Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ɗansanda ya harbe wani matashi a Najeriya
- Marubuci, Gift Andrew
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- Lokacin karatu: Minti 3
Hankalin ƴan Najeriya musamman matasa idan ya yi dubu ya tashi sakamakon ganin wani bidiyo da ke waɗari a shafukan soshiyal midiya inda ya nuna yadda wani matashi ke faman roƙon jami'an ƴansanda amma duk da haka suka harbe shi.
Bidiyon wanda sashen Hausa na BBC Pidgin ya gani ya nuna yadda wanda ake zargin mai suna Mene Ogidi yake zaune a ƙasa kusa da motar ƴansanda, inda suka ɗaure hannayensa da ƙafafunsa.
Ƴansanda sun ce al'amarin ya faru ne ranar Lahadi ta ƙarshen mako.
A bidiyon, matashin wanda ke zaune a ƙasa yana roƙon dansandan cewa shi ba shi da masaniyar abun da ake tuhumar sa da shi inda ya ce zai nuna musu mutumin da ya aiko shi domin ya karɓi kaya.
Rahotanni na cewa an dai aiko da wani ƙunshin saƙo ne wanda kuma ake kyautata zaton bindigogi ne a ciki.
Wasu mutanen gari sun ce matashin da aka kashe ɗin ya karɓi ƙunshin kayan da aka aiko to amma sai direban da ya kawo kayan ya fahimci akwai bindiga a ciki shi ne suka tsare shi sannan kuma suka je suka tseguntawa ƴansanda.
Sai dai kuma da zuwan ƴansandan maimakon su kama shi su tafi da shi sai kawai wani ɗansanda ya buɗe masa wuta inda nan take ya kwanta magashiyan.
Bayanai sun nuna cewa kafin harbe wanda ake zargin, ya ta faman kururuwa yana cewa "ofisa ku yi haƙuri zan faɗa muku komai, abokina ne ya yaudare ni. Yana Sapele."
"Ku yi haƙuri, ban san komai ba a kan batun, zan kai ku wurinsa, yana Sapele, zan kai ku wurinsa..ofisa..."
Yayin da yake ci gaba da roƙonsu su kuma suna ta ɗana kunamar bindiga inda wani daga cikin ƴansandan mai sanye da farin kaya ya harbi wanda ake zargin.
Bayan jami'an sun harbi matashin ne kuma sai suka ɗauki gawarsa suka jefa a cikin mota ƙirar Sienna zuwa ofishinsu.
Rahotanni sun ce ƴansandan sun yi ta harbin matashin har ya mutu a ofishinsu.
Wane mataki ƴansanda suka ɗauka?
Rundunar ƴansandan Najeriya ta kama tare da tsare ɗansandan da ya harbe wani matashi har lahira a jihar Delta da ke yankin kudu maso kudancin Najeriya.
A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta tabbatar da cewa jami'inta mai suna Nuhu Usman ya yi harbi inda ya harbe wani wanda ake zargi wanda kuma hakan ya saɓa da ƙa'idar aikin ɗansanda.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Okon Placid ya nanata cewa abin da ya faru ya saɓa dokokin ƴansandan
Sanarwar ta ƙara da cewa an aike da jami'an ƴansandan da suka yi aika-aikar zuwa hedikwatar ƴansanda ta Najeriya da ke Abuja.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Tun bayan bayyanar bidiyon matashin a soshiyal midiya, ƴan Najeriya suke ta faman caccakar ƴansandan ƙasar da suke bayyanawa da masu "tsananin mugunta".
Ƴan Najeriyan na ta kiraye-kiraye ga sifeto janar na ƴansandan Najeriya da ya tilasta wa duk wani ɗansanda da ke aiki sanya kayan sarki mai ɗauke da sunansa domin bai wa al'umma damar gane kowa.
Ƴan ƙasar dai sun riga sun yanke tsammani samun tausayi daga rundunar ƴansandan najeriya wadda ta yi ƙaurin suna wajen kisan mutane ba tare da hukunci ba, al'amarin da ya janyo zanga-zangar ƙin jinin ƴansanda ta ENDSARS a shekarar 2020 wanda kuma ya janyo gwamnati rusa rundunar.
To sai dai kuma ƴan Najeriyar na cewa a yanzu shekaru 6 bayan nan, abin da ake zargin ƴansanda wato cin zali da mugunta da kisa ba tare da hukunci ba sun sake yin kome a faɗin ƙasar.