana ci gaba da kwashe ‘yan ci-rani daga Afirka ta Kudu bayan ƙarin hare-hare

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana ci gaba da kwashe ‘yan ci-rani daga Afirka ta Kudu bayan ƙarin hare-hare da tashin hankali da ta shafe su a wasu yankuna na ƙasar.

    Rahotanni sun ce kusan mutane 140, mafi yawansu daga Malawi da Mozambique, ana mayar da su gida ta motoci bayan sun shafe kusan mako guda suna fakewa a wani ɗakin taro a garin Kleinmond da ke lardin Western Cape.

    Waɗannan mutane na cikin sama da 400 da aka ajiye a matsugunan wucin gadi a yankin Overstrand, bayan rikice-rikicen da suka tilasta musu barin gidajensu.

    Mozambique ta ce ta riga ta karɓi sama da ‘yan ƙasarta 500 da aka mayar gida, yayin da Ghana ke shirin tura ƙarin rukuni bayan ta riga ta kwashe kusan 300 a baya.

    Ita ma Najeriya ta ce sama da ‘yan ƙasarta 1,000 sun yi rajista domin komawa gida da kansu.

    A nata ɓangaren, gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce za ta tura wakilai zuwa ƙasashen Afirka domin tattaunawa kan lamarin, yayin da wasu ƙungiyoyin adawa da ƴan ci-rani e ci gaba da neman a fitar da duk wanda ba shi da takardun zama a ƙsar kafin ƙarshen watan Yuni.

  10. Iran ta zargi Amurka da hana jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Iran ta zargi Amurka da hana wasu muhimman jami’an tawagar ƙwallon ƙafarta shiga ƙasar, bayan ta amince wa ‘yan wasan da wasu ma’aikatan tawagar bizar halartar Gasar Kofin Duniya ta 2026.

    Iran ta ce an ƙi bai wa da dama daga cikin jami’an gudanarwa da masu ba da shawara biza, lamarin da ofishin jakadancinta da ke Turkiyya ya bayyana a matsayin tsoma baki a harkokin wasanni saboda dalilai na siyasa.

    Sai dai Amurka ta ce ta bai wa ‘yan wasan da ma’aikatan da ake buƙata biza, tare da jaddada cewa ba za ta bari a yi amfani da tsarin gasar wajen shigar da mutanen da ake zargi da alaƙa da ta’addanci ba.

    Iran ta kuma yi kira ga FIFA da ta shiga cikin lamarin, yayin da rahotanni daga Iran suka ce shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar da mataimakinsa na cikin waɗanda aka hana shiga Amurka.

    A makon nan, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce ba za a amince da mutanen da ke da alaƙa da dakarun IRGC su shiga cikin tawagar ƙwallon ƙafar Iran ba.

    Iran za ta buga wasanta na farko a gasar da za a yi a Amurka da Canada da Mexico ranar 15 ga Yuni a Los Angeles.

  11. Gyaran hanyoyi zai rage matsalolin tsaro a arewa - Goje

    Danjuma Goje

    Asalin hoton, Danjuma Goje

    A Najeriya yayinda matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara, ɗaya daga cikin jiga-jigan siyasa a shiyar arewa maso gabashin ƙasar, wato tsohon gwamnan Gombe, kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya Muhamad Danjuma Goje, ya ce ɗaya daga cikin dalilan da ke ƙara rura wutar matsala shi ne rashin hanyoyin sufuri.

    A cewar sanatan, ya jima yana jan hankali da neman ganin an inganta hanyoyin jihohin yankin don shawo kan matsalar, kuma da alama a yanzu shugaban kasa ya ji kokensu, la'akari da yadda ya bada kwangilar soma aikin wasu muhimman hanyoyi a yanzu.

    A cewarsa, ya ji daɗi a shugaban ƙasa ya amince da fara aikin tagwayen hanya daga Akwanga zuwa Jos zuwa Bauchi zuwa Gombe. "Da ya yi wannan ne sai na sake tashi na yi godiya, sannan na nemi a isar da hanyar ta kai Biu zuwa Maiduguri. Sannan na nemi a yi daga Gombe a yi tagwayen hanyar zuwa Yola ta ratse zuwa Jalingo. Idan an yi haka arewa maso gabas an mana komai."

    Goje ya ƙara da cewa ya ji daɗi da ya ga har an je an duba aikin, saboda a cewarsa, "maganar gyara hanya na da muhimmanci, saboda masu ɓarna sun fi yi a wuraren da hanya babu kyau. Idan an gyara hanya, hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a arewa musamman arewa maso gabas."

  12. Akpabio ya musanta ɗaukar alƙawarin nema wa sanatoci tikitin takarar komawa majalisa

    .....

    Asalin hoton, Godswill Akpabio

    Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi alƙawarin bai wa ‘yan majalisar dattawa da suka fadi zaɓen fidda-gwani na jam’iyya tikitin takarar sanata kai tsaye na komawa majalisa.

    A cikin wata sanarwa daga ofishinsa, ya ce abin da ya yi shi ne nuna tausayawa ga ‘yan majalisar da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa shugabancin jam’iyyar APC na duba rikice-rikicen da suka taso daga zaɓukan fidda-gwani.

    Mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Eseme Eyiboh, ya ce Akpabio bai yi wani alƙawari na ba da tikiti ba, kuma rahotannin da ke yawo ba su da tushe.

    Ya kuma jaddada cewa Majalisar Dattawa za ta ci gaba da yin aiki cikin bin doka da tsarin jam’iyya, ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar APC ba.

  13. Iran ta yi barazanar rufe Mashigar Hormuz gaba ɗaya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran ta yi barazanar cewa za ta iya rufe Mashigar Hormuz gaba ɗaya ga jigilar mai da iskar gas, a yayin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka a yankin Tekun Fasha.

    Ta ce wannan mataki na iya zama martani idan Amurka ta ci gaba da abin da ta kira “ayyukan da ba su dace ba”.

    Barazanar ta biyo bayan musayar wuta da aka samu, inda Amurka ta ce sojojinta sun kai hari kan wasu na’urorin sa ido a yankunan gaɓar teku na Goruk da Qeshm.

    A gefe guda kuma, IRGC ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain da Kuwait.

    Sai dai rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta bayyana cewa an kakkabo makaman ko kuma ba su kai ga inda aka nufa ba.

    Rahotanni na ci gaba da nuna fargaba a kasuwannin makamashi, yayin da Mashigar Hormuz ke zama muhimmiyar hanyar da ake jigilar kaso mai tsoka na man fetur da iskar gas na duniya, abin da ke sa barazanar rufe shi ta janyo damuwa a ƙasashen da suka dogara da wannan hanya.

  14. 'ICPC ta hana El-Rufai damar samun kulawar asibiti'

    .....

    Asalin hoton, Muyiwa Adekeye/X

    Mai ba tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya zargi hukumar ICPC da hana shi damar samun kulawar asibiti yayin da yake tsare.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce El-Rufai ya koka kan matsalar idanusa suna ƙaiƙayi da kumburi, inda ya nemi a kai shi asibiti domin duba lafiyarsa, amma jami’an ICPC suka ƙi amincewa da bukatar.

    Ya bayyana cewa an riga an kai shi asibitin ido a ranar 4 ga watan Yuni, amma daga baya yanayin idon ya ƙara taɓarɓarewa, abin da ya jawo damuwa ga iyalansa.

    A cewarsa, jami’an ICPC sun ga halin da idanuwansa ke ciki, amma ba a shirya masa ƙarin kulawar likita ba, abin da ya ce ya ƙara dagula lamarin.

    Ya kuma zargi hukumar da bayar da bayanan da ba su dace ba ga iyalan El-Rufai, inda aka ce bai nemi ganin likita ba, zargin da ya ce ba gaskiya ba ne.

    Adekeye ya kuma ce akwai umarnin kotu da ke ba El-Rufai damar samun kulawar lafiya, amma har yanzu ba a bi umarnin yadda ya kamata ba.

    ICPC dai ba ta mayar da martani kai tsaye kan waɗannan zarge-zarge ba, yayin da batun ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.

  15. Matatar Dangote ta ƙara yawan fetur da take samarwa zuwa ganga 700,000 a rana

    Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan man fetur da take samarwa da kuma rabawa gidajen mai a Najeriya, bayan da ƙarfin tace danyen man da take yi ya kai ganga 700,000 a rana.

    Matatar, wadda babban attajirin ɗan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote ya mallaka, ta fara samar da man fetur ne a shekarar 2024, kuma tun daga lokacin take ci gaba da ƙara yawan samar da fetur, dizal, man jiragen sama da sauran kayayyakin man da aka tace.

    Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin isar da fetur zuwa gidajen man da ke haɗin gwiwa da matatar, musamman na MRS, tsakanin ranar Juma'a da safiyar Asabar.

    A makon da ya gabata, matatar ta sanar da rage farashin fetur daga naira 1,275 zuwa naira 1,250 kan kowace lita a farashin da take sayarwa ga dillalai, yayin da ta rage farashin dizal daga naira 1,800 zuwa naira 1,700 kan kowace lita.

  16. Iran ƙasa ce mai ƙarfi da girman kai shiyasa ba ta amince da yarjejeniya ba - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa har yanzu Iran ba ta amince da yarjejeniyar da Washington ta gabatar ba saboda ita ƙasa ce mai ƙarfi kuma mai girman kai.

    Da yake amsa tambaya daga mai gabatar da shirin Meet the Press na NBC, Kristen Welker, Trump ya ce ba abu ne mai sauƙi ga Iran ta amince da wasu daga cikin buƙatun Amurka ba.

    Trump ya kuma yi ikirarin cewa Iran na da kusan kashi 21 zuwa 22 cikin 100 ne kawai na makamanta masu linzami da suka rage.

    Ya ce Amurka ta san kusan adadin sauran makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da Iran ke da su, da kuma wuraren da ake ajiye su.

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa mafi yawan cibiyoyin kera makamai masu linzami, masana'antun jiragen yaƙi marasa matuƙa, da wuraren harba makamai na Iran sun lalace.

    Sai dai ya ce har yanzu Iran na da wasu makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    Duk da haka, Trump ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran za ta kai ga cimma matsaya, ko da yake ya amince cewa samun yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu har yanzu abu ne mai wahala.

  17. Mun kai harin martani kan sansanonin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce dakarun juyin juya halin ƙasar (IRGC) sun kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya da makamai masu linzami na rundunar sararin samaniyarta.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya bayyana cewa harin ya zo ne a matsayin martani ga abin da ya kira "ta'addancin soji" da Amurka ta aiwatar a Sirik da tsibirin Qeshm na Iran.

    A cewar sanarwar, an kai hare-haren ne kan sansanonin da Iran ta bayyana a matsayin na "abokan gaba" da ke yankin da makamai masu linzami.

    Rahotanni sun ce Iran ta zargi Amurka da kai hari kan wani hasumiyar sadarwa a kudancin tsibirin Qeshm, lamarin da ya haddasa wannan martani daga Tehran.

    Sai dai rundunar CENTCOM ta Amurka ta bayyana hare-haren da ta kai a yankin a matsayin matakan kariyar kai, yayin da rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da ƙara tsananta duk da ƙoƙarin sasanta rikicin.

  18. Assalamu alaikum!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Asabar,

    Aisha Bababngida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za kuma ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.