EU ta sanar da ƙudirin taƙaita wa yara amfani da shafukan sada zumunta

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sanar da ƙudiri taƙaita wa ƴan ƙasa da shekara 16 yin amfani da shafukan sada zumunta a faɗin ƙasashe mambobinta, a wani yunƙuri na inganta lafiyarsu da kuma kare su daga matsalolin intanet.
A ƙarƙashin tsarin, yara ƴan ƙasa da shekara 13 zuwa 15 za su samu damar amfani da shafukan na tsawon sa'a ɗaya a kowace rana ta hanyar amfani da shafin da aka tanada musamman domin yara wanda kuma yake ƙarƙashin sa idon iyaye da masu kula da su.
Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce matakin zai bai wa iyaye damar sa ido kan yaransu musamman ta fuskar amfani da shafukan sada zumunta.
Dokar ta bai wa yara ƴan shekara 15 zuwa sama su buɗe shafukansu na sada zumunta da kansu.
Tuni wasu ƙasasahen EU suka sanar da nasu shirye-shiryen na taƙaita wa yara amfani da shafukan sada zumunta, cikinsu har da Faransa da Sifaniya.























