Nawa sojan Najeriya da ke bakin daga zai riƙa karɓa a wata?

Asalin hoton, Getty Images
Bayan sanarwar da gwamnatin Najeriya ta fitar a a makon da ya gabata cewa za ta ƙara albashin jami'an rundunonin sojin ƙasar da kashi 30 da 50 da 80 cikin 100, mutane da dama sun bayyana matakin a matsayin ci gaba mai kyau.
A wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, ya fitar, ya ce kusan jami'an soji 250,000 ne za su amfana da wannan ƙarin albashi.
Ya ce ƙarin zai ƙara Naira biliyan 26 a kan kuɗin da gwamnati ke warewa domin biyan albashin sojoji, inda jimillar kuɗin za ta tashi daga Naira biliyan 660 zuwa biliyan 924 a kowace shekara.
"Dole ne a tallafa wa maza da mata da ke taimaka mana wajen kula da tsaronmu, tare da nuna godiya gare su yayin da suke gudanar da ayyukansu na yi wa ƙasa hidima," in ji Tinubu a cikin sanarwar.
Nawa ne sabon albashin sojojin zai kasance?
BBC ta yi wasu ƙididdiga domin hasashen yadda sabon albashin jami'an sojin Najeriya zai kasance.
Rundunonin sojin Najeriya sun ƙunshi sojojin ƙasa da sojin sama da na ruwa. Duk da cewa sunayen muƙamansu sun bambanta, muƙaman suna da daidaito, kuma albashinsu yana cikin kusan irin wannan tsari.
Misali, mafi ƙarancin matsayi a sojojin ƙasa shi ne kurtu da ake kira 'Private', yayin da makamancinsa a rundunar sojin ruwa shi ne Ordinary Seaman (OS), sannan a ojin sama shi ne Aircraftman/Aircraftwoman (ACM).
A cewar Statisense, wata cibiya mai nazarin ƙididdiga a Najeriya, albashin da jami'in da ke matsayin farko yake karɓa a yanzu shi ne kusan Naira 104,000 a wata.
Wani jami'in soji da bai so a bayyana sunansa ba ya tabbatar wa BBC wannan bayani, inda ya ce albashin ƙananan sojin yana tsakanin Naira 103,000 zuwa 105,000.
A cikin sanarwar Onanuga da aka fitar ranar Laraba, gwamnatin ta ce an ƙara albashin jami'an da ke tsakanin matsayin na farko zuwa babban sajen wato Staff Sergeant da kashi 80 cikin 100.
Wannan na nufin sabon albashin mafi ƙarancin matsayi a rundunonin sojin Najeriya zai kasance tsakanin kusan Naira 189,000 zuwa 192,000 a wata.
A shekara, wannan zai kasance kusan Naira miliyan 2.26 zuwa miliyan 2.30.
Nawa sojan da ke fagen daga zai riƙa samu?
Sai dai bayan albashin sojojin, akwai alawus-alawus da ake biyan sojoji a ɓangarori da dama na aikin.
Muhimman alawus guda biyu ne da sojoji suka fi sa rai da za samu, musamma waɗanda suke fagen daga.
Akwai alawus da ake kira da Ration Cash Allowance (RCA), sannan kuma akwai wani allowace da ake kira da 'grumbe'.
Wani soja da ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce allowance da ake biyan sojoji a yanzu shi ne dubu 45.
"Yanzu ana ba mu alawus ɗin naira dubu 45 a matsayin RCA. Shi kuma grumble da ake magana dubu 50 ake ba mu," in ji shi.
Idan aka yi la'akari da abin da ya faɗa, ke nan sojan da ke bakin daga a Najeriya zai samu ƙarin naira 95 a asalin albashinsa.
Sai dai shi RCA na sojojin da ke bakin daga ne ko kum waɗanda aka tura su wani aiki na musamman.
Idan aka haɗa naira ubu 95 kan naira dubu 189, ƙaramin sojan Najeriya da ke bakin daga zai samu naira dubu 284 ke nan.
Nawa manyan hafsoshin soji za su karɓa?
Haka kuma, alƙaluman Statisense sun nuna cewa albashin manyan hafsoshin soji masu matsayi irin na Major Janar da Rear Admiral ko Air Vice Marshal yana kusan Naira miliyan 1.15 a wata a halin yanzu.
Sabon ƙarin albashin da Shugaba Tinubu ya sanar shi ne kashi 30 cikin 100 ga hafsoshi daga Birgediya zuwa janar.
Saboda haka, misali, Manjo Janr zai iya karɓar kusan Naira miliyan 1.49 zuwa miliyan 1.5 a wata.
Wannan na nufin albashinsa na shekara zai kai kusan Naira miliyan 17.9 zuwa miliyan 18.
Shin ƙarin albashi ake buƙata?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa babu shakka inganta walwala da yanayin aiki da albashi na jami'an tsaro na cikin abubuwan da ke taimakawa wajen ƙarfafa masu guiwa da ba su kuzari wajen gudanar da ayyukansu.
Masanin ya ce Idan aka yi la'akari da hatsarin da aikinsu ke saka su ciki na tsaron ƙasa ya kamata albashinsu ya fi na sauran ma'aikata da aƙalla kashi saba'in da biyar cikin ɗari.
A cewar sa, ya kamata akwai tsarin da za a riƙa waiwaye ta yadda albashin zai riƙa ƙaruwa.
Dr Kabir Adamu ya ce bayan batun albashin abu mai mahimmanci shi ne ɓangaren kayan aiki.
"Wani abu da yake tayar man da hankali shi ne yadda za a ce akwai dakaru a filin yaƙi amman suna cikin motocin da ba na sulke ba, hakan kuskure ne kuma hatsari ne sosai," in ji masanin.
Ya kara da cewa duk da kayan aikin su da suka haɗa da makamai da kayan da suke sakawa na kariya da yawan su da juye da ya kamata a ce ana masu da ba da taimakon gaggawa na rashin lafiya da ƙara masu muƙami duk abubuwa ne da za su taimaka wa jami'an tsaro wajen yin aikinsu.










