Su wane ne kwamandojin ISWAP biyu da suka miƙa wuya ga sojin Najeriya?

Iswap

Asalin hoton, Nigerian Army/X

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wasu manyan kwandojin ƙungiyar ISWAP su biyu sun miƙa wuya ga rundunar sojin Najeriya.

Rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ce ta sanar da cewa mutanen masu suna Ismail Mohammed da Abu Umar da suka miƙa wuya yanzu suna tsare a hannunta kuma suna ci gaba da bayar da bayanai masu muhimmanci, kamar yadda ta sanar.

"Rundunar Operation HADIN KAI sun samu wata gagarumar nasara a yaƙi da take yi da ta'addanci bayan da wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP biyu suka miƙa wuya ga dakarunmu a ranar 8 ga watan Yuni 2026," in ji muƙaddashin jami'in yaɗa labarai na rundunar Haruna Sani.

Wannan nasarar na zuwa a yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar hare-hare da garkuwa da mutane a ƙasar.

Bugu da ƙari wannan nasarar na zuwa ne bayan da rundunar ta samu nasarar kashe wani babban kwamandan IS a Najeriya Abu-Bilal al-Minuki, a wani hari da ta kai tare da haɗin gwiwar Amurka.

Su wane ne su?

A cewar wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a ranar Alhamis, ta ce mutanen suna da babban muƙami a ƙungiyar ISWAP, kuma su ke kula da kitsa ka hare-hare a Mangari a yankin tafkin Chadi

Daya daga cikin kwamandojin Ismail Mohammed, makusanci ne ga wani babban shugaba a ISWAP Baa Shuwa, kuma ya san abubuwan da ake tsarawa sosai a rundunar.

Ɗaya kwamandan mai suna Abu Umar, sananne ne sosai a harkar ta'addanci kuma yana da ƙwarewa wajen dasa bama-bamai.

Aikinsa shi ne haɗawa da kula da ababen fashewa da kuma wasu na'urorin kai hare-hare da ƴan ta'addan ke amfani da su.

Sai dai babu wasu bayanai kan shekarunsu, da inda suka fito da kuma abin da zai faru da su bayan sun miƙa wuyar.

Rundunar sojin ta kashe wani babban kwamandan ISWAP

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A gefe guda kuma, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani babban ɗan ta'adda mai suna Mohammed Khalifa, wanda mamba ne a kwamitin Shurah na ƙungiyar ISWAP.

Ta kashe shi ne a wani farmaki da rundunar Operation HADIN KAI ta jagoranta.

"Miƙa wuyan da kwamandojin biyu suka yi babban koma baya ne ga ayyukan ta'addanci da ƙungiyar ke ƙaddamarwa, musamman saboda ƙwarewarsu da ƙarfin faɗa a ji da kuma gogewarsu a fannin sarrafa makamai da na'ura."

Rundunar sojin ta ƙara da cewa miƙa wuyan da suka yi na ƙara tabbatar da nasarar da take samu na yaƙi da ƴan ta'adda da Operation HADIN KAI ke yi tare da taimakawar sauran jami'an tsaro.

"Hare-haren haɗin gwiwa na ƙara tursasa wa ƴan ta'adda ajiye makamansu da karya lagonsu na iya ƙaddamar da hare-hare a yankin," in ji rundunar sojin.

A watan Mayu ne shugaba Trump ya ce dakarun Amurka da na Najeriya sun kashe - mataimakin babban kwamandan ƙungiyar IS na duniya a wani harin haɗin gwiwa.

A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta, shugaban na Amurka, ya ce daga yanzu Abu-Bilal al-Mainuki ba zai ƙara zama wata barazana ga sojojin Amurka da ƙasashen Afirka ba.