Yadda magoya baya ke shan wahalar samun bizar zuwa kallon gasar Kofin Duniya

.

Asalin hoton, Abdulla Adnan

Bayanan hoto, Magoyi bayan Iraƙi Abdulla Adnan ya kasa samun bizar tafiya Amurka domin kallon yadda ƙasarsa za ta yi wasa
    • Marubuci, Nadia Huraimi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

A lokacin da tawagar kwallon kafar Iraƙi ta samu tikitin gasar Kofin Duniya a ƙarshen watan Maris, Abdulla Adnan ya sayi tikitin kallon wasannin da ƙasarsa za ta buga da Norway da Faransa, wanda za a yi a Boston da Philadelphia a wannan watan.

"Halartal kallon wasa, kasancewa a filin wasa, cikin dandazon jama'a, ana sowa kana kallon tawagar ka, abu ne mai muhimmanci sosai," in ji shi. Wannan shi ne karo na biyu da ƙasar Iraƙi ke samun tikitin gasar Kofin Duniya, tun bayan na shekarar 1986.

Sai dai samun biza ya zama abu mai wahala.

Ba Adnan kaɗai ke fuskantar hakan ba. Magoya bayan sama da kashi ɗaya bisa huɗu na ƙasashen da ke halartar gasar Kofin Duniya na fuskantar ƙalubalen rashin samun biza, kamar yadda wani binciken BBC ya nuna.

Sai dai Iraƙi ba ta cikin ƙasashen da Trump ya sanya wa takunkumin samun izinin shiga Amurka. Hakan ya sa Adnan bai yi tunanin zai samu wata matsala ba.

Bayan fara yaƙi tsakanin Amurka da Isra'ila da Iran, Amurka ta dakatar da ayyukan ofishin jakadancinta a Iraki saboda matsalar tsaro a yankin.

Wannan na nufin babu yadda Adnan da sauran magoya bayan Iraƙi za su iya samun biza saboda dole ne su je ofishinsu da ke ƙasar domin amsa tambayoyi.

Don haka Adnan ya yanke shawarar zuwa maƙwabciyar ƙasar Jordan domin neman biza a ofishin jakadancin Amurka da ke kasar.

Amma bayan ya tafi, ma'aikatan sun faɗa masa cewa, tunda shi ba ɗan ƙasar Jordan ba ne, ofishin jakadancin ba zai iya ba shi biza ba.

Ya kashe kusan dala 1,800 wajen sayen tikitin wasannin da tafiya Jordan.

Ya yi tunanin jaraba ofishin jakadancin Amurka a Turkiyya, amma da yake babu tabbacin samun bizar a can kuma zai iya ɗaukar tsawon makonni biyu, sai ya fasa kawai.

.

Asalin hoton, Julien Kouadio Adonis

Bayanan hoto, Julien Kouadio Adonis, tare da mambobin ƙungiyar magoya bayan Ivory Coast, inda ya ce dokar hana tafiye-tafiye "wani nau'i ne na wariya"
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Magoya bayan wasu ƙasashe sun shaida wa BBC cewa wasu matsalolin da ake samu suna fusata jama'a da haifar cece-ku-ce.

Daga cikin abubuwan da ke kawo cikas shi ne jerin sunayen da shugaba Trump ya fitar, na ƙarin takunkumin hana shiga da fita da kuma hana wasu kasashe biza, ciki har da huɗu waɗanda za su halarci gasar: Ƙasashen su ne Haiti, Iran, Senegal, da Ivory Coast.

Wannan na nufin cewa ƴan waɗannan ƙasashe ba su da damar samun bizar baƙi da hukumomin Amurka ke bayarwa ga magoya baya.

Julien Kouadio Adonis, na kwamitin magoya bayan tawagar Ivory Coast, ya bayyana cewa: "Wannan wani nau'i ne na nuna wariya da bai ya zai bayyana shi ba, amma akwai hujjoji."

"Ba wata ƙasar Turai da ta fuskanci irin wannan takunkumi. Me ya sa sai Afrika?"

Ƙungiyarsa ta kan yura ƙungiyar magoya bayanta zuwa gasar Kofin Duniya, amma a wannan karon sun yanke shawarar ba za su yi ba saboda saboda ƙa'idojin.

Duk da cewa an rage musu wahalar sayen tikitin "masu tsada", wanda ya ce suna kan farashi tsakanin dala $300 zuwa dala 5,000 (CFA 170,000 zuwa 2,820,000 CFA), Adonis na ganin bai kamata a bar duk ƙasar da ba ta son ƙarbar magoya bayan ƙungiyoyin da za su fafata, ta karɓi baƙuncin gasar Kofin Duniya ba.

.

Asalin hoton, Aliou Ngom

Bayanan hoto, Magoyi bayan ƙasar Senegal Aliou Ngom na ganin babu amfanin neman bizar zuwa kallon tawagarsa da aka fi sani da Les Lions de la Teranga da za ta buga wasa a Amurka.

Kasashe 42 masu ƙarfin tattalin arziki ne suka ci gajiyar shirin sauƙaƙa bayar da biza, wanda ke ƙarƙashin hukumar ESTA ta Amurka. Farashinsa bai wuce dala $40.

Sai dai babu wata ƙasar Afrika da ke cikin wannan tsari. Masu neman bizar daga Afrika sai sun biya dala 185, kuma su je ofishin jakadanci domin amsa tambayoyi da bayyana aniyarsu ta barin Amurka da zarar an kammala gasar, sannan kuma su tabbatar da cewa za su iya ɗaukar ɗawainiyar kansu a lokacin gasar.

Sai dai a watan Mayu, Amurka ta sanar da cire buƙatar ajiye dala 15,000 ga ƙasashen da suka samu tikitin gasar Kofin Duniya da suka haɗa da Aljeriya, Cape Verde, Ivory Coast, Senegal da Tunisiya, idan har mutum ya riga ya sayi tikitin wasannin.

Dole sai da magoya bayan Senegal da Ivory Coast suka mallaki biza kafin wata Disamba.

Magoyi bayan Senegal Aliou Ngom, ya halarci gasar Kofin Duniya biyu da suka gabata a Qatar da Rasha.

A ganinsa, babban abin ƙayatarwa a gasar shi ne "ganin al'adu daban-daban daga sassan duniya a waje guda".

Magoya bayan ƙasashen da za su buga gasar Kofin Duniya sun ce hana su bizar Amurka da ƙa'idojin da aka gindaya, suna jin kamar an ware su daga gasar ne.

Duba da yadda ake ta samun yawaitar hana biza, abu ne mai wahala magoya bayan waaɗannan ƙasashen su iya kashe kuɗaɗe da yawa wajen siyan sayen tikitin wasanni kafin neman bizar, wadda ba lallai su samu ba.

Idan sun sayi tikitin kai tsaye daga shafin FIFA, za su iya sake sayar da shi a shafin FIFa ɗin idan suna so, sai kuma su yi amfani da takardar izinin FIFA domin gaggauta samun bizar su.

"Izinin da FIFA ke bayarwa, wata dabara ce mai kyau saboda za ta ba da dama ga waɗanda suka sayi tikitin kallon wasa su samu damar zuwa neman bizar cikin sauri," in ji Céline Atallah, mai kamfanin taimakawa masu neman zuwa ci rani a kusa da Boston, Massachusetts.

Amma ta ƙara da cewa duk da hakan na taimakawa wajen gaggauta neman bizar, ba ya nufin za a iya samu.

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Ƙasashen da suka karɓi baƙuncin gasannin Kofin Duniya guda huɗu da suka gabata, dukkansu sun yi tsarin ba da biza ta musamman ga magoya bayan ƙungiyoyi, duk da yake ba kowanne aka amince da takardunsa ba.

A shekarar 2022, Qatar ta gabatar da katin Hayya, wanda yana daga cikin takardun da suka wajabta kan kowane magoyi baya ya samu kafin neman bizar shiga ƙasar a lokacin gasar, kuma an yi komai ta intanet ne.

Duk da yake da dama sun ji daɗin tsarin, wasu sun ce an yi ta samun matsaloli na sadarwa a wasu wuraren, yayin da magoya bayan Yemen suka ce an soke katinsu ba tare da wata sanarwa ba.

Irin wannan tsarin aka yi amfani da shi a gasar Kofin Duniya a 2018 a Rasha. Waɗanda suka sayi tikiti ƙarƙashin shirin tantance magoya baya sun samu damar shiga ƙasar ba tare da biza ba. Babu wanda aka buƙaci ya je ofishin jakadanci kafin ya samu bizar.

Haka nan a yayin gasar a Brazil a 2014 da Afrika ta Kudu a 2010, an gabatar da biza ta musamman domin gaggauta samun izinin ga magoya baya.

Duk da yake Kanada da Mexico na cikin ƙasashen da za su karɓi baƙuncin gasar, wasanni 78 daga cikin 104 za a yi su ne a Amurka ciki har da wasan ƙarshe.

Tsarin samun biza a Kanada da Mexico ya sha bamban da na Amurka.

Duka ƙasashen babu wadda ta sanya takunkumin ga wata ƙasa daga Afrika, ko da yake Kanada a baya-bayan nan ta dakatar da shiga ƙasar daga ƙasashen da aka samu ɓarkewar cutar Ebola, musamman Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo.

Kanada ta buƙaci mutane su gabatar da kansu domin ɗaukar hoton zanen yatsunsu, amma kuma ƙasashe biyu da za su buga gasar, Iran da Cape Verde ba su da ofishin da Kanada za ta ɗauki waɗannan bayanan.