Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Juventus ta fara zawarcin Alisson, Real Madrid na harin Emery
Juventus na Italiya ta sanya golan Liverpool Alisson kan gaba a jerin an wasan da za ta yi zawarcinsu a bazara. Ɗan wasan na Brazil mai shekara 33 na shirin shiga shekarar ƙarshe ta kwantiraginsa a Anfield. (Sky Sports)
Kocin Aston Villa Unai Emery na cikin jerin sunayen waɗanda Real Madrid ke nazari su zama sabon kocinta, amma ya na da kwantiragi da ƙungiyar ta gasar Premier har zuwa bazarar 2029. (Talksport)
Manchester United na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Portugal, Mateus Fernandes, mai shekara 21, wanda ake sa ran zai bar West Ham idan ta faɗo daga gasar Premier zuwa matakin Championship. (Telegraph)
Har ila yau Manchester United na son sayar da ɗan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekaru 25 ya fara buga wasan lig sau ɗaya kacal tun lokacin da aka naɗa Michael Carrick a matsayin kocin riƙon ƙwarya a watan Janairu. (Sun)
Manchester United ta shirya kashe fam miliyan 150 don siyan gogaggun ƴan wasan tsakiya guda uku a wannan bazarar. (Mail)
Brentford na zawarcin ɗan wasan bayan Red Bull Salzburg ɗan ƙasar Austria Jannik Schuster, mai shekara 19, inda ta fara tattaunawa kan cinikin kusan fam miliyan 16. (Mail)
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Inter Milan ta amince da kudirin Yuro miliyan 15 (£13m) domin siyan ɗan wasan Manchester City Manuel Akanji bayan da ta lashe gasar Seria A. Ɗan wasan baya na ƙasar Switzerland mai shekaru 30 ya koma Italiya a matsayin aro a bara. (Fabrizio Romano)
Liverpool da Arsenal na daga cikin ƙungiyoyin da ke sa ido kan ɗan wasan gaban Paris St-Germain da Faransa Bradley Barcola, mai shekara 23. (Teamtalk)
Chelsea na zawarcin ɗan wasan bayan Club Brugge ɗan ƙasar Ecuador Joel Ordonez, mai shekara 22, wanda a baya aka alaƙanta shi da komawa Liverpool a cinikin fam miliyan 43 a watan Janairu. (Teamtalk)
Inter Milan ta gargaɗi Barcelona game da zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan bayan Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 27, bayan ta kammala lashe gasar Serie A. (ESPN)