Yadda kisan mata a Afirka ta Kudu ke ɗaga hankalin hukumomi

Asalin hoton, Brenton Geach/Gallo Images via Getty Images
Ƴansandan Afirka ta Kudu sun sanar da gano wata gawar a dandalin Dawan Park a gabashin birnin Johannesburg, wadda ita ce gawa ta tara da hukumomi suka tabbatar da ganowa a cikin wata biyu.
Wannan na zuwa ne bayan gano gawa ta takwas a gefen hanya a KwaThema, Springs, da ke yankin Ekurhuleni a ranar Talata da ta gabata.
A ranar Talata, manyan jami'an gwamnati sun gana da masu bincike na lardin Gauteng bayan gano gawar mace ta takwas.
An gudanar da taron a ofishin rundunar ƴansandan Afirka ta Kudu (SAPS) na lardin Gauteng da ke Parktown, inda suka tattauna ƙoƙarin da ake yi na bincike tare da gano waɗanda suka aikata waɗannan laifuka.
Muƙaddashin babban kwamishinan ƴansandan Afirka ta Kudu, Laftanar Janar Puleng Dimpane, ta ce sun kama wani wanda ake zargi da hannu a ɗaya daga cikin kisan da aka gano a watan Yuli.
Ta kuma bayyana cewa gwamnati ta sa tukwicin dala 25,000 (R400,000) ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su taimaka wajen warware binciken mutuwar mata takwas a Ekurhuleni.
Ta ce: "Mun samu nasarar binciken ɗaya daga cikin shari'o'in watan Yuli kuma wanda ake zargin yana tsare. Mun kama mutum ɗaya kuma muna neman wani. Muna kira ga al'umma su taimaka mana, saboda haka muka sanya tukwicin rand 400,000 domin taimaka wa binciken."
"Muna kuma kira ga iyalai su sanar da mu idan suna da wani dan uwa da ya bace domin hakan zai taimaka wajen gano gaskiyar lamarin."
A ranar Talata, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya umarci ƴansanda da su gaggauta bincike tare da warware kashe-kashen matan da ake yi a Ekurhuleni.
Ya ce: "Na yi magana da ministan ƴansanda da muƙaddashin kwamishinan ƙasa, kuma sun yi min bayani kan binciken. Na umurce su da su ba wannan shari'a fifiko tare da tabbatar da cewa an gurfanar da masu hannu a ciki gaban kuliya."
Muƙaddashin ministan ƴansanda, Firoz Cachalia, shi ma ya nuna damuwarsa tare da jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu.
Ya ce gano gawarwakin mata da dama a yankin Kempton Park abu ne mai matuƙar tayar da hankali, amma hukumomi ba za su daina bincike ba har sai an gano gaskiyar lamarin.
A baya, BBC News Pidgin ta ruwaito cewa a ranar 14 ga Satumba ƴansanda sun sanar da gano gawar Elizabeth "Tsontso" Moselakgomo mai shekara 38.
Gawarta ita ce ta biyar da aka gano a yankin Kempton Park, musamman a Rhodesfield, cikin wata biyu da suka gabata.
Cachalia ya ce: "Gano matan da aka kashe da yawa a Kempton Park abu ne mai matuƙar tayar da hankali. Duk da cewa bincike zai tabbatar ko waɗannan shari'o'in suna da alaƙa da juna, yiwuwar cewa masu laifin suna kai hari ga mata na buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa."
Yaushe aka gano gawarwaki?
15 Yuli: An gano mace ta farko mai shekara 37 a Kempton Park. An kama wanda ake zargi bayan kwana biyu.
Agusta: An gano gawar mace ta biyu da ta uku a Kempton Park.
10 Satumba: An gano gawar mace ta huɗu tsirara kuma a cikin yanayin ruɓewa.
12 Satumba: An gano gawar Elizabeth Moselakgomo mai shekara 38 a Kempton Park.
14 Satumba: An gano gawar wata mace a gefen hanya a KwaThema, Springs.
15 Satumba: Daga baya an sake gano wasu gawa biyu a Ekurhuleni Municipality.
Me ƴansanda ke yi game da kisan?
Kakakin rundunar ƴansanda ta ƙasar, Athlenda Mathe, ta ce gawar da aka gano a KwaThema tana kama da ta mace mai shekara kusan 30.
Ta ce: "Gawar ta riga ta fara ruɓewa, kuma ana kyautata zaton an jefar da ita a wurin. Masana har yanzu suna nazarin bayanan shari'o'in, bayanan waɗanda abin ya shafa da kuma ɗabi'un wanda ko waɗanda ake zargi."
Ta ƙara da cewa har yanzu ba a tabbatar ko mutum ɗaya ne ke aikata waɗannan laifuka ko kuma wata ƙungiyar mutane ba.
"Wannan bincike ba abin gaggawa ba ne. Shari'ar tana da sarƙaƙiya kuma tana iya haɗa da masu laifi fiye da ɗaya. Muna son jami'an bincike su yi aiki cikin natsuwa domin kada a kama mutanen da ba su da laifi."
Me ƴansanda ke yi game da kashe-kashen?
A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin binciken wannan lamari, muƙaddashin ministan ƴansanda ya ce muƙaddashin babban kwamishinan rundunar ƴansandan Afirka ta Kudu (SAPS), Janar Puleng Dimpane, zai gana da tawagar masu bincike domin samun ƙarin bayani kan yadda binciken ke gudana.
Ya ce taron zai ba da damar duba ci gaban binciken tare da tabbatar da samar da dukkan kayan aiki da goyon bayan da ake buƙata domin gudanar da bincike yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa hukumomi za su gudanar da cikakken bincike domin gano ko akwai alaƙa tsakanin waɗannan kisan-kisan, su gano waɗanda suke bayan aikata laifukan, sannan a gurfanar da su gaban shari'a.
"Tsaron mata shi ne babban abin da muka sanya a gaba. Rundunar SAPS za ta ci gaba da aiki tare da al'ummomi da sauran masu ruwa da tsaki domin gano haɗurran tsaro, ƙarfafa matakan aikin ƴansanda, da kuma tabbatar da cewa ana binciken duk wani sahihin bayani da aka samu."
Sai dai a wata hira da gidan talabijin na SABC, wata mata ta bayyana cewa gawar mace ta shida da aka gano a yankin na iya kasancewa ta ɗiyarta da ta ɓace. Duk da haka, kafafen yaɗa labarai na yankin ba su tabbatar da ko wace ce gawar mace ta shida da aka gano a safiyar ranar Talata ba.
Ƴansanda sun ce: "Muna roƘon duk wanda yake da bayanan da za su taimaka wajen binciken ya tuntuɓi hukumomin ƴansanda ta hanyoyin da suka dace. Muna kuma kira ga jama'a da kada su yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba ko kuma su yi zargi ba tare da hujja ba."
Rundunar ƴansanda ta kuma jajanta wa iyalan waɗanda wannan lamari ya shafa tare da nuna alhininta game da waɗannan munanan kashe-kashe.
Su wane ne waɗanda aka kashe?

Asalin hoton, SA Justice, Crime Prevention and Security
Mace ta farko: Mai shekara 37 da aka gano a ranar 15 Yuli kusa da hanyar R21. Har yanzu ba a tabbatar da sunanta ba. An gano ta tsirara kuma an ɗaure ta da igiyoyin. An kama wanda ake zargi kuma yana tsare.
Mace ta biyu: Mai shekara 32 da aka gano a ranar 24 Agusta kusa da hanyar R21. An same ta ne tana sanye ne ba tare da cikakkiyar sutura ba.
Mace ta uku: Ba a san ko wace ce ba. An gano gawarta a ranar 10 Satumba cikin munin ruɓewa kuma tsirara.
Mace ta hudu: Mai shekara 38 da aka gano a ranar 12 Satumba a Rhodesfield, bayan wani otel. Tana sanye da kayan motsa jiki.
Mace ta biyar: Elizabeth "Tsontso" Moselakgomo mai shekara 38. Iyalan ta ne suka tabbatar da gawarta a ɗakin ajiye gawa na Germiston.
Ta ɓace ne bayan fita gudu da rana a ranar 9 Satumba a Rhodesfield, Kempton Park.
Mutane da dama sun bayyana alhini bayan tabbatar da mutuwarta, yayin da mata da yawa a Afirka ta Kudu ke nuna tsoro da damuwa kan matsalar rashin tsaro.
Ƙungiyar kare haƙƙin mata ta Women for Change ta bayyana fushinta kan gano waɗannan gawarwaki.
Merlize Jogiat daga ƙungiyar ta ce:
"Mene ne amfanin samun rundunar tsaro idan har mu ne za mu ci gaba da kare kanmu da kanmu?"








