Arsenal ta dage kan Stones, Chelsea na harin Lacroix

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Ingila John Stones, a kyauta idna har ya tabbata ɗan wasan bayan Faransa Willaim Saliba zai yi doguwar jinya. (Sun)
Chelsea ta tattauna da Crystal Palace kan ɗaukar ɗan wasan Faransa Maxence Lacroix, inda suka yi wa ɗan wasan kudi kan fam miliyan 55. (Talksport)
Hull City na tattaunwa da Aston Villa kan yiwuwar siyen dan wasn Jamaica Loan Baily. (Athletic - subscription required)
Sabon mai horar da Fulman Alvaro Arbeloa na son ɗauko ƴanwasa biyu daga tsohuwar ƙungiyarsa ta Real Madrid, ciki har da ɗan wasan Arjantina Franco Mastantuono da takwaransa na Sipaniya Gonzalo Gracia. (Sun)
Ɗan wasan Bologna Jonathan Rowe har yanzu na cikin jadawalin ƴan wasan da Aston Villa da Chelsea ke zawarci. (Calciomercato - in Italian)
Hull City na dab da ɗauko tsohon ɗan wasan Newcastle Matt Targett, wanda kwantaraginsa da ita ya ƙare, bayan da ya bar ƙungiyar a wannan kaka. (Mail)
Liverpool na shire shiryen yin gogayya da Manchester Untied wajen zawarci dan wasan Faransa da Roma Manu Kone. (Football Insider)
Aston Villa ta yi wata tattaunawa Chealse kan yiwuwar siyen Nicolas Jackson da Alejandro Garnacho a wannan kaka. (Teamtalk)
Ɗan wasan AC Milan da Portugal Rafael Leao na son komawa buga gasar Firimiya maimakon ci gaba da zama a Turkey, yayin da ake ganin ɗan wasan zai iya komawa Aston Villa.(Gazzetta - in Italian)
Lazio na harin ɗan wasan West Ham da Jamhuriyar Kongo, Aaron Bissaka, yayin da itama Arsenal ke harin ɗan wasan. (Mail)
Juventus na harin mai tsaron ragar Aston Villa da Arjantina Emiliano Martinez, yayin da ƙungiyar ta Serie A ke ci gaba da sa ido kan mai tsaron ragar Fiorentina, David de Gea. (Calciomercato - in Italian)
Everton na iya zama kishiyar Inter Milan wajen zarcin dan wasan Tottenham da Ingila Djed Spence. (Football Insider)
Liverpool na son ɗaukar ɗan wasan Sweden da Daniel Svensson daga Borussia Dortmund, sai dai za ta iya fuskantar gogayya kan siyen ɗan wasan daga Arsenal(Caught Offside)














