Matar da ta haifi ƴan biyar bayan shekara 12 tana neman haihuwa

    • Marubuci, Michael Teferi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wata mata ta haifi yara biyar rigis, wani abu da ba kasafai ya cika faruwa ba, a jihar Harari da ke ƙasar Habasha, bayan shafe shekara 12 tana jira.

Matar mai suna Bedriya Adem ta ce ita da mijinta suna cikin "farin ciki mara misaltuwa bayan samun yara biyar a lokaci ɗaya".

Matar, mai shekara 35 ta haifi yara huɗu maza da kuma mace ɗaya, waɗanda dukkaninsu ke cikin ƙoshin lafiya, a wani asibiti mai suna Hiwot Fana Specialised Hospital, kamar yadda hukumar asibitin ta tabbatar.

"Babu isassun kalaman da zan yi amfani da su wajen bayyana murnar da nake ciki," in ji Bedriya a lokacin da ta tattauna da BBC.

Ta tuno yadda ta shiga damuwa sosai da raɗaɗi a shekarun da ta kwashe kafin samun haihuwa.

Shugaban asibitin Dr Mohammed Nur Abdullahi ya ce ana ci gaba da kula da matar da jariran nata a asibitin.

Jariran na da nauyin kilo 1.3 zuwa 1.4.

Ya shaida wa BBC cewa akwai kyakkyawan sa ran cewa duk wani jariri da nauyinsa a lokacin haihuwa ya zarce kilo ɗaya, to zai rayu cikin ƙoshin lafiya.

Likitan ya ce Bedriya ta samu cikinta ne ta irin hanyar da aka saba ta al'ada, ba tare da wani aiki na daban ko dashen tayi (IVF) ba.

Tsarin dashen ɗan tayi na IVF na iya samar da ƙaruwar damar samun fiye da jariri ɗaya idan aka dasa fiye da ɗan tayi ɗaya.

Yiwuwar samun cikin ƴan biyar na faruwa ne sau ɗaya kacal a cikin mutum miliyan 55.

Likitan ya ce an haifi yaran ne ta hanyar tiyata a yammacin ranar Talata.

"An ba ta kulawa kamar kowace mai ciki a lokacin da take ɗauke da juna biyu, inda aka shaida mata cewa tana ɗauke da jariri fiye da ɗaya a cikinta.

An ci gaba da ba ta duk wani taimako da take buƙata, in ji Mohammad, kamar yadda ya bayar da labari yana cike da farin ciki.

Bedriya ta ce da farko an shaida mata ne cewa tana ɗauke da cikin yara huɗu, amma a lokacin haihuwa sai guda biyar suka fito.

"A baya na yi addu'a Allah Ya ba ni koda guda ɗaya ne, amma sai ga shi Ya ba ni biyar," in ji ta a lokacin da take bayani kan tsawon shekarun da ta kwashe kafin samun haihuwa.

Matar, wadda wannan shi ne haihuwarta ta farko, ta ce dama mijinta yana da ɗa ɗaya daga auren da ya taɓa yi a baya, inda yaron yake zama tare da su.

"Mijina ya riƙa ce min yaron guda ɗaya ma ya ishe mu, ya riƙa cewa kada na sa wa kaina damuwa, to amma na kasance cikin damuwa a zuciyata da tunanina - kasancewar al'ummar yankinmu na ta yaɗa maganganu kan cewa na kasa samun haihuwa," in ji ta.

"Yanzu kuwa da na jure, abin da ya faru a baya ya zama tamkar mafarki, ba na ma son tuna abin da ya wuce," a cewarta.

"Na kwashe shekara 12 ina cikin takaici, ina ɓuya, kullum ina addu'ar samun haihuwa - daga ƙarshe Allah ya amsa addu'ata."

Ta bayyana cewa takan yi sana'ar noma, kuma a yanzu ba ta sani ba ko za ta iya kula da ƴaƴan nata.

"Amma na san cewa Allah zai huwace mana, kuma ina sa ran samun tallafi daga al'umma da kuma gwamnati."

An sanya wa yaran suna Naif da Ammar da Munzir da Nazira da kuma Ansar.