Ana cigaba da zanga - zanga a Masar

An wallafa
Magoya baya da masu adawa da Shugaba Muhammad Morsi na Masar na ci gaba da zanga zangar hamayya da juna gabanin kuri'ar raba gardamar da za'a gudanar ranar asabar a kan daftarin wani sabon kundin tsarin mulki.
A jiya dai masu zanga zangar kin jinin Gwamnati sun keta shingayen da ke kewaye da fadar Shugaban kasar.
Babban hafsan sojin kasar ya bukaci dukkanin bangarorin al'ummar Masar su hadu a yi wata tattaunawa ta kasa domin sasantawa yau Laraba.







